← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 80

Sashe 55

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ce ta amsa sallamar da fara'a kasancewar tasan su Salma ne sun sanar dasu zuwansu Har Anty Rukayya ma tazo ganinsu,Salma da gudu ta fada jikin Umma tana ta murna sai lokacin Malam ya fito daga dakinsa da fara'a cike da tsantsan murna ya karbe su,sai lokacin su Mummy suma suka shigo gidan gaba dayansu,nan suka kacame da murna harda Anty Rukayya,katuwar tabarma aka shimfida kowa ya zauna ana gaisawa da juna,Umma da Rukayya suka kawo musu abinci shinkafa da miya da salat sai soyayyan nama,lallai su Mummy sun yaba matuka da tsabtar Umma kamar ba a kauye ba komai das.

Bayan sunci abinci sunyi Sallah nan fa Suka shiga bangaren da Salma da Na'im suka zauna suka kalla komai tas sabo da Umma tana shiga ta gyara,Zainura bata magana Sam sabo da burinta taje gida wajen iyayenta,Umma tace Mazan sai su kwana a bangaren da Na'im suka zauna da aka musu aure,matam kuma su kwana a dakinta,yau Na'im tsarin bai masa ba shi da yake so a bashi part dinsu shida Salma subar tarihi a saman Bed din,amma shi yaushe rabon da ya kwana shi kadai yanzu za a raba musu makwanci,suna yin Sallar magrib Zainura ta kwashi kayanta da tarkacenta kaf tace gida zata tafi ita kafin gobe su Mummy suzo a gaisa da iyayenta.

Tunda Zainura ta tafi Irfan da Hunaif suka ji ba dadi domin ita ke sasu dariya da nishadi sabo da surutunta,anyi Sallar Isha Irfan yace Umma ina yaro ni dai a rakani gidan su Zainura zanje,Umma tace to,Hunaif yace nima muje pls ko yawo ta kaimu,Na'im yace to shi da Salma zasu tafi gidan Abubakar da Rahina.an bar Mummy,Dada,dasu Umma suna ta hirarsu.

Gaba daya yan mata frnds na Salma da Zainura sun hadu kaf a gidan Rahina ana jira Salma da Zainura suzo yau asha hira,Wani yaro ne ya Raka Irfan da Hunaif gidan su Zainura,gidan ba laifi na kauye me kyau ga uwar tsabta komai Kal Kal, Babanta Malam Yahaya suka gani a waje ai nan suka gaisa cikin mutunci yana ta murna tare da godiya ta rike masa ya da sukayi ga Sha tara ta arziki da Zainura tazo musu dashi,abin ba a cewa komai,yace ai ba gate kawai su dinga shiga gidan direct idan sunzo,har ciki ya kaisu,dakin da Zainura take kwana da katifarta me kyau yasha gyara ba tarkace nan yace su shiga,aka kawo musu fura da Nono da pure water,tare da tuwon dawa miyar zogale da Namanta,Zainura ta shiga wanka lokacin,har Babarta tazo sun gaisa dasu Irfan

sai da ta fito ta shirya fes harda sa doguwar riga red ready made tayi kyau,a daren saida ta shafa powder da jambaki red tayi kyau tana kamshinta ta shigo dakin da Sallama,Irfan ya kalleta yaga tayi wani kyau,har kinyi wanka? Zainura tace yes tana bude kwanikan da aka kawo musu abinci basu ci komai ba,Zainura tace badai kyankyaminmu kuke ba?,Hunaif yace no..no kawai munci abinci a gidan Malam ne,ina can aka kawo muku ba wani na kirki kuka ci ba fa,dan kar tace basu ci ba suka ci kadan,Ku tashi mu tafi gidan Rahina,Wai wacce Na'im suka tafi gidanta?ae cewar Zainura,sun Mike kenan aka kawo nepa Wal ko ina ya dau haske,yaran gari sai ihu ake Nepaaaaaaaaaa.....Irfan ya dinga dariya da mamaki jin yanda gari ya dauka da ihu da tsalle ana Nepaaaaa.
Flasks din kayan dadin Zainura da taho dasu tun daga Abuja kadan ta ebarwa yan gidansu ta dauko abinta zata kawowa su Zainab kawaye suma suci albarkaci.

