← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 80

Sashe 66

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna hutawa suka fito wajen kida gaba daya ba kidan hausa ciki kidan wakokin arna yan kudu ake sawa su Wizkid,Timaya,lilkesh,kiss daniel,Kawayen Aisha ne ciki suke ta bari da kudi suna taka rawar Shaku Shaku da wasu kalolin,Mazan abokan Angwaye suna wajen suma dasu akeyi suna liki,Zainab taje wajen Hunaif yana gefe yana waya tace yaje yace a sa musu na hausa su,Yace dole kuyi mana wannan rawar mu Sha kallo,Zainab ta dinga dariya tace Allah baza mu iya ba mu dai,Sabo da son kai Hunaif yace to ta Larabawa za asawa su Afrah suyi,aka sa musu Wakar Arab ta bellydance duk suka shiga danginsu jar fata suka dinga yi ba ji ba gani,Har Hunaif sai da yayi ta Larabawa,su Na'im suna ta dariya,Irfan Zainura tace yaje yayi shima ta masa liki ta garinsu,ya shiga aka basu fili kidan Arab na tashi amma da zai fara sai ya fara dariya ya fasa,Zainura kuwa tace in baka yi bani waje ta daga hannu sama yanda taga sunayi ba mistake kun San dama ta iya gwada komai na mutum idan yayi sai ta gwada,Zainura ta dinga yi kuwa aka dinga dariya da Ihu harda haukarta ma yi take wai ita balarabiya,ai kuwa Dukkan fararen da su Na'im suka dinga mata liki kamar me ana tafa mata,Na'im yace Salma taje itama ta gwada,Salma ta makale kafada tana dariya ni wlh bazan iya ba,na iya rawa dai amma banda ta Arab,Na'im yace to a koma kidan Nja songs Salma ta shige idan baku manta ba Salma gwana ce,sai da ta bawa kowa mamaki har bangaren su frnds na Aisha,haka su Mummy da Umma da sauran mutane suma sunyi liki,Ita kuma illar Salma idan ta fara rawa to bata san ta tsaya ba,Na'im yaga ana kalle masa abubuwa yace tazo su fita taki yarda,sai ya jawota ta makale,taki fitowa cashewa take abinta,kizo mu fita haka cewar Na'im,ni fa ban gaji ba,daya gaji sunkuyawa yayi sama da ita ya daukota kamar jaririya yayi waje da ita,Taji an canja kida ta kwace hannunta zata koma ciki Na'im yace zan bata miki Salma na gaji haka daga cewa kiyi kadan kina gani Maza sai kalle min abu sukeyi,me yasa bakya min ni na gani? Kace nayi maka ne? To shike nan zaki dinga min amma karki karayi anan.
Hunaif kuwa ba ruwansa cashewa yakeyi kamar ba gobe,Irfan kuwa ko ya shiga baya iyawa,Na'im yace Saura frnds din Zainura sun Zama yan kallo za ayi basu,yace Dj suma ya sa musu wacce suke so,
Aka samo masu shegen kida na Hausa na zamani,nan fa kallo ya koma wajensu suka dinga jijjiga hips a wajen nan suna bada show,kowa tunaninsa kalar na kauye zasuyi kuma kamar wanda sukayi training iri daya sukeyi,ko wanne kida aka sa to akwai rawar da sukeyi kuma duk iri daya sun iya har Zainura,Salma ta kwace zata fada ciki ayi da ita Na'im ya jawo rigarta kamar me Aljanu suka dinga kokawa wai sai shiga, Allah yasa Umma ta gani tazo tace ke baki da hankali ne?mene haka karki sake na ganki ciki duk mazan nan,Salma sai lokacin ta hakura wai ita an takura mata kowa da masu auren suna ta rawa amma ita an tsaneta an hanata,duk ga masu aure nan sai ita za a hana,tayi fushi tare da Zuciya ta bar wajen ma ta koma can bayan wani part building ta Zauna ta fara kuka.
Na'im ya dauka ta hakura ma tafiya tayi kawai zata huta bai San tana can tana kukanta ba,Irfan kuwa Kujera aka ajiye masa a tsakiyar fili ya zauna daram da kudinsa na liki Zainura ta shugo kamar shedaniya haka ta zage ta dinga casa Rawa yanda taga dama,yana mata liki,ana ta cin dariya ana ihu da tafi,ta tafi da Imanin kowa,Idan taga dama har mazaunanta zata juyawa Irfan baya ta murguda Masa Shi kanshi watarana kasa likin yakeyi sabo da dariya kamar ba itace Amaryar ba tayi rashin kunya yanda take so,Manya da yan mata Tare da Samari Zainura ta taka rawar birgewa tasha liki, Irfan ta mikawa Hannu ya Mike kuwa kamar wani abu sai aka ga ya cire hular da ya sa ya sawa Zainura ita ita kuma ta sa masa gogoronta,Na'im Ido ya rumtse sabo da rashin kunyar da su Irfan suke a filin nan yayi yawa,Hunaif kuma ya shigo da Afrah suka fara rawar turawa su biyu da slow music,
Doctor Aliyu shi gentle ne aikinsa liki kawai yake kowa,har Aisha in ta shiga zaije yayi mata liki ya gaji ya fita.

