← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 80

Sashe 13

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kayan jiya data cire ta dakko zata sa ya Mike tare da fisge su ya hada har Night wear data cire ya fice dasu,part dinsa ya shiga ya kwaso mata wasu kayan ya kawo mata ba magana ta karba ta shirya ciki lace riga da skert tasha kyau kamar sarauniya,abinci yace me zaki ci? Hawaye ne ya zubo mata sharr tace na koshi,tausayinta yaji yace am so sorry for yestersay ok? Sai lokacin ta kalleshi tare da sakin murmushi me tsada wanda ke gigita mazaje,dimple dinta ya loba tace na hakura ai dama ba fushi nayi ba,kawai kace ne kar na kara kulaka jiya shi yasa naji haushi,yanzu na kulaka?ta kara tambaya,yeah kiyi ta kulani kullum kullum dariyar Jin dadi tayi tace to,ashe kina iya fushi haka? Ae aini duk nafi iya fushi idan baka kulani sai na koma kububuwa ma,ko na koma tolo tolo,dariya Na'im yayi tare da cewa kefa kana da shirme mene wannan Tolo Tolo oya muje dining to ki Zaba abinda zakana ci,a dining taci abinda take so sannan yace tazo suyi game,Ya kunna musu kowa ya rike Handle suna PS abin ya bashi mamaki yanda ta iya sosai bugawa,yace wannan ma Raheel ne yana
Dinga koya miki?tace yes tana danna handle nata suna ta dariya da Surutu sun cika palon da hayaniya,haka Irfan Ya iskesu shima da sauri yazo suka buga da Salma ta cinyeshi tas,Har tafawa sukeyi da Na'im idan ta cinye Irfan,Hunaif ma yace sai ya cinyeta rainasu tayi ana farawa ta cinyeshi da kansa ya gudu,Irfan ta kalla ta kalli Na'im tace kuna kama,sannan taci gaba da cewa baza ka daina abinda kake ba ko sai Allah ya konaka?Irfan yace me nayi kuma munafuka?yau Bilkusu me kukayi a Hotel dazu?kunya ta kama Irfan,yace pls ke aljana ce wai? Baki ta cuno ni ba ita bace amma ai naga Bilkisu yar gidan Gomnan Kwara state ko ba haka ba? To ki rufa min asiri karki fadawa Mummy kinji,to kayi kokari ka daina idan ba haka ba wlh a gabanta zan fada mata,Na'im yana jinsu yace Irfan kayi asararren na banza Banza ne
halinka,(Irfan kayi asarar Halinka na banza ne).

Irfan yace uhm amma ai Bana Shan alcohol ni,Na'im ya hade rai ya Mike ya bar palon,Irfan yace sai ki dage ki dinga Sallah sannan sai kiyiwa wani Wa'azi ya Mike fuuu ya wuce Bedroom.

Kwanciya tayi a sofa tana kallon American film na turawa kuma na love,tana kallo suka fara Romancing juna har Sex Salma ta rumtse Ido tace da gani za a ji dadi a wannan Harka bari muyi aure da Raheel,hade rai Na'im yayi domin yana jinta ya sakko daga samansa sharewa yayi kamar bai ji komai ba,key din mota ya dauka zai fita tace nazo muje? Hospital fa zanje cewar sa,ae naji zan bika pls,ok dakko mayafi muje,kalar kayan ta dauko ta bishi suka fita tare,yana Driving tana ta faman Surutu,ko da suka je Office tana saman Table a zaune sai jagwalgwala masa takardu takeyi,dukkan masu ganin Doctor me Imani tunaninsu kanwarsa ce tazo yau, shagwaba take ta yi ta hana ayi aikin ma,ita wai sai an tafi yawo.

Hashim da Matarsa Maimuna kullum a fada suke a tsakaninsu kai kara har Hashim ya gaji ko me yayi mata sai ta fito tsakar gida wajen matan gidan Maimuna ta kwashe ta fadawa matan gida ayi ta shewa,suma sauran mata duk sanda mijinta ya kwanta dasu haka suke kwashewa su fada a junansu,
Maimuna ce zaune cikin dabar matan gidan tace Sakina kin San jiya Gogan nawa kwana yayi yana kuka da ihu ai maganin nan yayi,ke kuka fa wiwi wai shi mutuwa zaiyi ma idan bani, sai ya tafi Bahar Maliya a kasa sannan ya tsunduma ciki,matan gidan suka rafka shewa heeeee ayyiriri,matar Shehu tace shege yaji harkoki,kin San ranar dana Sha nawa Shehu ko masallaci kasa zuwa yayi,yara suna bacci zasu je makaranta ina so naje wajensu na gyara su amma Shehu yace Bai San zance ba,ke fada karce ni da Malam Musa cewar matar Malam Musa itama tace ai ranar ban taba Sanin haka Malam yake ba sai ranar,nace Malam Almajirai sun fito karatu fa yace dan Ubansu su shekara da jira bazan je ba,ke ni daga yau in kika ce na daina koya musu ma zan bari,in banda takurani da akeyi me akeyi,nan ma Suka sheke da dariya Maimuna yanda suke zubar da mutuncinsu kamar ba suraka da suraka ba ko wacce bata kunyar ko wacce girma da mutunci babu,Maimuna ta San me uban Hashim keyi haka itama uwar Hashim tasan me danta keyi,Allah shirya haka ake samun wasu da dama suruka tana batsa gaban matar danta sosai,dukkan matan gidan sinkai su goma haka suke wannan iya shege.

