← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 80

Sashe 2

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasarsu daya ta rage tal a duniya wato ta bangaren uwa Dada Babar Hajiya Zuwaira Mummy, Zuwaira mutuniyar kirki ce ga son yan Uwa da dangi,kuma ga taimako tana son kasarta da hausawa shi yasa tunda mijinta ya rasu tace baza ta kara aure ba yaranta zata rike ta dawo gida Nigeria kusa da yan Uwanta,Arzikinsu yayi yawan da duk wani dan uwan Zuwaira dake kauye tuni sun maidasu cikin birni,Dada kakarsu Babar Mummy ma gidanta daban a cikin Abuja da yan aikinta, sauran kuwa duk suna Kebbi cikin city suna Jin dadi,maza da mata Zuwaira tana nema musu aiki tana biya musu kudin makaranta,ta ko ina Zuwaira halayenta sunyi bata da makusa,haka ma mijinta Al'awwal Abban su Na'im kafin ya rasu mutumin kirki ne na gaske.

Na'im da yan uwansa suna da tarin ilmin addini dana zamani,kuma alhmdllh suna aiki dashi kasancewar sun samu tarbiyya sai dai yanayin Zamansu a kasar waje dole suna abubuwa da basu dace ba da Rayuwar tamu kasar ko nace rayuwar musulmi,baya ga haka dama dole a samu dan Adam da laifi dole ne sai dai wani yafi wani.
basu dauki mace Nada banbanci da maza ba Sam,yanda zasuyi kawance da namiji haka sukeyi da mace,gwara ma Na'im shi baya neman mata sai dai tarin frnds mata kamar me hadadde wayayyu masu kudi amma kuma yana son yayi Sex,yana so yayi rayuwa dasu yana da karfin sha'awa amma abin haushi ya rasa dalili da mace ta rabeshi da niyyar Jin dadi sai yaga ta fadi ko ta bugu da jikin bango,kuma nan take zaiji ya tsaneta sai yaga ta rikide ta koma mummuna me suffa marar kyau,duk abinda ke birgeshi a jikinta sai yaga sun koma abin kyama,abu daya ne ke rage masa Zafi Shan giya sama sama bada yawa ba,sabanin su Irfan basa Shan giya sai dai suna dan having sex da mata amma bada yawa ba sai lalura ta taso,
Aisha kuwa zaman turai yasa mata ta saba da shaye shayen kwayoyi da syrup, sai Lesbian da ta fara jefa kanta ciki, amma dukkansu suna addini sosai kuma kowa yasan laifin da dan Uwansa ke aikatawa.

Na'im Babban likitan kwakwalwa ne a Abuja Mummy ta bude masa katafaran Hospital na gani na fada wanda babu kamarsa likitoci ko ina a ciki,sannan kuma consilor ne a cikin Embassy na kasar lebanon dake Abuja,sune masu yarda a baka visa kasarsu sune masu interview cikin lebanon Embassy, haka kuma yana kula da dukkan business da companies nasu dake kasar Nigeria,shi ke kula da komai na dukiyarsu dake Nigeria,Irfan kuma me Kula dana kasashen ketare,Hunaif ma yana taimakawa.
Na'im duk yafi yan uwansa kyau da komai ma,jinin Sarauta jinin kudi,gadon Arziki,ga kyau shine kadai ke nuna Sarauta a jininsa take,kana ganinsa kasan ya hada jini da Sarauta, matsalarsa Shan giya kadan,tarin kawaye mata amma fa masu class ba karamar wacce ta isa bace zata iya ganin Na'im har su hadu ba, ba a haduwa dasu wajen kananan yara masu karamin karfi,

Matsala ta biyu bashi da mutunci idan yaga dama yanzu zai wulakanta mutum,ga isa takama da gadara,baya saurarar rayuwar wasu bare har ka bata masa rai ko kuma ya wulakanta talaka yaushe ma ya shiga harkarka da har zaku samu matsala,kuma ko uban me zakayi bazai ce ka daina ba wai shi Bature ba ruwansa rayuwarka ce,yasha kama Aisha da mata suna Lesbian Bai taba ce mata ta daina ba kyau ba,haka kannensa ko me zakayi Good for u rayuwarka ce,
Akwai barnar kudi wajensa yanzun nan sai yayi wasa da dollers ba abinda ya dameshi mahaukaciyar kyauta yakeyi baya karama,ko zakka idan zai fitar to sai wanda ya bawa ya washe,kyautar kudi a wajensa ba komai bane,ko ina a motarsa kudine,haka kayansa ma a aljihu ma har cikin takalmi idan yaga dama Dollers zaka gani ya fyalla ta a cikin takalmi ya baka kyauta,
Watarana mutunci watarana babu sai tsiya,haka ma'aikatan sa duk sun San halinsa da kallon Banza watarana watarana fara'a.
Hospital idan yaje tab ai duk patient din da sukayi dace ya dubasu da kansa ba sauran Doctors dake aiki karkashinsa ba to zai wahala patient ya biya kudi kyauta zai masa komai komai girman cuta.
Shi yasa yanzu sunansa ya koma Me Imani,Doctor me Imani,baya Jin hausa sosai sai dai akwai me karasa bayani yanda zai gane idan yana mu'amula da hausawa,shi yasa ma ya dan iya hausa da yawa,a hospital har so ake yazo aiki ranar Monday da Tuesday yake zuwa suna Shan dariyar hausar tasa,wanda basa Jin hausa ya musu turanci amma Mummy dukkan ma'aikata da tasa aka Eba a Hospital Hausawa sunfi yawa sabo da kishin kai, kusan Kullum sai yaje wajen Dada kakarsa sun gaisa tana kara koya masa hausa.wannan kenan nan gaba zaku ci gaba da Jin halayen Na'im wanda ban fada ba sai gaba zaku jisu yanda suke,amma wannan sune Manyan.

