← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 80

Sashe 10

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi yaja kene Mayya?ya tambayeta,ni ba mayya bace,to kene Mannira?dariya tayi tace sunana Salma,yace no...no yana dacewa ace iyaye naka Mannira suka sa miki ko mayya,kaine Dan Fulani masu shaniya da noanoa?,yes muna da shanu da Nono kana Sha?baki ya tabe Kazami.. kazami kune Bana so na Shaniya sai na kwali Holandia understand?ni sai na dura ma na Saniyata ka shanye,hannu ya fara karkadawa wai no...no bazan Sha bama na kulle bakina harda tsuke dan bakinsa,Dariya tayi sosai,ya tsaya yana kallonta, Raheel me yake damunka ne? Kana ce mini Raheel ba shine ba,Na'im ne ni,aiki..aikina inayi kazo kana damuna pls back to ur Room banma san Why na kiraka nan ba kana damuna cewar Na'im.
Kida ya kunna na turanci a wayarsa nan take Salma ta fara bin wakar kamar ita ta rera har kada kai takeyi.

Affa da Ummitu suna can takaicin rashin ganin Salma ya ishesu ga talauci,can Affa ya kokawa yan uwansa matsalar da suke ciki tare da abinda Salma takeyi,nan take yan uwansa suka hadu suka zugashi, shi yasa watarana ma shawara da wasu matsala ce, cewar Salma idan ta dawo ya koreta kawai yayi mata korar kare Domin zata kasheshi tun kwanan sa Bai kare ba,ya dawo ya Sanarwa Ummitu,itama ta gano zancensu gaskiya ne tace Malam wannan gaskiya ne ka duba farar kafa irin ta yarinyar nan tunda aka bamu ita kullum talaucewa mukeyi bamu taba ci gaba ba,munfi kowa talauci a garin nan namu,yanzu akan nema mata magani duk abinda muka mallaka ya kare,saniya ko daya babu,kayan dakina,gonakinmu duk sun kare tas,a abinci har makwafta taimakon mu sukeyi kullum talauci yaki ci yaki cinyewa sai yawan Shan garin kwaki,duk ya tsotse mana jini da ruwa,Uban Salma mahaifi ya zalunce mu dama yasan yarsa haka take Ashe ya lika mana ya mutu ya barmu da wahala..shi yasa yan uwansa suka ki riketa.
Affa ya nunfasa yace yanzu na tsani yarinyar nan wlh Bana kauna na bude Ido na ganta a gidana,dama kaddara ce tasa na dauki jaraba,tunanina munyi yar kirki Ashe jaraba muka Raina da hannunmu,
Bamu karu da ita ko tsinke ba sai raguwa,Allah ya gani munyi iya yinmu munyi na Allah munyi na Annabi munyi na Binta dan haka taje can tayi yawon duniyarta,wannan rainin hankali ne yarinya gantalalliya cewar Ummitu.

Affa yace ko ta dawo idan kika barta ta shigo min gida to Allah ya isa ban yafe miki ba,na gaji da talauci,Ummitu tace oh Ashe gaskiyar bahaushe da yace tsintacciyar mage bata mage mun karbi Bala'i da hannunmu,Affa ya kara da ni dama Bana kaunar rike dan wani,dan wani ko jaraba Allah bai bamu ba mu hakura,dama dan kar nace ban so ne kice wani abu shi yasa nayi miki kara naga kina sonta.

Ummitu ta tafa hannu tare da cewa yo aini ta Dade da sire min dama kwadayin yara yasa na karba jaraba ai zamu yarda kwallon mangwaro mu huta da kuda,nan take shedan ya kara dasawa Affa da Ummitu kiyayyar Salma a zukatansu suka ji ba wacce suka tsana a duniya sama da Salma,suna ganin cutarsu ma takeyi tun farko.

Dan Adam kenan bashi da tabbas,yanzu da Salma bata samu matsala ba ko Allah yasa suna daukota kudi suka samu ta hanyarta ko wani abu da yanzu basu da sama Salma, baza suce komai ba, amma an musu kyautar ya guda tsakani da Allah sabo da kaddara ta sameta ta shafesu suna furta kalamai munana,dan Adam me manta alkhairi,inama Tall Man Baban Salma Bai rasu ba yaga cin Amana,butulci da manta alkhairi wajen Affa da Ummitu,farko sunyi bajinta amma at the end sun kasa jure kaddara wanda ita kanta ba ita ta dorawa kanta ba,
Yanzu da yarsu ce ta cikinsu baza suce komai ba ta Zama dolensu,dole su hakura su karbi komai,kuma baza su taba tsanarta ba,amma wannan sabo da basu San ciwonta ba basu San zafinta ba sun zobe ladansu wajen Allah,dama haka dan Adam yake bashi da tabbas kuma ba a iya masa musamman zamanin da muke ciki,daga naka sai naka,naka iya naka,kowa kansa ya sani baza ayiwa wani Uzuri ba.

Tun daga wannan rana Affa da Ummitu suka shiga bata Salma a cikin wannan kauyen,duk inda suka shiga sai sun zagi Salma cewar ko Sallah bata yi ga bin maza,bayan sun tabbatar aljanu gareta amma saboda kar aga laifinsu kar a zagesu idan sun kori Salma sai suka fadawa duniya cewar cikin shegenta yafi uku ma,sune suke rufa mata asiri suna kaita can Borno wajen danginta tana haihuwa sai ta dawo wasu kuma aka zubar.
Mutane Fulani na daji da jahilci sun yarda sabo da duk wasu shedu sun samu sabo da Salma duk wani sign na cikakkiyar yar bariki Aljani Raheel yasa ya fito fili an gani wanda a zahiri ba haka abin yake ba,kuma su Affa sun San gaskiyar magana.

