Sashe 38
Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna haka Sai ga Na'im tunda yaga takalma haka yasan sune domin yaga ma shigowarsu gidan,Sallama yayi ya shiga,Salma ance a zaman Aure ba kunya sai ka zama Karuwa gaban mijinka,aiko duk yan matan nan ko a jikinta ta mike tana karairaya tare da girza sassan jikinta har gaban Na'im ta makale murya kamar me rada sannan ta rungumeshi tare da Rada Masa a kunne Sannu da zuwa,yan mata suka dauke wuta duf suna kallo,Na'im ya dago da fuskarta tare da tallafo kumatunta da hannu biyu yana aika mata da wani mayen kallo me aika sakon zallar so sannan yace kinyi kyau My Heart,nan take ya hade bakinsu waje daya suka dinga kiss,Su Barira suka ja ajiyar zuciya,Zainura ce taga sunki dainawa sai tayi gyaran murya,sannan Na'im ya dawo hayyacinsa yaja hannun Salma tare da cewa muje ki cire min kaya ki canja min wasu wannan sunyi Nauyi,Jamila ta daura hannu aka irin abin ya wuce tunani,kallonsu Salma tayi tace ku dan jirani Kunji, muryar Zainura suka ji tace Ina yini mijin me kyau,jin tacewa Salmansa me kyau ya kalleta harda murmushi yace lfy ya kuke,suka hada baki lfy kalau kalau wlh,ya janye Salma suka shiga,da Sauri ta canja masa jallabiya fara,yana ta faman tabe tabe a jikinta,sai da ta gama ya dan dan rike hannunta da karfi ta kwalla kara,Su Zainura a palo kasa kasa sukace to fa Kunji mun shigesu kuji yan Iska,
Salma ta fara masa cakulkuli yana mata sai dariya sukeyi saman Bed,Zainab tace ko dai abin akeyi,Jamila tace wasa suke dan ubanku yau mun shigaigada mun lalace,Zahrau tace yan iska ne wannan sabon Salo kunga Amarya ba kunya ba tsoron lamyalid walam yulad,Zainura tace munga waje wlh baza mu tafi ba sai munga me sukayi.
15mnt sai ga Salma da Na'im sun fito sunga Na'im da jallabiya,Salma zata zauna yasa hannu a wuyanta tare da cewa Umma zan taya aiki tunda kinyi baki,Ok Honey ayi me kyau,ya fita yana murmushi,
Zainura ce ta fara magana yau naga abinda yafi karfin kuma wallahi Allah canja masa kikayi?Haka kamar jariri Salma? Barira tace gaskiya yan Iskane ku Salma Bazan boye ba,Zahrau tace wai muka ji kararki dukanki yayi ko mintsini?Salma tana dariya tace wasa muke, ke ki bari Dan Manzo ai yanzu har wasa kuke kamar wasu Yara yan firamari?Salma tana dariya tace to mene,To da kuke kyalkyala uwar dariya kuma fa?,Jamila ta tambaya tana tagumi irin abin mamaki Salma tace kuma dan bani da hankali sai na fada muku?wlh Bazan fada muku ba,Zainab tace ke Jamila kema kin san Iskanci sukeyi taya zata fada miki,heeeee suka kwashe da shewa tare da cewa wlh Iskanci sukeyi,Barira tace da aurensu fa ba Iskanci zaku ce ba Sunna sukeyi heeee nan ma dai,Zainab suka ji ta kwashe da dariya tare da cewa wayyo ciki na,Zainura dan Uwarki kin san me na tuna? Wai tsotsar bakin juna sukeyi dama haka akeyi ance a birni,Amma a nan garin yasin ban taba gani anyi ba a tsotsi baki cab,
Zainura tana dariya tace Na rantse Bazan yarda Isyaku ya makamin bakinsa cikin nawa ba,a haka ma gefe nake matsawa idan yana min magana wani hamami wlh kamar yaci daddawa Alquran Bada ni ba,ai ko an aura min shi yasin kaina na gefe,Kinsan rannan yace wai Zainura ina magana kina dauke kai?nace Isyaku kar kace naci ma fuska,dan Allah duk bishiyar dalbejiya dake garin nan da gawayi,ga Alimun yanzu ace har yau kana cikin duhu baka goge bakinka,shike nan matsiyaci ya kai karata wajen Babana har dukana akayi.
Jamila tace yo ai ke da sauki akan Abdullahi na idan ya bude bakinsa kamar mushen tsuntsu ya rube hhhhhhhh suka sheke da dariya,Barira tace yanzu a haka da kike yarda yana rike miki hannu?Zahrau tace duk baku san me rubabben baki ba ai doyin baki yana wajen Shamsiyya Mahamudi wacce akayiwa aure rannan kun tuna? Suka ce yeeeee kwarai kuwa Shamsiyyan gidan na Ilalo,Barira tace Shamsiyya me doyin baki dai dana sani?Suka ce ita domin har yau tana da aure Amma bakin nan sukub a rube ba a zuwa kusa da ita ai Uwarta me dambu ta gado itama haka take,gaskiya Na Ilalo Baban Shamsiyya yana hakuri da Uwarta,
Rannan a masallaci yace a tayashi da addua ko zai samu kudin kara aure.
