← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 80

Sashe 7

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hunaif da Aisha dariya sukeyi kawai yanda Na'im yake zare Ido gashi Salma kamar jela ta cukwikwiyeshi,
Palo suka shiga gaba dayansu Family din,Na'im cike da izza ya zube saman kujera Salma ma batayi kasa a gwiwa ba ta fada kansa tayi Flat tace My Love muje dakinka zanyi bacci,Salma ta saba da Raheel bata tsoron hada jiki dashi dama sun saba ba kunya, Mamaki ya kashe Na'im ba shiri ya hankadota kasa ta fado ta fasa goshinta sai jini,amma Salma ko a jikinta saima cewa tayi yau mugunta kake ji My Heart.a fusace Na'im ya kwasheta da Mari har sau biyu fuskarta take ta kumbura sumtum,
Mummy ce ta masa fada sannan ya Mike a fusace yayi sama part dinsa,Salma zumbur ta Mike tana kuka da shagwaba ta rufa masa baya,yaje zai shiga Dakinsa yaganta a bayansa yace ke wacece jakara ce (ke wacce Jaka ce),Shuru ta masa tana tsoronsa jikinta na Rawa tace Wai me nayi maka? Ur Father stupid cewar Na'im, kuka ta saka masa tana shagwaba da burburwa,ya salam cewar Na'im, ba imani ya sa kafarsa ya harbota Saura kadan ta gangaro daga steps Allah yasa ta bige da karfen benen nan take Hannunta ya karye Baras,Kuka ta kwalla tana wayyo hannuna wayyo Raheel dina, wayyo Affa wayyo Ummitu ,a fusace Na'im yayi shigewarsa bedroom ya barta nan tana ta kuka,abinka ga sun Saba Rayuwar turai ba wanda ya kulata sai Dada da Mummy ne suka je kanta.

Mummy ta sata a mota tare da Raheel suka kaita asibitin Na'im Mummy ta masa waya lallai kazo kasa a duba yarinyar mutane kuma wlh kai zakayi jinyarta harta warke marar Imani kayi gaggawar zuwa kaji na fada maka,Aisha zata baka abinci ka taho dashi da sauran duk abinda patient zai bukata na kwanciya a asibiti.
Na'im kamar yayi kuka haka yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya hadaddun gaske,jean black da Riga dark Green tasha Rubutu da baki,
Yana zuba uban kamshi Dada ta shirya masa komai aka zuba a mota saida yaci abinci ya gama yangarsa sannan ya tafi Hospital cike da Mulki.

AsmaBaffa

A dinga Sharhi Fans
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉 KAMARSU CE DAYA🏉

26-30 31-35

Official

By
AsmaBaffa

AsmaBaffa Fans club Wannan page naku ne sabo da jin dadin sharhinku.

Driver da guards nasa ne suka kwashi komai suka shigar dasu room din da aka kwantar da Salma, Na'im saida ya gama yangarsa sannan ya sallami guards nasa ya shiga hospital din nasa,ma'aikata sai kwasar gaisuwa sukeyi suna masa ya me jiki yau an kawo Kanwar Ogan nasu Hospital sai faman kai kawo likitoci keyi a kan Salma.
Mummy tana gefe da Irfan likitan kashi yazo zaiyi gyara Allurai aka zo za ayiwa Salma,ita a duniya ba a taba mata Allura ba Raheel ke mata magani idan bata da lfy,
Kallon Na'im tayi wanda shigowarsa kenan kamshinsa ya cika wajen,Salma ta zabura tare da cewa zaka ce ba kaine Raheel ba ga kayan jikinka wanda kazo min dasu last wk baki ta cuno tare da aika masa harara tace hummm kuji ni zaka Yiwa zara?

Mummy tace yi hakuri yarinya a doraki tukun idan kin warke ayi maganar,Salma ta fashe da kuka wlh shine za a ce ba shi bane,sai da ta bawa Na'im dariya yanda takeyi kamar yarinyar goye,Salma tace gashi nan ma yana dariya Allah shine ka fada musu gaskiya Raheel kaji pls,

Doctor yace kawo ayi miki Allura zanyi aikina,Salma nan ma tace Ni Raheel ne zai mun magani ai shi yake min ni ba a min Allura idan kun bar hannun ma da kansa zai dorani,so kuke Ku zubar min da ciki na,ina da ciki fa Raheel ya bani ajiyar Babynsa, basu gane ajiyar ba har ga Allah tunaninsu ciki wani yayi mata da gaske amma ko kunya babu take fada musu haka,
Wata uwar Tsawa Na'im ya buga mata ba shiri tayi shuru jikinta ya fara rawa tsoron Wannan Raheel din take ji,wancan kuwa bata tsoransa gaskiya wannan mugu ne ba irin Raheel dina bane.

Kuka ta fara tana ta shagwaba da kyar Na'im ya karbi Allurar da kansa da mugunta ya tsira mata a duwawu tana kuka ya gama mata du yace a fara dori duk su Mummy su fita,suna fita Na'im ya kama Salma ya matseta ya riketa kam ko motsi bata iyawa haka aka gyarata zam zam,ba wani kuka ba komai sabo da dadi take ji tana jikin Raheel dinta sabo da kauna bata San ma an gama gyaran ba,ta lafe a jikinsa tana shakar kamshinsa cike da tsananin so da kauna sai bacci ya kwasheta nan take.