Mummy da taje gidan Dada wani malami me yaki da Aljanu suka je wajensa can wani kauyen Kebbi takanas suka daukoshi yayiwa Na'im maganin Aljanu,
Na'im ba masifar da baiyi ba amma haka aka dinga masa magani kala kala har aka samu Aljanin yayi magana shine dai Raheel wanda ke jikin Salma cikin nasara Raheel yaji azabar ayar Allah ya bar jikin Na'im gaba daya dama ba wani shigarsa yayi ba zuwa jikinsa yakeyi.
Suffarsa yayi amfani da ita yake zuwa wajen Salma zance,sai yanzu su Mummy dukkansu suka gane zancen Salma Ashe yarinya da gaskiyarta Raheel ke zuwa mata a suffar Na'im.
Maimakon Su Dada su hada da Salma suyi mata magani itama tsabar son kai da Salma kuma ita bata da gata basuyi ma zancenta ba iya Na'im kawai suka yiwa ya warke tsab,Salma tana nan da cikinta sai girma yakeyi tana Shan wahala.

Irfan ne ma yayiwa Momma dinsu maganar ayiwa Salma ma amma ta share zancen ma Sam.
Malami ya koma gida cike da makudan kudade yana murna,
Na'im ya warke yanzu mace ko wacce ba sai Salma ba zata iya tabashi a zauna lfy kome zaiyi bashi da matsala,Mummy bata San wannan magani ba gata tayiwa Na'im ba domin Raheel kariya yake bashi sabo da zai iya Zama fasiki,sha'awarsa dole sai da mace kusa dashi, taimaka masa yakeyi shi yasa duk masifar son iskancin Na'im da kuma son ya hole Raheel ne yayi Kane Kane ya hana hakan sabo da Salman sa,idan da Mummy sunyi hakuri akwai lokacin da Raheel ya ibama kansa dole zai bar jikin Salma da Raheel,sai gashi rashin sani yafi dare duhu har Mummy suna nuna son kai nasu kadai suka sani shi zasuyi wa magani.
Tunda sukayiwa Na'im magani kullum yake jajibo yan mata Allah ma yasa yana da tsoron Allah da kyankyami iya Romancing kawai yakeyi amma baya yi a gaban Salma bama yaso ta sani,kawai dai tana ganinsa cikin yan mata iri iri abinda ke damun Salma yanzu kenan kishin Na'im takeyi kamar ta kashe wata haka take ji dannewa take dan yi.
A gaban Mummy yake kawo mata su yini a gidan amma sai tace just normal frnds ne bata San me sukeyi ba har ga Allah,shi kuwa Irfan sabo da tona masa asiri da Salma keyi ya rage halayensa sai jefi jefi,Aisha kuwa tana nan yanzu ma take ganiyar shaye shaye da lesbian,Hunaif sai Club kullum,sabo da Dada ta hana su komawa turai sai dai da yawo,yanzu Private university sukeyi a Abuja ta masu kudi.

Kamar kullum yau Weekend Na'im yana gida a part dinsa,Sha'awa ta motsa masa ya kwankwadi giya da yawa amma baiyi bacci ba,Ya rasa inda zaisa kansa,wata frnd dinsa Balarabiya da suke aiki a Embassy tana mugun sonsa ta hadu,kiranta yayi a waya tazo ta dan taimaka masa ya samu sauki,Dama Balarabiya Nadiyya abinda take jira kenan ko a kirjin Na'im ta kwanta,20mnt sai gata kuwa ta Parker da arniyar motarta,Lokacin Salma na Palo ta cakare cikin doguwar Riga fitted,ko wacce sura ta bayyana,Mummy da dukkan yan gidan suna Palo suna hira cikin harshen Turanci,Mummy tana musu fada hausa zasuyi dole.

Kwas kwas Nadiyya ta shigo tasha kyau kamar a saceta,takalminta cokalelen gaske,da Ladabi suka gaisa da yan gidan,turai ta ratsa su kawai tace Na'im yana ciki?Suka ce yana part nasa taje,Mummy tace Salma rakata Part dinsa abokiyar aikinsa,Salma ta hade rai kamar an Aiko mata da mutuwa ta wuce gaba,Nadiyya na binta a baya har hadadden part din Na'im,can kuma su Mummy ko a jikinsu hirarsu kawai suke ma.

Na'im yana jin Knocking ya mike daga shi sai singlet da nicker,bude kofa yayi fuska dai ba rahma,kawai Salma ta bangajeshi ta wuce dakin kamar nata,tace bakuwa na kawo ma ta fada saman Bed din tayi kwanciyarta tace yi Sauri kuyi hirarku zan fita da ita,
Cikin Hausarsa da ba wani kwarewa yayi ba yace Mari kina son karba ne ko? Bana sho na iskanci,u knw me Better sheni iya mareki ko na Maki duka duka da yawa( kina son na mareki ko?kin sanni sosai zan iya dukanki sosai bana son Iskanci fa)

Baki Salma ta tabe tace ba inda zanje sai kun gama,Nadiyya kuma bata jin Hausa daga turanci sai larabci,harara ta zabgawa Salma tana tambayar Na'im me take nufi? Na'im yace ai kanwarsa ce bata so ayi having Sex shi yasa,Nadiyya ta gallawa Salma harara tace hey u better lv ths room before i give u a dirty slap.
Chapter 13 · 0% Book details