Sashe 21
Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Salma ta warke fes Aljani Raheel ya tafi har abada amma matsala daya har yau memory dinta ya goge bazai dawo yanzu ba sai zuwa wani lokaci me nisa,sai anyi wani abu wanda zai tuno mata baya sannan ta dawo tana ganewa,amma asibitin basu gano matsalar ba,kawai suka tambayi Salma tasan garinsu da gidansu tace ae,dama kafin a fara maganin Aljani taji ana cewa wani kai dan Katsina shike nan ta rike,suna tambayarta tace Katsina state take ita,a wani kauye tasan garin zata iya zuwa da kanta a bata kudin mota,nan take Doctor ya kaita tasha ya sata a motar Katsina ya bata kudi Dubu biyar sannan ya biya kudin motar,su dama asibitin arna sunfi yawa basu wani damu da bin dokoki ba,amma ya za ayi in ba sakaki ba a kasar nan ta Nigeria a sallami mace ta tafi ita kadai kawai ba bincike,haka ake wannan sakakin iri iri a Nigeria rayukan mutane na salwanta,Salma dai dama ta gaji da asibitin ne so take ta gudu shi yasa tayi karya amma bata San wace ita ba.
Mummy hankalinsu ya tashi bacewar Na'im sati guda ba shi ba labarinsa,har kafafan radio an bada sanarwa amma shuru,haka anyi nema an gaji,Mummy ta sanarwa dangin uban su Na'im gaba daya dasu Mummy su Dada da dangin su Na'im na uba su Irfan duk sun tafi saudiya zasuyi Umrah da addua akan Allah bayyana Na'im,Mummy kullum kuka ba sukuni haka su Irfan ma.satinsu uku suka dawo Nigeria ana ci gaba da addua ba dare ba rana,an kai report wajen hukuma an watsu ana neman Na'im amma ba labarinsa,Uk Embassy ma ambassador ya bada sanarwa ana ta nema.
Salma kuwa Motarsu ana fara shiga Katsina dai dai wani hanyar kauye wasu mutane sukace a saukesu itama tace nan zata sauka,Hanyar kauyen biyu ce da kauyen da Na'im yake da kuma wani sai tabi mutanen daya kauyen da Na'im baya ciki,taje ta gama garari a kauyen tana neman aikin karfi ko wanda zai tallafeta ta zauna a gidan sa kowa yaki yarda,sai ma aka dinga cewa barauniyace,ko me satar yaran mutane,bako ba a San halinka ba,har wajen magriba tasha wahala sai ruwa da tasha a wani Borehole tare da siyan Alala taci cikin kudin da Doctor ya bata, machine ta hau ta fito daga kauyen ta ce me machine ya kaita wancan kauyen ko anan zata samu me taimakonta,Wato kauyen da Na'im yake kenan,har nan aka kaita ta biya me machine ta nausa cikin kauyen me kyau da tsari,tafiya take duk wanda ta gani sai ta roki taimakonsa wajen kwana ko aiki,ko kulata ba a ayi sai dai ma a zageta,ta gaji har anyi sallar Isha tace Wai ni wace ni ne?wacce bakin Uwa ce ni haka, wacce bani da Sa'a sam,ko dai tsinanniyace ni ban sani ba,ina Mamata?Babana fa? To ni ina jin dai jaka ce ni,bakin masallaci ta koma ta zauna mutane anyi sallar Isha maza ana ta fitowa still Salma neman taimako takeyi amma ina sai dai ma wasu su bata sadakar Naira biyar ko goma,Malam Magaji da hadadden Handsome Na'im yasha wanka na kece raini tunda kayansa na gida yake sawa,Da gudu Salma ta tare Malam tana neman taimako Malam da tausayi ba ruwansa yace yarinya na sauki namiji ma bare mace dauko akwatinki mu tafi kin samu gida,ni bani da yara ban taba haifa ba amma na sameku muje,Abinda zaku Sha mamaki readers Salma sanda tazo ba akwati a hannunta amma sai gashi Raheel itama ya ajiye mata a gabanta katuwa kayanta na sawa hadaddu manya da kanana,Allah sarki Raheel yana gefe yana kuka wiwi an rabashi da Salma cike da bacin rai yace tunda na goge musu Memory ai shike nan baza su taba auren juna ba,tunda ba wanda zai tuna da wani bare kuma sannan yasa musu baza su so juna ba,Allah ne yake hada Salma da Na'im ba ta dalilin Raheel ba,shi kanshi Raheel yasha mamakin hakan ikon Allah amma ba yanda zai kara shiga jikin dayansu bare ya raba musu gari again, kawai sabo da tsananin son Salma da yakeyi yasa itama ya kawo mata kayanta na sawa yana kyakyata dariya irin ya gama dasu suyi ta Zama gida daya ba wanda zai so wani,kuma ya goge musu Memory.Tafiyarsa yayi ya barsu nan cike da takaici sai ya koma can kasarsu China bazai kara dawowa ba duniyar biladama har abada ya koma cikin jinsinsa,yan uwansa sai murna sukeyi tare da tayashi jimamin rashin cikar burinsa wato auren Salma.