Hanyar Abuja Can cikin daji akwai wata ruga ta yan Fulani usul ciki,amma duk da haka rugar a kusa da gefen titi take,tana da girma ba laifi,harda makaranta primary da secondary tare da islamiyya,Fulanin dake wannan dajin ko hausa kadan suke ji basu iya sosai ba amma suna Jin hausar,
Wata Dattijuwa ce kyakyawa me cikar haiba ta fito domin zuwa asibiti dake Suleja Hanyar Abuja kusa dasu,Dattijo yana rike da hannunta da Alama mijinta ne sai sannu yake mata,haka suka shiga mota har suka karasa wannan asibiti,bayan an duba Lafiyarta an tabbatar rashin haihuwa ce ta kawota tunda likita yace baza ta taba haihuwa ba haka ma mijinta shima,cike da tawakali suka siyi magunguna suka fito wajen me gadin wannan asibiti suna hira dashi sama sama,me gadi ya kalleta tare da cewa Hajiya idan baza Ku damu ba ko zaki iya rike min yata guda daya danake da ita?tunda bakya haihuwa kuma na yaba da halayenku zan baku tarihina idan kun amince sai na bar muku yata kyauta Ku riketa Amana.
Sunana Ahmad wanda akewa lakani da Tall Man a cikin Garin Borno muke da dangina tare da dangin matata wacce Allah yayiwa rasuwa kwanan nan,Matata yar Asalin Nijar ce buzuwace gaba da baya amma danginta kaf suna Borno a unguwarmu,Yan uwanta da kuma kanin babanta sai sauran danginta amma iyayenta dama sun Dade da rasuwa,Bayan munyi aure da shekara biyu Allah ya bata ciki ta haifa min yata sunanta Salma watan Salma 7 a duniya Allah ya karbi rayuwar matata Khairat wacce Hawan jini ya kama da karfin gaske,
Bani da Uwa bare uba nima bani da yan Uwa mata sai maza a zamanin nan idan na bawa dan Uwana namiji rikonta matar zata iya gallaza mata tunda ba shine zai zauna da ita ba,haka idan nayi aure ban san wa zan aura ba,haka na hakura na bawa dangin matata Khairat yata Salma,amma yau Salma shekarta biyu a duniya wahalar rayuwa take Sha a hannunsu rayuwar yanzu ba imani ba tausayi,

idan kun yarda muje garinmu kuga gidanmu ayi yarjeniya da dangina da dangin matata kusan juna sai ku tafi da Salma wajenku Ku rike ta Amana,sai Ku dinga kaita wajen dangin ubanta dana uwarta suma zumunci kawai amma na baku ita halak malak Allah yayi jagora kune iyayenta daga yau,Murna wajen wannan dattijai ba a magana,kamar wasa ya dauki Hutu washe gari suka tafi har Borno state,Dukka sun gaisa da danginsa dana Khairat Babar Salma,hannu biyu suka karbesu amma da gani Salma a cikin wahala take ba a kula da ita Sam,haka yayi musu bayani ya dauki Salma da kayanta na sawa ya bawa wannan dattijai da sharadin zasu dinga kawo Salma ana gaisawa da danginta suna zumunci,cikin dangi babu wanda yace kar ayi haka su zasu rike kowa mukus yayi harda fatan alkhairi,cike da murna dattijai suka koma gida suka nuna Ahmad Tall Man baban Salma ga kowa dake da alaka dasu a rugar Fulani duk da cewar yan uwan nasu suma kusan duk sun kare sai kadan daga ciki sai makwafta da abokan arziki,

Kamar wasa tsakani da Allah suke rike Salma ko yarsu baza taji dadi haka ba sabo da gatan da suke nuna mata,ubanta Tall Man idan yazo ganin yarsa dadi yake ji ba kadan ba yana shi musu albarka,haka mutanen gari ma,Salma sai abinda take so shi yasa ta taso cikin shagwaba da tabara ta gaske,amma suna bata tarbiya ta gasken gaske, tana da shekara biyar suka sata a schl tana ilmin addini dana zamani,kamar yanda alkawari yace suna kai Salma Hutu cikin danginta tayi Hutu acan,duk Hutu a Borno take yinsa Affa da kansa yake kaita can abin sha'awa.

tana da shekara takwas Ahmad Tall Man mahaifin Salma ya rasu sakamakon ciwon Koda daya kamashi ba tare da doguwar jinya ba,masu rikon Salma sunyi kuka sunyi zaman makoki,Salma tana primary 4 aka fara ganewa kamar tana da tabin kwakwalwa,sai aganta tana ta maganganu ita kadai,ko aga tana dariya ita daya,wani lokacin kuma tayi ta kuka tana shagwaba,sai ta dinga kallon waje daya,watarana kuma tayi ta wasa tana maganganu kamar da wani takeyin maganar,sai aga tana shafa iska ko ta rungumi iska,a schl ma haka takeyi,watarana kuma aji tana ta rawa tana cashewa kamar tana Jin kida har karkata kunne takeyi,bata da kokari a sauran Subject da dama banda English da French,amma fa Idan anzo exam,a class duk tambaya zata amsa amma kuma bata da kokari kan kowanne subject sai dai English kadai sai French idan ana musu,har kure malamai takeyi indai akan yare ne to baka isa ka kureta ba.
Chapter 2 · 0% Book details