Na'im suna zuwa Abubakar yayi Murna da mamaki,Haka Rahina ma murna kamar me,suka zauna ana zuba hira saiga kawayen su Zainura sunzo wajen Salma.
Zainab ce ta fara shigowa ta rike baki tana kallon Salma tace Salamatu yanzu kece haka kamar Baturiya kema?Salma tana dariya tace nice mana Ku shigo yau za a Sha hira,dukkansu suka shigo,Abubakar yace Na'im ya taso su koma dakinsa,Jamila tace Wai ina yar duniya Zainura na matsu na ganta,Salma tace tana tare da kannen Honey zasu zo ne,Zahrau tace shegiya Zainura kaga yar banzar yarinya yanzu har ta samu shiga cikinsu?ke Salma mene hany(honey) Salma tace ai Zainura yanzu nema take ta siye gidan su Honey gaba daya,Honey zuma kenan ai,ruwan Zuma, Rahmatu ta rike baki tare da cewa Yau na shigesu ni jikar Talatu,yanzu wato shi Na'im ne Ruwan zumarki heeeeeee Suna shewa haka sai ga Sallamar Zainura dasu Irfan,

Rahina da Danta Raheel ta shiryo Jullof din taliya tasha kifi,Rahina tace Zainura Ku shigo mana,Zainura ta shigo nan take suka dauki ihu,sunsha mamakin yanda Zainura ta kara haske da kiba ga kyau da tayi tasha gyaran gashi,Dama Zainura ma tana da haske sosai ba baka bace fara ce bata kai Salma haske ba da kadan,Su Na'im kuwa gaba dayansu kamar Turawa fatarsu take fari kar,
Barira ta Mike tare da shafa jikin Zainura tace Alquran laushi,Irfan da Hunaif ba ruwansu da wani mata suka shigo aka basu kujera suka zauna matan suna kasa,Rahina ce da Salma suke saman kujerar Palo suma.
Zainab ta Mike ta damki hannun Zainura ta ja yaji shiiiii billahillazi huwarrahmanu Laushin Bala'i kamar auduga,Dan ubanki Zainura yaushe kika dawo haka?kwai kike ta ci ko kaza? Su Irfan sai dariya suke yanda yan matan nan suke ta haukar kyan da Zainura tayi.

Zainab sarkin Baro zance tace Zainura wai yaushe kika cika haka dan uwarki? Ke da kike yar figigiya,Rahmatu tace Zainura ta Zama yar Ethiopia ai,Flasks ta bude musu tace kowa yazo aci dadi dashi,yan matan kauyen suka dinga ci suna Santi,Suna Zainura Allah ya biya,Allah ya kai gaban manzo,Jamila tace Yasin dole ki canja yanzu wannan kuke ci kullum?Zainura tace kan Bala'i ai ya zarta wannan iri iri ne,suna gama ci suka fara hira nan Zainura ta fara basu Labarin birni da yan makarantarsu.