Hunaif yace to duk su Jamila kawayen Zainura su shigo ya shiga tsakiyarsu suka dinga cashewa dashi ana ta liki a nan shi kanshi Na'im yaje ya musu liki sosai,suka ce Irfan ma ya shigo shi tsayawa kawai yayi sukayi sosai suka Sha liki,gaskiya yau sun cashe kamar baza a mutu ba,anyi watsi da kudi,babu kamar Amarya Zainura a wajen nan yanda dama tace ta rantse idan bikinta yazo sai ta ajiye tarihi,ba wanda ya isa ace ta tsaya kawai sai ta cashe ta bar tarihi,aiko yau kowa ya sheda Zainura tana kaunar Irfan din nan nata.

Na'im ya nemi Salma ya rasa,ya kirata a waya taki dagawa ya duba ko ina bai ganta ba,har aka gama kidan wurin 9pm aka watse sai kuma gobe dinner.

Har 10pm ta wuce Salma tana can inda ta zauna a waje bayan Building wai a nan ma zata kwana tayi fushi,duk wanda Na'im ya tambaya sai yace Bai ga Salma ba,shi kuma yunwa yake ji ma so yake tazo ta bashi abinci,ya shiga nemanta,ba ita ba labarinta,hankalinsa yayi matukar tashi ya koma Compound yabi ta inda yaga tabi dazu har bayan Building din yabi wurin garden ya hangota Zaune ta kudundune a Zaune,da sauri ya karasa wajenta yana tambayarta lfy? tace ba komai tayi shuru,taso mu tafi me kikeyi a nan? Salma tace ni bazan je ba anan zan kwana,Me ya faru ne? Salma tace ka fini sani ai tana Hawaye,sai lokacin ya tuna me ya faru ma ya hanata shiga rawa shine tayi fushi,tsugunawa yayi tare da cewa oops na tuna kuma akan wannan kike fushi?ai dole nayi kowa gasu nan sunayi kuma da aurensu amma ni sabo da bani da gata bani da iyaye shine za a nuna min banbanci a hanani yi,to bazan kwana a gidan ba,dariya Abin ya bawa Na'im,Salma gani take kamar wani ne ya hana Danginta su kulata,sai tayi ta zargin cewar dan bata da gata shine ba a damu da ita ba,dama haka dan Adam yake ko mutum talaka ne aana yi masa abu zai ce dan anga mu talakawa ne bamu dashi,idan rashin lfy ne ma haka,idan rashin yan Uwa ne sai ace Allah sarki to bamu da gata,ba Uzuri Allah kyauta,komai ace dan kaza ne zargi kawai da hasashe.

Na'im ya kalleta kawai yasan to Dan Adam musamman ma mace me rauni,sai ya share tare da cewa eyya so Sorry ban san zakiyi fushi ba,bazan kara ba,yana tsugunne ya juya mata baya tare da cewa hau na goyaki mu tafi amma sai dai mu bi ta dayan part din sabo da main akwai mutane,ba kunya ta hau bayan tana mita ita dama bata da yanci har suka karasa part dinsa ba tare da kowa ya gansu ba.
Yunwa Honey baki bani abinci ba tun rana,bata ce komai ba ta Mike ta fita ta kawo masa wanda dama ta dafa masa da yamma,tashi tayi zata bar dakin muryarsa taji yana magana da alama ransa ya baci ki dawo bazan iya bacci ni daya bafa,Salma tace jibi fa za a kawo ni,dariya ma ta bawa Na'im kamar wata Amarya sabo da kuruciya wai sai an kawota,bai ce komai ba yace jeki to sai jibin,ba tunanin komai tace good night ta tafi abinta,kawai murmushi yayi domin kuruciyar Salma har mamaki take bashi.

Bedroom din Amare ta koma itama Salma,Zainab tace kai Jama'a Zainura ta fesa rashin kunya a wajen nan,Zahrau tace kamar ba itace Amaryarba yau Ango yasha kallom kugu,Zainura da fitowarta daga wanka kenan tace ai dama tun a kauye na Rantse da bikina sai na taka na girgije bazanyi kaffara ba ehe.
Aisha tana dariya tace zaki fadawa mutan garinku wlh mijinki Baida hakuri,Salma tace ai Zainura duk ranar da taji dadin Amarci Haukacewa zatayi,Zainura tace tun a first night dole mu murji duniya,suka dinga dariya Zainura zata fada nan gaba,Z ainura kuwa dadi take ji tace kai yau na cashe ban taba Sanin cewar haka nake ba sai yau e..e...e...e ta kara yin girgiza a gaban mirror tana kida da bakinta.
Kiran Irfan ne ya shigo wayarta ta sai da ta kusa tsinkewa wai ita Jan aji,hello! My life ya gajiya? Alhmdllh tana wani kashe murya,me kikeyi yanzu wanka nayi ma yanzu mai nake shafawa,Irfan ya gyara kwanciya tare da cewa mene a jikinki?Zainura ta kara kasa da murya,towel ne dan guntu,Irfan yaji yawunsa ya tsinke ya fara kissima Surar Zainuransa yanda zai more jibi,Allah ya kaimu Sunday Sweety,Zainura tayi shuru kawai tace uhm Ameen.
Chapter 66 · 0% Book details