Zainura ta kalli Salma tace ku tsotsi bakinku da kyau ku gaba dayanku yan kamshine Amma mu kam a wannan fanni billahillazi babu mu a ciki Alquran Bazan yi Couse ba Bazan ma yi amfani da wannan darasi ba, domin ina ji ina gani bazan yarda Idan Allah yasa na auri Isyaku ya baje bakinsa cikin nawa ba,Barira tace ke yo ni aka aura min Ashiru ai kafin ya kawo bakin na Suma,
Zahra'u tace ya kuka gano min bakin Audu me kifi cikin na Aishalle hhhhhh suka sheke da dariya,Ubale me Rake fa?wai wai Zainab ta toshe hanci tare da cewa ai gwara na leka Masai na Shaka ya fiye min,nan Su Zainura suka dinga iya shege a gidan nan Salma tana ta dariya, Zainab tace yo yaushe zan Yarda kwakwarar Runguma ta hadani da Gali,Gali kunga Gali matashi yaro amma ya kashe bakinsa ya rube,idan Gali ya miki magana tun daga jikin kofar can to wlh warin bakinsa har nan wajenmu.
Zahra'u tace Indo fa duk kyan Indo fara ga kyau amma ya tashi a banza tana magana zakice Billahillazi anyi Asarar sabulun wanka,luf a jikinta tasha wanka amma baki ba kanta.
Zainura tace to ai wasu masu auren mazansu kuka suke wai ana Saduwa wajen na bashi hhhhhh Jamila tace sai kace Bomb Zainura aji tsoron Allah,Yasin idan karya nake Allah tsine min,Alquranin Allah Ku tambaya, basu tafi ba sai da sukayi Sallar Isha suka kwashi tuwonsu harda Salma sannan suka mata Sallama sukace sai watarana kuma.
Salma tasha hira yau su Zainura sun kusa illata mata ciki da dariya.
Wata biyu kenan da bikin Na'im da Salma,suna ta zuba soyayya amma har yau ba ayi babban iskancin ba,Rahina watan haihuwarta ya kama,Salma suna yawan zuwa gidan,kuma duk taje har gidan Su Zainura daya bayan daya tare da Na'im sunji dadi sosai,suma suna yawan zuwa suyi hira,haka Na'im ya dauketa har Katsina gidan Rukayya suka yini suka dawo,wajen dangin Malam dana Umma duk suna zuwa su gaishesu watarana.
Yau tun Safe Rahina tana asibiti cikin Katsina zata haihu,tasha wahala sai wurin magrib ta haihu lfy danta kato Namiji,washe gari da Safe da wuri aka sallamosu,yan Uwa da abokan arziki ana ta zuwa barka,Salma da Na'im ma da dare suka je suka ga yaro kyakyawa kato.
Ana gobe Sunan Rahina da dare 8:30pm Salma da Na'im suna kwance Salma ta kira Rahina a waya tace Hajjaju gobe suna wanne suna za a sawa dan Namu? Rahina tace wlh yace ya bani zabi na Zaba duk sunan da nake so,ni kuma wani suna dana taba ji lokacin da naje bikin wata a Kano sunan ne ya birgeni shine nace Insha'allah shi zan sawa dana idan na Haifa,ina son Sunan sosai kalar na Larabawa,Salma tayi dariya tare da cewa ya sunan muji idan da dadi,Rahina tace RAHEEL Salma tayi dariya tace aiko da dadi Allah raya to ya masa Albarka sai gobe zan zo da wuri nan sukayi Sallama ta kashe wayar, saman kirjin Na'im ta kwantar da kanta tana shafa kirjinsa a hankali tace Wai kaji sunan yaron da za a sa gobe? Yace Me? Tace Wai RAHEEL ta rada masa a kunne,tana dariya tace da dadi? Nan take kan Na'im ya dau Zafi ya fara ciwo ya Dafe kan nasa,Salma ta firgita sosai,Na'im ya rike kansa sosai kam ya rufe ido,wurrrrrrr....inda kasan ana tariyo film ya dawo baya haka Na'im yake gani a kansa,ya dade a haka sai da Memory din Na'im ya dawo kaf na baya babu kuma na rayuwarsa wacce yayi a kauyen su Malam.
Zumbur ya Mike tare da saukowa kasa yana kallon kansa yana kallon dakin,Salati ya fara tare da cewa Mummy,Salma ta matso gabansa da mamaki ya tabbatar dai Salmansa ce da yake nema,da karfi yace Salma...yaushe na ganki,ina kika shige ya jawo Salma da take tsaye kamar photo ya rungumeta yana ta murna,a ina muke nan muje gida wurin Mummy,Irfan fa dasu Hunaif? Salma ta fara hawaye tace ni ban gane ba wlh ban sansu ba,baki sansu ba kamar ya? Wai me ya faru dani ne? Salma tace muje wajen Malam da Umma,da Mamaki yace waye kuma malam da Umma ni Mummy nake nema,Salma tace Malam fa baka San Malam ba? Na'im yace ni na sanshi ban sanshi ba,Salma tace Muhd ban son karya,da sauri yace waye kuma Muhd Salma ni nake miki karyar? kalau kike kuwa?Salma tace wlh sunanka Muhd,No..no...kamar baki sanni ba Na'im ne fa,Na'im dinki kin tuna har kike ce min Raheel ne Aljaninki.