← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 80

Sashe 56

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Irfan suka dinga ta Shan rake suka ci gyada,kwakwa da dabino tare da yan matan nan,Na'im da Abubakar ma suka dawo ciki za a Sha aci dasu,Salma nata ya dawo,Raken take barewa ta gutsiro da hakoranta ta mikawa Na'im ya shanye,Zainab tace Iskancin kullum gaba yake,Zainura tace ya ci uwar na da yanzu na birni akeyi,Jamila tace inama muna nan da munsha kallo,Zainura tace kiyiwa Abdullahi naki? Jamila tace Allah kiyaye kazamin Banza,Zainab tace yo saida kika bari ya dan rage Zafi zaki ce Kazami me yasa da baki ji,Jamila ta radawa Zainab sabo da dadi heeeee sukayi shewa.
Zainura tace dan uwarku Audu me kifi kara lalacewa yayi wlh kun San da ya min magana tab Wal hamhamatu,S alma tace da Hamami,Hunaif ya rike ciki sabo da dariyar yan matan ta masa yawa,Irfan ma ko tunawa yayi sai yayi dariya,su yan kauye watarana ba ruwansu da kunyar kowa harkar su suke ko kaji ko ka toshe kunne,Salma ma biye musu take Ashe cewar Na'im.

Na'im yace dole Ashe shi yasa sanda muna garin nan ba kya so su tafi Ashe gulmar mutane kukeyi kuna zaginsu,Salma tace ba ruwana ni,Barira tace ai sai dai Allah ya yafe amma fa baza mu fasa ba,Na'im ya kalli su Hunaif yace Ku kuma ko a jikinku kuna cikin Mata harda matan wasu fa,Irfan yace idan akan matarka ne ka dauketa Ku tafi mana baza ka takura mana ba.
Barira tace bayin Allah Ku tayani jaje Sabon Gidan Tafida ya kawo kudin Aure na kuma Baba yace ya bashi,da Sauri Zainura ta daura hannu a ka tace kin mutu kawai,Sabo fa Barira? Jamila tace ya wuce wai wlh,Zainura kin tuna Sabo me suma kamar ta gyartai,Zainab tana dariya tace kin shiga Uku Barira hannunsa kadai idan ya daga hammata wlh gwara ki leka kanki cikin masai ta gargajiya Sabo da Hammatarsa inba Alquran sai kin suma ba Allah ya konani,Salma tace nafa San Sabon ko ba dan Ball ba? Rahmatu tace ras ma kuwa kin gano shi,kullum shi a dole Bature wai sai yayi ball yake jin dadi,ya hada uban gumi da wata jercy dinsa ja an rubuta Kaka, suka sheke da dariya,Zainura tace shegen hakori kamar kacar keke Irfan suka sheke da dariya gaba daya,Barira tace Ku dai Ku tayani jaje Wallahi Irfanu (Irfan) idan ka ganshi kamar daga cikin toka aka tonoshi,Zainura tace ga farce cako cako kamar dan Damusa ko uban wa zai yakusa oho ,ai nan gayune cewar Salma,Na'im ya make mata baki ta rike wajen tana shagwaba tare da cewa da Zafifi Allah zan rama ne.

Zainab tace kai dan muhammada Rasulillahi Ku dinga salalawa junanki kamar zaku ciye juna,wai haka ake wannan soyayyar ne irin taku ta shiga da masifa baza a dinga hutawa ana sakewa ba sai dai a junanku,bakwa gajiya da juna,ni wlh irin wannan damuna zatayi kale kale a wajen miji baza ayi Harka da Alumma ba sai iya miji,Barira tace ke kyalesu zamu koyi Darasi,Zainura tace lallai Sabo zaisha love,Barira tace ai wlh ya matso kusa dani ma sai na tsandara masa mari,Jamila tace ke ki bar ganin Sabo haka figigi jikinsa kamar itace haka yake ke bakya ganin kaurinsa,Zainura tace da zaki kyasta Ashana a kauriin Sabo kamawa zaiyi da wuta sabo da bushewarsa,nan ma suka kara shekewa da dariya,Barira tace ko a gari ba dukansa idan fada ya kama,Rahmatu tace bare kice zaki mareshi ai gwara ki cijeshi,Barira tace kaji banza cizo salon na karto dauda da hakorana kenan,Sabo bazai taba Jin dadi ba idan ya sake ya Aureni kin San Allah yana Palo ina ciki,yana ciki ina Palo,Zainura tace ga shawara idan ta tabbata an daura ki kulle shege ki tsiyaya petir kina daga waje kice ya sakeki ko ki cinna wuta,Rahina tace a'a ai tayi sake an daura idan ya saketa ta Zama bazawara ba daraja,kawai ta masa tun a waje yace ya fasa aure,Zainura bada shawara kinfi kowa iya mugunta,Salma tace ni zan bayar ki samu idan yazo zance ki dauki dutse ki shammaceshi ki faki Ido ki rotse masa kai,ki tabbatar jini ya zuba zai ga lallai zaki iya daukan ransa a waje zaice ya fasa,

