← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 80

Sashe 24

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta karbi kudi,Umma tace sai kice an gode Allah kara Budi,Salma ta fada kuwa tana tufe Ido,Na'im sai murna yake.
An soya kaji,anyi farfesu da wasu harda su zabbi,da safe kuma Umma sukayi Shinkafa da miya da nama ga hadin salat,ga kaji suna tokare murfi da da kafa,haka makwafta ma suka dinga kawo kalar nasu suma suna basu,ga kowa an raba an bashi nasa a kwano shi kadai dukkansu kowa kaji Uku da farfesu guda daya,biyu kuma soyayya,Naman rago kuma a miya,wai ranar ana bargaje dadi,Salma harda siyo musu lemon kwalba kowa biyu,nan fa kowa yaja gefe Kaci son ranka ka rufe anjima ka kara,Yamma tanayi kuma kowa ya dau wanka na gaske kai ba kace yan kauye bane,har matan aure kowa da sabon kaya yara da manya maza da mata samari da yan mata tare da tsofaffi gaba daya an fito ga kida da wasanni na tashi iri iri,kuma kidan wakokin hausa na zamani na wannan shekara,mata da maza cashewa akeyi harda yan jarida suna dauka.

Salma da Na'im wankansu kamar party zasu halarta a Birnin duniya,sun kure adaka da kayansu na karshe,Salma ansha doguwar rigar material cotton maroon and white,haka Na'im ma komai fari Kal,suka fito tare da jerowa,Umma da Malam suna gida sunce basa fita su,
Ana karasawa Salma taji kida jikinta har rawa yake karku manta dama ta saba da rawa abinta tun suna tare da Raheel ta iya.
Yan mata cashewa sukeyi samarinsu ana musu liki,Salma ta basu Doller dinta a Dubu ashirin suka bata sababbi yan Dari da yan hamsin ta bawa Na'im yan 100 ita kuma ta rike yan 50.

Yace shi bazai shiga ciki ba,Salma ta fara kukan shagwaba Saurayin kowa yana gwada bajinta amma yanda suka Sha kyau yaki yi mata Zata fasa auren ma,nan yace to zai je amma liki kawai zai yi mata,ana canja kida me tashi Salma ta shige yanda take rawar birgewa nan take waje ya dau ihu da tafi,kafin Na'im ya shiga maza sunyi yuuuuu suna zazzage lalitar kudinsu kan Salma,sun manta da yan matansu harda matan ma liki suke ta yiwa Salma,Na'im zuciyarsa kamar ta fito kawai sai ya jira su gama,aka canja kidan Yan Nija me dadi gaske da duka,Salma kamar yar rawa dama haka take canja salo,Ana Shan kallo,Na'im ya shiga duk ba wanda ya lika yan Dari sai shi ya zazzage kudin duka ya rage 3k ciki kawai ganin yanda ake kallon Salma ya fasa ya janye ta sukayi waje,suka koma yan kallo tuni labari ya cika gari turawa sunyi bajinta,sun hada Kansu da mutan kauye basu da girman kai,ai sai aka koma sonsu a kauyen,ana ai ba ruwansu basu da girman kai komai dasu akeyi suna shiga su Zama dai dai da yan kauye,shigarsu ce kawai ta ban banta.Anan nake tunatarwa ga duk wacce ko wanda Allah ya kaishi aiki kauye ko wani abu kar ya dinga nunawa cewar shi ya fisu yana wulakantasu,ana nunawa basu San komai ba etc ka Zama social to duk inda kaje ko aiki ne za ka samu yabo da shedar arziki,ba ana cewa kasan wance kaji ance Allah ya tsine mata,tsinanniya,ai wannan jaraba ce,Allah ya mata kaza etc ba dadi amma duk inda akaje aji ana yabon ka da shedar kirki ko mutuwa akace kayi addua za ayi maka sannan ka samu sheda me kyau,basai kauye ba ko ina Allah ya hadaka muamula da mutane a kiyaye a zauna da mutane lfy a fahimci juna,sai ka samu kyakyawan sheda.

Salma suna gefe suna kallon masu yi can suka koma wajen masu wasanni,wasu yan matan da maza gada akeyi ana wake waken dandali ,Salma taji ana In... nai... haka.. in.. nai. .haka na gano rufin dakina,wai gidan mijin da zasu aura,wata tace in nai haka na gano shi tsaye,Salma ta shige itama ta juya kai kamar yanda sukeyi tace in. Nai....haka...in...nai...haka na gano masoyiiiina....ta kalli Na'im yana sakin murmushi kamar yanda mazan sukeyi idan tasu ta fadesu,sunsha kallo iri iri so sweet sannan suka dawo gida wajen 12am na dare sai baccin gajiya.

Washe gari kuwa Umma tasha labari na kallon da sukayi har gwadawa sukeyi yanda akeyi,yauma da yamma basu shiga ba amma sunsha kallo,wani Dan birni yazo da kafceciyar waya ta birgewa Camera kamar ka dauko mutum,ya dinga yiwa su Na'im da Salma pics iri iri a ko ina tun jiya haka yau ma,har kajin su saida yaje gidan ya dauka,ya daukesu tare da Malam Magaji da Umma ya musu iri iri masu kyau, sannan Salma ta karbi yar karamar wayar Rahina tana da memory aka tura musu pics dinsu a ciki wai idan sun siyi tasu zasu tura abinsu.
Dan birni yayi deleting pics nasu daga wayarshi yayi musu Sallama ya tafi.