Nan garin ya dauka duk majalisa zagin Salma akeyi haka mata ma ana tsine mata,mutanenmu hausawa basa yiwa mutum addua ko aji lafazi da kyakyawan zato idan ya aikata mugun abu kawai sai dai a fara tsinewa mutane ana aibatasu ana zaginsu,ba Uzuri kuma mutum baya hango nasa laifin sai na wani,abin haushi ma yawanci zargine kawai ba tabbas a kan abun.

Affa da Ummitu Rashin Imaninsu bai tsaya iya nan ba,Tall Man ya rasu hankali kwance tunaninsa ya tserar da yarsa daga wahalar duniya zata samu rayuwa me kyau ashe an bar baya da Kura ba a sani ba,shi yasa mutum bashi da wani Plan sai abinda Allah yayi.
Afda suka ce ta inda aka hau ta nan ake sauka muje Borno kawai mu wanke kanmu idan ta dawo idan zasu iya su rike yarsu can,haka sukaje Har Borno suka shiryawa dangin Salma karya da gaskiya su Malam Shehu da Malam Musa Baban Hashim harda Kuka ta bata musu suna da zuriya,suma dama kadan suke jira,zamanin haka yazo idan ka rasa iyaye to kafin a samu me rikeka tsakani da Allah ya tsaya maka sai an tona haka zakayi ta garari ana zaluntarka.
Malam Musa ya kalli Affa yace Allah ya saka muku da alkhairi,Allah ya biyaku da Aljanna,ko a gun Allah kun fita tas,Mu mun San rufawa wannan yarinya asiri kukayi amma ba komai zata zo ta samemu ace Zuriyarmu da cikin shege har yafi uku,nan muka tashi da safe sabo da ta Kware da bariki tace ya bace cikin daga jikinta makaryaciya,Ummitu tace ai zuwa tayi aka Markade jaririn yanzu ciki ko wata tara ne ana iya markadeshi a cire ai anci gaba,makaryaciya ce kar Ku yarda da zancenta,Shehu kanin Baban Salma yace to ai tayi kai,zata zo ne dama ubanta shine ya hada tunda kuwa haka take ai zumunci ba dole ba dole bane sai ka ajiye shi ina zaka iya rike irin wannan.
Ku duba tunda ta tafi ko leko mu batayi ba, nan Kuwa Shehu Murna yakeyi sabo da ya cinyewa Salma Gadonta kaf gonaki,fili, da wasu kadarori da Babanta Yayansa ya mutu ya bari.

haka bangaren mahaifiyar Salma su indai ba wani abu zaka basu ba to baka da mutunci a idonsu,komai a basu,idan kaga ana washe maka baki to sun San zaka basu wani abu,ita kanta Khairat Babar Salma ta bar sarkar Gold da rakuma biyar,tare da gona amma tuni suka je Nijar suka siyar dasu da komai suka handame kudin kaf tunaninsu sunci banza Salma ai yarinyace,duniya kenan Dangi a gyara Hali dan uwanka na jini ya mutu ya bar yara amma a rasa me rikesu,a cinye musu gado kuma still ana zaluntarsu.

Affa harda Hawayen karya,haka kowa ya tashi da tsanar Salma me tsanani dangi da kuma marikanta su Ummitu haka suka dawo Rigarsu Ransu fari Kal sun gama fita daga zagin dangin Salma dana mutanen gari.

Washe gari suna tashi da Safe Affa ya daga kasan pillow nasa yaga kudi sababbi yan Dubu Dubu har Naira Milliyan daya,daga sama yaji murya na masa magana cikin nutsuwa ance kudin shanunka ka siyo shanu Kaci gaba da kiwo,haka ma kuma arzikinka zai bunkasa tunda ka rabu da me kashin tsiya.
Affa ya rasa inda yaji maganar ji yayi kamar a kunne aka rada masa,amma yace yanda yaji haka zaiyi,nan ya tafi kasuwa sai ga Affa da shanu har bakwai maza da mata,ya siya musu kayan abinci da yawa,yayi musu dinkuna sababbi ya samu ya siyi gona har biyu na noma,daga nan yaci gaba da kiwonsa cikin nishadi da jin dadi arziki ya Karu,tun daga wannan rana Affa hanyoyin samu suke bude masa,mutane sai murna ake tayashi cewar gwara da ya rabu da Salma tsiya.
Readers tunaninku Affa da Ummitu Aljanu suka sasu aikata hakan rabuwa da Salma da zaginta?ba ruwan Aljanu a nan da gaske sukayi wannan abun,hali ne na Dan Adam dama yana faruwa.
Dama Raheel kuma yace bazai barsu suyi arzikin da zasu nemowa Salma magani ba,gashi sun ce baza su bar ma Salma ta shigo musu gida ba shi yasa ya basu kudin da ya lashe musu ya biya su arzikinsu ya dawo,sai suke ganin dama Salma ce me kashin talauci ita ta jawo musu.

Allah sarki Salma tana Hospital na Na'im hankalinta yanzu kuma yayi gida babu wanda take tunani sama da Ummitun ta da Affa tare da yan Uwanta na borno,yanzu kam tace ta gaji da ganin Raheel dole yasa a kaita kauyensu ta gano lafiyar su Ummitu domin bata da Kamarsu a duniya, su Mummy sun dawo daga ziyarar yan Uwa a Kebbi kullum sai sunzo duba Salma da kayan dubiya iri iri.
Irfan yana yawan zuwa susha Hira da Salma yana jin shirmenta.
Chapter 10 · 0% Book details