Zameta yayi daga jikinsa ya fita yana niyyar barin hospital din Mummy tace dawo wlh kai zakayi jinyarta kayi wa yarinya mugunta ka barmu da wahala,ga abinci nan in ta tashi ka bata muje Irfan gida,gobe ma ka karawa gwadawa wata mugunta haka indai ba wani abu kazo dauka gida ba karka sake na ganka a gida sai ta warke a nemi gidansu a maidata can,cikin fushi Mummy ta masa magana shi yasa ya kasa musawa har suka bar Hospital din.
Office dinsa yayi tafiyarsa ya dade ciki har 8pm yaje yayi Sallah yaci abinci a wani eatery ya dawo room din Salma.

Tun daga waje yaji tana ta bige bige tana gurnani,da sauri ya shiga ciki a saman Bed ya hangota tana ta dukan katifar bed din hawaye na shararo mata daga Ido,Dankwalinta ta zame ta fara barbaza gashinta tana tsigoshi,
Na'im yace no wonder nasan yarinyar nan bata da lfy Aljanu gareta,karfin Hali yayi ya shiga tare da rike mata kai ya dinga tofa mata ayatul kursiyyu,Amanarrasul,Falaq,Nas,Iklas etc sai ga Salma ta fadi sharab tana ta baccinta tayi bacci ya kai na One hr lokacin Na'im yana ta danna wayarsa a kujera gefen bed nata ta farka da Kuka tana kiran Raheel,Na'im yace wannan kwai dan iskan Raheel ya cuceni,
Kallonsa Salma tayi ta Mike ta koma kusa dashi tace Dan Allah idan kasan kaine Raheel dina ka fada min,
Zan mareki fa ni sa'anki ne sau nawa kike so na fada miki ba shi bane Na'im thats My Name.

Je kiyi wanka da Brush kizo maza kiyi salloli,Kafada ta make tace Allah ni bazanyi sallah ba,Na'im yace sai kana cewa Period kike yi me wani baja kiyi sallah ba na iskar banja(sai kice period kikeyi mene wani baza kiyi Sallah ba? yar iskar banza)

Hausar tasa tana bawa Salma dariya tace Raheel muyi yaren da muke magana dashi tunda baka iya hausa ba,yanzu zan iya yin sallah kenan ka amince? Zaro Ido Na'im yayi yana mamaki,yace kai dan Uba naki we bakina da hankali? Wlh sai kinayi sallah yau je kayi wanka da Alwala harda Brush ma( ke dan Ubanki baki da hankali wlh yau sai kinyi sallah je kiyi wanka da Alwala da Brush)

Kunkuni Salma ta fara tace ai sai kace nayi Sallah ka yarda ba kawai ka dinga zagina ba Ubana ya mutu amma kana zaginsa,kai idan an zagi naka zaka ji dadi,mikewa Na'im yayi a fusace yayi kanta zai daketa ta fada toilet da gudu tana lallaba hannunta marar lfy, sabo da mugun tsoron Na'im takeji,Murmushi me lafiya ya saki,haka tayi duk abinda yace da hannu daya sai kuma ta kasa daura Towel ta dinga kwala masa kira Raheel.... Raheel, tsaki yaja ya je jikin kofar cikin lion Voice yace what? Cike da shagwaba tace na kasa daura Towel fa Ok na rufe idona just come out ki bani towel naki sai na daura miki,
Abinka da yarda kuma da Sabo Salma ta saba Da Raheel dinta ganin Na'im takeyi kamar shi,haka ta fito zigidir idonsa a rufe ba cin Amana ta Dora masa towel a hannu tare da rike hannunsa ta Dora saman kafadarta nan take ya gane ido rufe ya daura mata sama sama.

Baki ta cuno tana sangarta taje saman Bed ta zauna shi kuma ya bude idonsa,. tace
a bani Body cream dina ya Raheel,idan kinka kanra ce mini Raheel zakina ganin me zana miki,ita hausarsa ce ke bata mamaki Raheel dinta komai ya iya amma wannan turanci kawai ya iya hausar ma sai kadan duk da cewa itama hausar bata isheta ba amma tafi shi iyawa.

Gashinta ta turo masa ko kallonsa ba tayi ba yana gefe yana satar kallonta yanda tayi wani Fresh gashinta me tsayi baki ga santsi,jikinta luwai luwai gwanin sha'awa tana zamanta da Towel ko a jikinta sabo da ta saba da Raheel bata damu ba gani take da gaske Na'im ma shine,vaseline ta murza a hannu da kafarta komai da hannu daya take yinsa,hannu dayan baya komai,Towel din ma nema yake ya zame,Kallon Na'im tayi tace Raheel zo ka sa min riga ta bazan iya ba wankan ma da kyar nayi,pant dina ma a dustbin na jefashi har bra din tunda bazan iya wankewa ba,
Na'im komai sabo ya dauko a katuwar leda yace mata oya Mika tsaye(Mike) pant sabo ya dakko size kamar nata ya tsuguna a kasa ta dafa kafadarsa da hannu me lfy sannan yace Daga kafar naka kasa,ta daga tasa ya gyara mata tsab,Sai kallonsa takeyi tana murmushin jin dadi, ba tare da ya kulata ba ya dakko doguwar Riga marar nauyi Maroon sabuwa da siririn dankwalinta,yace sunkuyo na sa maka vest bazan iya sa maka Bra ba,haka ya shirya ta komai ya mata tana lallaba hannunta shima hakan dan yaga irin Aljanun da tayi ne da wlh sai dai ta shekara da dirty.
Chapter 7 · 0% Book details