Mummy Allah Sarki ta rame hawan jini ya kamata me karfi kullum suna hanyar asibiti,gaba daya Family din ba a jin dadi a cikinsa Sabo da rashin Babban jigonsu Na'im da ace mutuwa yayi da hankalinsu zaifi kwanciya sunga gawarsa da ace bata yayi,Kullum Sa rai sukeyi za a ga Na'im Amma shuru.

Affa da Ummitu ana ta cin duniya ba ruwansu da kowa,kawai cin kudinsu sukeyi,wannan shekarar ma Affa ya saida wasu shanu nasa zai tafi kasa me tsarki domin sauke farali,ko Salma basa tunawa a rayuwarsu,sun manta ma da ita,Affa arziki ya karu yace yanzu ya daina zama da ka sai da bin malamai ana neman tsari Sabo da masu hassada,nan ya fada malamai a tsare masa dukiyarsa,tsafi da shirka iri iri yakeyi akan shanu,har makabarta yake binne binne Sabo da wai duk na tsarin kai ne da dukiya Sabo da harkar ta koma ta malamai,ana neman ran mutane ana neman lafiyar mutum shi yasa yanzu mutane mutum bashi da niyyar bin malamai Amma Sabo da mutanenmu sun koma shirka ana kashe juna,ana tsafi ana neman lfy mutum,ana shatile ma kafa,yan mata,kishiya,yan kasuwa,ma'aikatan Gomnati,yan siyasa,barayi,yan fashi,yan sane,samari matasa etc kowa kusan yanzu Malam,mijikinki zaiyi budurwa tana sanin cewar yana da mata tun kafin ta shigo za a fada malamai ganin an raba su,ta mallake miki miji tun tana waje,uwargida tana kunsar takaici,daga nan itama a bata shawara baza ta dinga addua da kanta ba sai a fada malamai,idan kuma an sawa mutum cuta dole sai da malamai za a warke daga nan idan an warke baza a hakura ba anga hanya shike nan sai aci gaba da kai bukatu.
Malam ya zauna ya nuna shi na Allah ne yana ta kawo aya da wa'azi ta yarda dashi malamin kirki ne baya shirka ashe a daki shi kadai yana can yana rafka Sabo yana bautar Aljani yana shirka wa Allah,gasu nan abinda akeyi kenan yanzu,ko yar karamar sana'a mutum ya fara sai ya fada malamai Sabo da yanzu masu hassada za fara masa binne binne a wajen na layoyi,dan a hanashi ci gaba,wani container zai siya kafin ya hada ta wai sai kaga har anje an masa binne binne ciki,abin haushi yanzu har gonaki na kauye akeyi,da anga gonar wane tayi kyau sai aje ayi maka kulunboto ta lalace kar a samu abin kirki,kar dai aci gaba.
Abin haushin kaga mace bata ci gaba wata ma ragwargwajajjiya Amma in kaji tana lissafin malamai abin sai ya Bada mamaki,kuma dai bata ci gaba ba tana nan yanda take sai baya ma da taci,a dinga hakuri da lamarin Allah mata,wasu ma su suke dauko HIV wajen bokaye su sawa mazan ace miji ne,wasu ayi amfani da ruwan ni'imarsu,aji tsoron Allah mata da Maza musulmi,shirka Babban laifine kar a mutu anayi wlh wuta har abada ba sassauci ba rangawame.
Idan ma kinayi ki roki Allah ya rabaki da shirka ki daina,duk rabonka bai wuce ka,abinda zaka samu shi zaka samu a duniya ba wanda ya Isa ya hana ko yasa.

Maimuna anyi kiba an kara haske anyi kyau sosai tana juya Hashim dinta domin magungunan mata take sha tana gyara jikinta,bata shirka iya maganin gyaranta take siya sai yanda take kunna Hashim dinta yana like mata,Zainura matar Ubale tana da kishiya anyi mata Amarya ta siyi me kwado dan mukulli,Zainura tasa Ubale baya sha'awar kowa sai ita,kishiyarta Asiya sam Ubale baya sha'awarta duk ranar kwananta,sannan ta siyi maganin sawa a tsohuwar rijiya na malkakar miji,itama Asiya taje takanas ta siyo me dan mukulli,duk ranar kwanan ko wacce sai ta kulle Ubale,ranar kwanan Zainura sai Asiya Tace Bismillahi na kulle Ubale,shike nan bazai sha'awar Zainura ba yanzu,Haka itama Ranar kwanan Asiya sai Zainura ta daga nata tace Bismillahi na kulle Ubale sai ta saki karfe fas shike nan,gaba daya sun hana Ubale sha'awar ko wacce cikinsu,ko wacce ta kulleshi,sunyiwa kansu sun cuceshi kuma.
Chapter 24 · 0% Book details