Salma ta bawa kanta amsa tace idan yaki yarda fa kun san Sabo da taurin kai shegiyar Hammata kamar bishiyar kaya cako cako hhhh suka sake dariya,Har Na'im dariya yake ta yi Salman tasa ma Ashe shu'uma ce bai sani ba,Salma tace Plan B ki tafi da Reza sabuwa sai kuna hira ki lallaba ki dora masa ita a gadon baya kawai yaji kyat kin yankeshi kice idan ya aureki da Wuka zaki farke masa Hanta,Zainura tace plan c ki tafi da kwalabar lemo ki fasa ta a jikin katanga kiyi kansa kamar da gaske zaki caka masa,zaiga fa lallai kasheshi zakiyi zai fasa aurenki,amma idan har ya daure ya aureki haka am so sorry Barira sai dai buzunki domin sai ya dauki fansa yaci ubanki a gidansa,wlh sai kin raina kanki,Hhh Hunaif yace ga tawa Shawarar kawai ki lallabashi yace baya Sonki da kansa Barira tace kai maye ne wlh karata ma zai kai gidanmu baka San muguntar Babanmu bane gashi masifaffe,Hunaif yana dariya yace to Kiyi addua kawai mafi Alkhairi,Zainura tace sannu Ustaz to Sabo ba Alheri bane ka auri mutum irin Sabo Kazami ina khairi ciki,ga taurin kai baza a nuna masa gaskiya ba,komai shi ya iya nasa ne me kyau,ba a isa an canja masa ra'ayinsa ba bare ace Barira zata iya koya masa tsabta,bazai yarda ba,Barira tace ai sabo gani yake yafi kowa wayewa da komai a duniya,kai ko kai baka isa sabo ya saurari shawararka bare mu na kauye.

Hunaif yace dan Allah gobe a nuna masa Sabo ya ganshi,Salma Da Na'im sai kus kus sukeyi a gefe su kadai,Zainura tace dare yayi goma ta wuce Ku tashi mu tafi gida,gaba daya suka Mike tare da yiwa su Rahina Sallama sai gobe,Abubakar ya rakasu ya rufe gidansa,ko wacce budurwa ta tafi gida,Irfan da Hunaif har gida suka Raka Zainura sannan suka koma gidan Malam cike da nishadi,Hunaif yace amma wanne yan mata kwai yan banza,ga surutun tsiya ko baka so sai kayi dariya,Irfan yace irinsu Zainura haka Allah yake yinsu komai wayewarsu duk inda suka shiga sai anci dariya,abin dariya ne dasu,haka wasu suke ba yanda za ayi Ku hadu basu bada dariya ba.

Gaba dayan su Irfan su uku bangaren su Na'im da suka zauna nan ne masaukinsu,Irfan da Hunaif suna bed room saman Bed,Na'im kuma a Palo ya samu an shirya masa yar katifa madaidaiciya,shi bazai iya kwana shi daya ba Bai ma saba ba,Salma kuma tana wajen su Mummy can zata kwana,Na'im tunani yayi dabara ta fado masa wurin 12am dole so yake ya bar wani tarihi a kauyen shi da Salma,bedroom din ya shiga ya tashi Irfan,Irfan cikin bacci yace wai dan Allah mene haka ka damu mutane kamar kai kadai kafi kowa matar aure,me za ayi maka,Na'im ya bata rai sannu yayana gadonmu zaka daga mana Ku koma Palo ai ba gidanku bane,

Hunaif yace wai bro ba kwaya kakesha ba?kai wai kullum a Iskanci zaka kare,to mu bazamu fita ba,kun San ai ba kunyarku nakeji ba wlh Ku fitar min daga Bedroom ai ba gidanku bane,Irfan yace muje Hunaif idan ya fara masifa wlh bazai bari muyi bacci ba.
Suka koma Palo saman katifar,shi kuma ya kara gyara bed din ya fita tsakar gida yana ta faman kiran Salma a waya tana bacci bata daga ba sai da ya kira yafi sau goma,Sannan Dada ta farka a tsorace tace Innalillahi kunnena za a kashe min dodon kunne ke tashi ki daga waya ko na jefarta waje,Salma ta farka tana ganin Na'im ta Marzaye dan kar ta tashi Mummy can kasa tace hello Honey,preetyna fito ina tsakar gida,kai dare fa yayi Honey kuma Mummy da Dada fa zasu ce ina naje,su suke aurenki? Sanda aka daura suna ina?kizo ko na shigo na fadawa Mummy da kaina a gabansu ma Daukoki zanyi bare wata Dada kunyarta zanji?
Salma tace to tsaya karka zo gani nan,Sai da Salma ta faki Ido ta tabbatar sunyi bacci yayi nisa ta lallaba ta Mike tare da Zare Sakatar dakin,Mummy ta farka dama taji Hirar da Salma tayi,tace ke dawo dan Ubansa ya kwana a waje,baza kije ba,Salma ta kwanta tayi luf,Na'im ya kara kira Salma tace yana kira fa kuma a waje yake gwara na fada masa kin hana sai ya tafi,Dada tace kyaleshi ya bushe,Salma tace kai Hajjaju,Na'im ya kara kira Salma ta daga tace Mummy ta hana,Na'im yace ta bawa Mummy wayar,Mummy ta karba yace Mummy yanzu fa zata dawo Paracetamol zata kawo min kaina ke ciwo idan baki yarda ba to ta baki ki kawo min da kanki,jin yace a bata ta kawo masa sai Mummy ta yarda lallai gaskiya ne,Salma tana ji tana dariya a boye,Mummy tace dauko maganin na gani a Idona sai ki kai masa,Salma ta duba ta dauko paracetamol kamar gaske tace gashi,to jeki ki dawo da wuri,tace to.

Dada tace ke dai kwai sakara yara suna miki wayo to bari ki gani baza ta dawo ba zaki ce na fada miki.
Mummy tace Hajiya ai Salma bata da wasa da dai Zainura ce nasan zata aikata amma Salma ai akwai kunya,Dada tace Salma wlh tafi Zainura Fitsara Salma a boye take yi,Zainura kuma dan tana da baki ne ita barta wajen dariya a yaran yanzu waye Ustaz?
Mummy tun suna jiran Salma ta dawo suka ji shuru har bacci ya kara tafiya dasu.
Chapter 56 · 0% Book details