Zainura tace Barira watakil fa idan za ayi tashin kiyama sai dai na bugo muku waya ya juju wamajujju sun bayyana ta birni,domin alamomin tashin alkiyama sun bayyana kaf a cikin birni,kunga kuwa kafin tazo zasu faro ta birni,Jamila ta rike baki da mamaki tace ke ki Bari dan manzo? Zainab tace Zainura munshigesu yanzu mu ya za muyi bamu sani ba,Zainura ta sheke da dariya haka su Irfan ma,Zainura ta kalli Salma tare da cewa Salma dan ubanki ba dai tunanin Mijinki kike ba? Salma tace ba dole ba ni na saba dashi kullum,Suka sheke da dariya harda Shewa,Hunaif yace wace Zainab ne? Zainab ta daga yatsa sama tace I'm irin Baturiyar nan,Hunaif yayi dariya yace ai naga Alama ina jin muryarki kuna waya da Zeena,Zainab tace au Zeena ake ce mata yanzu? Irfan yace ai ta waye yanzu kowa Zeena ake ce mata,Zainura ta dafa gwiwar Irfan tace ban son sharri Allah,Da sauri Zainab tace laaaaaaaa kunga Zainura ma ta koma irin Salma ke Zainura yar Iska kika dawo kema,Zainura tayi dariya tace ke dakikiya ce Zainab a birni haka suke normal ne ai,Zahrau tace Alamomi lallai sun bayyana sai a jira hura kaho.

Ke Zainura kinji yan kauyen nan ana ta cewa wai Karuwanci kika tafi birni kinji surutu cewar Rahmatu,Zainura tace na Karuwawa Uwarsu zagi,Salma tace kaji Matsiyata,suna haka sai ga Sallamar yaro Wai Zainura tazo Inji Audu me kifi,Hunaif ya kwashe da dariya yace mutuminki da kullum sai kince Audu me kifi,
Zainab tace kai Bature wlh Audu Son Zainura yake sosai amma yarinyar nan sai dai ta kwashe mu muje mu cinye masa kifi,bata sonsa fa,Irfan haushi ya kamashi ya hade rai,Zainab taci gaba tace to Zainura tafimu Farin jini a garin nan kowa sonta yake,kaga Ubale?a kanta jarinsa ya karye,Hunaif yace tab lallai tana da farin jini,Sadisu me kwakwa sai da talla ya gagareshi sabo da Son Zainura,Zainura tace kin tuna Deeni me Keya hhhhh suka kwashe da dariya gaskiya kin cuci Deeni har yau yana nan bashi da Sana'a, Zainab tace Dan Isiya me Rake na ya isheni Alquran .

Audu yaji Zainura shuru ya kara aikowa,Zainura tazo zasu gaisa zai bata sakon kifi,Hhh sabo da yasan Dama Zainura idan yace tazo bata zuwa sai yace ga kifi sai taje,amma yanzu Zainura ko kaza bata isheta kallo ba bare kifi,ganin Irfan yana ta fushi yasa ta ki zuwa,Hunaif yace kije mana ki karbo mana kifin mu gani,Zainura ta Saci Kallon Irfan suka hada Ido ta masa magana da Ido tace naje? Rahina ta zunguri Zainura da kafa irin an kamata tana Signa,
Irfan yayi banza da ita tare da dauke kai,Zainab tace Zainura kin shiga uku wlh muna kallonki kinfi karfinmu,Zainura ta Mike tace ina zuwa,Taje wajen Audu,maimakon Audu yayi hira tunda ta fito ya fara Zainunu Zainunu Na rantse Da darajar Allah kinfi da kyau jar uba,nan kawai ya miko kunshin kifi a leda yace jeki kici kiyi bacci tawan,dan Allah ki dawo muyi aure Alqur'an kullum sai kinci kifi,Zainura tace na gode tayi cikin gida,ta dire musu ledar kifi,ana budewa kifin jela ce guda uku rak,har Irfan sai da yayi dariyar kyautar Audu,Suna zaune nan ma Ubale ya turo Zainura taje,tana zuwa ta dawo dauke da ledar Kwakwa da dabino,Sadisu bai zo ba sai gyada me bawo dafaffiya da yawa ya aiko da ita Wai a bawa Zainura taci,Can Samari suka dinga yo aike kowa da abinda za a kawowa Zainura,haka sauran Yan matan ma nasu suna ta kawo abubuwa,Dan Isiya ya kawowa Zainab rake me Uban yawa ta bawa bakin kawarta turawa,ana ta kawowa wai duk na turawane kaji fa kara ta mutan kauye da karamci tare da karrama bako,
Chapter 55 · 0% Book details