Alhmdllh Raheel tasa ta kare kuma Salma da Na'im sun huta duk da cewa ya barsu cikin matsala.
Sanda Malam Magaji yace Na'im ya daukowa Salma akwatinta su tafi sai ya bata rai yace shi bazai iya ba,Salma ta dalla masa uwar Harara tare da cewa to sai me ance bani da karfi ne ko hausa baya ji jibarshi ta dauki akwatinta tare da cewa Malam na gode Malam.Na'im da Salma ba wanda ya gane daya tsakaninsu,sai hararar juna sukeyi har suka shiga gidan,Haleematu ta dinga murna ta samu ya mace zasu dinga shawara da hira,nan Dakin dake jikin Na Na'im aka bawa Salma itama,tana bude akwatinta kayantane na gidan Mummy da komai na mace da zata bukata ciki kaya sun kai set 20,itama Salma bata gane cewar kayanta bane ko daya kawai dai taga kaya size nata bata iya tuna komai sai tayi tunanin cewar ko ita ta dakko akwatinta amma baza ta tuno ba.
Wanka tayi ta shirya cikin doguwar Riga baka me kyau sannan ta fito tsakar gida itama Haleematu tana tabarmarta gefe daya tare da Malam yana cin tuwo,Na'im kuwa cewa yayi Bai cin tuwo shine Haleematu ta masa faten doya yake ci shima a saman wata farar kujera plate din yana hannunsa,Salma ta dauko tabarma ta shimfida kusa da Na'im tayi zamanta akace Faten doya ko tuwo tace tuwon dawa miyar kubewa danya idan da man shanu ma Umma a sa min kuji Salma daga zuwa kamar gidansu,Malam da Haleematu dariya sukayi sosai,abinda yasa Salma tasan manshanu sanda taje kauyen dake jikin Na Na'im taga suna cin tuwo suna cewa a sa manshanu shine itama tace a sa mata.amma ko girki basa tunowa na baya da suka sani kafin bacewar Memories nasu.
Salma taci tuwo ta koshi tacewa Malam gaskiya ita bata San gidansu ba ne ta manta ya danyi mata Uzuri ta zauna dasu na wani lokaci kafin Allah ya bayyana mata iyayenta,Malam da Haleematu sukace ba komai ta zauna,Na'im yaja tsaki yace tana kwekweyona ne zata ce tana mantawa iyaye nata gaskiya ta tafi ta bar muna House(wai Salma ta kwaikwayesa zata ce ta manta iyayenta)suna gane yarensu da abinda suke cewa Amma basu gane wasu words din me suke nufi.
Salma ta cuno baki tare da cewa ina ruwanka Malam kayi mana tsakani dashi bani ba shi,tunda nazo yake takalata da fada ya takura min shi ba gidansa ba da ganinsa bako ne yazo shima kayi rayuwarka nayi tawa.
Malam yace kyaleshi zaku saba ne ai,bana son fada Ku zauna lfy ke banda rashin kunya da tsiwa kaima kaja girmanka,Na'im Bai gane Karin maganar ba yace Naja girma nawa na kai shi ina ne? Suka dinga dariya kuwa har Salma,Salma tace bagware hausarma ba aji bature masu Jan kunne,wai wannan Malam a ina yake ne?Malam yace bawan Allah ne kamar inda na kawoki haka shima,ku hada kanku Ku zauna lfy kunji,Na'im yace bata da kunya ne wannan daga zuwa gidan mutane sai ina mari nata kullum ths girl.
Salma dai batace komai ba,washe gari da safe Salma ta saba da asibiti da wuri suke tashi haka ta tashi sakamakon tun tasowarta bata saba da yin Sallah ba shi yasa yanzu ma sai taga dama takeyi idan taga dama ma watarana baza tayi ba ko da Aljanin baya jikinta yanzu bata saba da yi ba wasa take da Sallah,tare suke aikin gidan da Umma tana koya mata abubuwa tunda ta manta na baya,haka Na'im ma Umma ke masa wankin kaya ta goge masa sai dai yasa.
Salma tazo tare sukeyi da Umma har wankin amma da anzo na Na'im sai tace baza ta wanke nasa ba,Malam Magaji da Haleematu sun gano Salma ma kwakwalwa bata ganewa irin Na'im ce sai sukace dalilin da bata Sallah kenan memory ya goge har sallah ta manta da ita,shi kuwa Na'im addini ba abinda ya fasa akwai kokari.
Malam da Haleematu suka zage sosai wajen koyawa Salma Sallah azkhar etc duk ta iya kawai bata yi ne amma dalilin sata tayi kullum ba fashi dole sai tayi ko taki ko taso tun bata saba ba har tazo ta saba da addini sosai,watarana dai tana kinyi akan lokacinta ko ta hada magrib da Isha,la'asar da azahar amma kullum sai tayi bata missing.