← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 80

Sashe 65

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Salma tace ai ki saki jiki ki nuna masa love zaki ji dadi,Zainura ta rungume pillow tare da cewa wayyo Gardi da dandano,wayyo Irfan ni ayi a kaini,Jamila tace Wai Amare wanne kuskus kuke ne? Salma ta kafta musu Ido tace irin dadin da ake ji daren farko mana muke fada mata,Zainab tayi dariya a boye Rahina ma haka tana jijjiga yaronta tace matan aure ai suna sheka karyar zafi,Salma na zata Zafi akeji da gaske Ashe masifar dadi ne a ciki,sauran ma suka ce muma munji labari daga baya Ashe dadi ne,Zainura tace Amma Aishalle kwai yar kutmar....ta dinga mana kuka da safe da mukaje wai da zafi,Rahina tace Ashe karya take ai ta fada min rannan wai maganin da idonku tayi,Zainura ta fado kasa daga saman bed tace to muma Iskanci is somewhere around the corner wlh naga yar iskan da zata min karya nan gaba,oh na ciki baiga gari ba.

Page din nan ya min dadi wlh.

Ayi afwa da typing error pls.

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉

191-195 196-200

Official

By
AsmaBaffa

Wannan page nakine MARCYCOOL

ZAINAB ATIKU SALAMA,SAMEERAN GAYA,HAFSAT KHAIRAN and ASYCOOL godiya me tarin yawa kuna bada gudun muwa.

Gaisuwarki daban ce QUEENMERMU.

Zainura su Salma sai zugata sukeyi,ta daina Jin tsoron first night dama sabo da haka ma take Jin tsoron auren gaba daya shi yasa jikinta yayi Sanyi amma yanzu ba matsala,
Suna zuba hira Umma tazo tare da yan uwan Zainura suka fesa mata turaren Kamu ana guda,haka suka yiwa ma Aisha,Salma tace sai an kara yi mata itama da yake Umma ce sai ta fesa mata itama kamar Amarya,ana gamawa kowacce ta nemi wajen bacci,

Na'im ya kira Salma a waya,Aisha tace dan Allah Salma ki canja daki wannan wayar taki ta kaddara kullum sai kin kusa kwana,Zainura tace kuma fa Zancen Iskanci sukeyi a wayar in kin San haka ne ki koma wajensa mana ayi me gaba daya,kanku akeji cewar Salma,ta gyara kwanciya tare da daga wayar Na'im,can kasa take magana ba ka jin me take cewa,Hlo My Husband kamar kasan am just thinking abt u,really? Ya tambaya,of course 100% sured,can't do without u Dearna,Zainura ta tabe baki,Salma tace oya gist me Baby kaga na kasa bacci,bana iya bacci ba tare da ina Saman kirjinka ba,Aisha ta toshe kunne da hannayenta,Na'im yayi wani murmushin dadi har ana jiyo sautinsa sabo da kaunar Salma dake ransa sannan yace ba wani nan ba haka bane,da hakane me yasa zaki gujeni,kwana nawa ko ganinki banayi,cike da shagwaba Salma tace to ai ka kusa ganina kullum ma,kwana nawa dan Allah? Am doing ths for our own benefit Baby,u sure?yeah,am missing my lollypop,uhm na sani ai zan baka abinka sai yanda kaso nan da Sunday, shagwaba ya fara sauke mata shi ya gaji da jira tazo yanzu,biye masa ta dinga yi da kyar ta lallabashi ya hakura,Sun dauki lokaci me tsaho suna waya sannan sukayi Sallama.

Aisha kuwa Doctor Aliyu ne yake ta faman kiranta taki dagawa, har ta gaji ta mikawa Salma cewar daga kice nayi bacci pls zai damu mutum da naci, Salma kamar gaske ta daga Hello Doctor Aliyu gata nan kusa dani bari na bata ungo Aisha karbi Aliyu Hydar ne,Aisha ba yanda zata tayi tace baza ta dauka amma Salma anyi shu'uma.
Aisha ta karba ta dole tare da cewa hello tana turo baki,yana magana tana shareshi har dai ta dan sake kadan sukayi hira sama sama,Zainura kuwa tuni tayi bacci ta baje angonta Irfan ya kira shuru ta sa wayar a silent,Aisha ta daga tare da cewa hello ya Irfan,dalla bata wayarta,tayi bacci fa,tashe ta ki bata haka magana zamuyi,Aisha ta tashi Zainura ta mika mata waya,cikin magagin bacci ta fara magana Ango ne? Irfan yayi murmushi yace Amaryace,ke Amarya ya bakya kuka ne?ya kamata kiyi kuka,irfan yace akan me zanyi kuka ina son mijina,Zainura bacci ya kara tafiya da ita suuuuu ta farfado again hello waye wai? Irfan yace Amarya ce,nice Amarya zaka ce kaine ai na ganeka,tashi muyi magana pls,bacci a bari sai shekaran jiya sai ayi maganar,magagin bacci kikeyi da girmanki? Tace ae tun jiya ma inayi,jin Sam baya fahimtar me take nufi ya kashe wayarsa taci gaba da baccinta.
Rahina fa itama ta kara gogewa sabo da Zama da sukeyi a kano,ita da Abubakar dinta kamar bashi ba yana wajen su Na'im ana Harka dashi manager company kuma ya koma BUK zai karasa Degree nasa.

Washe gari Friday ranar daurin aure,ranar Sarkin Lebanon kanin Baban su Na'im ya sauka a Nigeria za a daura aure dashi,Su Na'im duk suna wajensa,an gabatar masa da matayensu dangin Mummy da kowa da kowa,yayi kyauta sosai ranar irin ta sarakai ta alfarma,har jinjinawa Malam da Umma yayi yanda suka rike musu Na'im har suka yi masa aure ba tare da matsalar komai ba yayi musu godiya tare da kyautar mota dalleliya me tsada ya bawa Malam, angwaye da Amare da sauran yan biki anci wanka,tsayawa fadar tsaruwa da haduwarsu bata lokaci ne,karfe 11am Central mosque Abuja aka daura auren Irfan da Zainura,Hunaif da Afra,Aliyu da Aisha,Sadaki Dubu Dari biyu ko wacce,Na'im ne ya biyawa ko wanne ango Sadaki.
Daga can Mazan suka wuce walima a wani tsararren waje,matan kuma Mummy ta shirya musu nasu a gidan anci ansha,sannan angwaye suka dawo aka dinga zuba pics an gama komai Sarki ya hau jirgi da wasu daga cikin fadawansa suka koma kasarsu,yana cewa da fatan nan gaba Su Na'im zasu kai masa Amare har kasarsu suga dangi kaf.
Ana gama komai tun 2pm Dj ya fara tashi a gidan nan,Kawayen Aisha wasu duk sun dawo da yawan gaske za asha rawa dasu,yan mata na gaske sunsha wanka na kece raini,suma na Zainura yan schl sun dau nasu,haka Su Jamila sun saje da yan Birni sabo da har kwalliya yi musu akayi komai na yan gayu baza kace daga kauye suka zo ba,cikin abokan Ango Barira tayi saurayi dan Kaduna,Zainab ma wani dan Adamawa ya makale mata,haka dukkan sauran ma sai da suka samu saurayi cikin samari a wasu state din suke,Zahrau ce kawai wani dan 40yrs yake sonta Dan cikin Katsina city ne me kudi da matarsa daya,Zahrau tace ai da irin su Sadisu ko Dan Isiya me Rake gwara me mata hadadde wlh aureshi zanyi ko a jikina.
Chapter 65 · 0% Book details