← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 80

Sashe 42

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainura ta dan bigi Salma ta kalleta tare da yi mata signa da Ido tana kallon kayan abincin wai su kwashe mana su wanke,Salma a hankali tace akwai masu yi,Zainura kowa naji tace mun shigesu haka zamuyi ta yini muna kwana ba motsa jini ba aiki daga wanka sai ci? Ni wlh bazan iya ba na saba da aiki na zauna haka ai sai jikina ya fara ciwo ni dai zan dinga taya yan aiki muna yi tare dasu bazan iya zaman kashe wando ba,Mummy tace ba matsala ai Salma ma tana aiki a gidan nan ta nuna Aisha kinga dai wacce ko cokali bata dauka,Zainura ta kalli Aisha tare da rike baki tace keeeeeeee kiyiwa kanki fada kiyiwa kanki Kiyamullaini ki koyi abin duniya haka za a miki aure Me gida yaji baki iya girki ba wlh koroki zaiyi,Mu yanzu Mummy a kauye baki iya tuwo ba ai kin shiga uku da gori,bakiga wata kawarmu ba Marsiyya abin mamaki bata iya miyar taushe ba ranar Juma'a batayin tuwon shinkafa miyar taushe Juma'a guda aiko mijinta Lawwali ya kai kararta gida aka zaneta aka ce muje mu koya mata,to kema Aisha idan baki iya ba Allah Mummy kisa na koya mata kuma wlh sai na dinga dukanta idan ina koya mata,Dada tayi dariya tace ni dama ke aka barmin muka tafi gidana mukayi zamanmu tare a saki a makaranta,Zainura tace keeeeeeee iya rufa ni ki sayani a nan ma na dan rabe kafin na tafi garinmu,Dada tace da gaske nake fa,Mummy tace Hajiya ki Bari ta gama aikinta da nace idan iyayenta sun baki shike nan ai,Dada tace Allah kaimu.

Malam tuni sun koma wajen da aka saukesu suna hira Dada tana wajensu da Mummy,Zainura tana zaune a Palo ita da Salma sai ga Irfan Ya shigo ya Sha wanka ya kalli Salma yace fatan dai yanzu ana Sallah matar Yaya Na'im, Salma tace kai ka sani an fada ma yanzu da ne? Irfan yace ina Raheel wai?Salma tace ni ban san wani Raheel ba wlh waye? Ganin fa Aljanine kuma idan mutum yana Aljanu idan ya warke baya Sanin me yayi ma sai ya share zancen,Zainura tana zaune sai ga Hunaif ma sun fito da Aisha suna ta faman dariya suna kallon wata katuwar waya,Hunaif Yace Bro muyi game mana mun dade ba muyi ba,Aisha tace zanyi nima,Zainura ta watsa mata harara tare da dauke kai can kasa tace uwar iyayi ba a iya girki ba,Aisha taji ta,Salma ma harda dariya,Irfan suka fara game sosai Zainura tana kallon abin mamaki kuma tana ganewa kafin kace me ta gane yanda ake game din to akwai basira,Aisha bata wani Iya ba cinyeta suke tayi,Sai muryar Zainura suka ji tace zan iya nima a bani abun muyi da wani,Suka sheke mata da dariya,Irfan yace ke ko Aisha bata iya ba sabo da ke ba brain zaki ce ayi dake,Hunaif yace to ko Handle zata iya rikewa ne? Muryar Na'im suka ji yace hey guys ba a haka fa wannan shirme ne idan zakuyi da ita kuyi idan baza ku bata tayi ba mene na mata dariya.

Irfan yafi Saukin kai yace to ke taso muyi na dura miki kaya,kuma baki isa kin daina ba sai an gama komai cin da za ayi miki,Zainura tana dariya tace to,Hunaif ya bata Handle dinsa ita da Irfan,Zainura Uwar basira sai ga Irfan Ya kasa cinta,sai wahala yake Sha,tana ta dariya bata ci ba shima Bai ci ba,suna ta yi,Hunaif ya dinga mamaki da sauran mutanen,Da kyar Irfan yaci daya da zero suna tayi ta farke dayar daya da daya,har game time ya kare 1-1 suka tashi,kuma a haka Irfan yafi kowa iya game,Hunaif yace sai ya cinyeta suka farayi da Zainura ta masa 2-1,Aisha ta karba ta mata 5-3, suna gamawa ta jefar da Handle irin shegiyar nan tare da cewa Ku kiyaye hada kwanyata da taku haka Allah ya yini ni,dukkanku yanzu zan iya yin kalolin muryoyinku tafiyarku da komai naku,ni ba a ja dani ko a kauye,Na'im ya zauna gefen Salma da tayi shuru tana mamakin Zainura da basira ko ita duk zamanta gidan bata iya ko gwada game din ba.

Na'im taji ya kwanta mata a jiki tare da cewa muje Bedroom Ki tayani hira yanzu naga Alama gudu na kikeyi,Salma tace uhm ni bazanje dakinka ba,Zainura tace ke yar Iska wannan karya kike a gabanmu wlh kuke tsotsar juna bakwa kunyar uban kowa har kinfi me kyau maita,wanne iskanci ne bakuyi ba sai yanzu zaki dinga karya,to wlh ba abinda me kyau baiyi dake ba domin mu shaida ne,Irfan ya dinga dariya kamar me yace yawwa Zainura kike ko?gwara ki dinga tona musu asiri wlh,Hunaif ya kalli Zainura yace ke mene tsotse juna Zainura tace kaji yaro kato da kai baka sani ba duk iskancin da samari keyi yanzu,yo kai daga ganinka Alla ai ka dan yiwa mata wani abu,yanzu Ko a kauyenmu su Ubale,Ashiru,Habu,Audu me kifi,Dan Isya me Rake sun San Iskanci bare kai me Jan kunne,Irfan yana dariya ya Kalli Hunaif yace kaga ka jawowa kanka hhhh kuma gaskiya ta fada mene baka yi ba dan Iskanci zaka tambayeta.

Zainura tace wlh duk yaran gidan nan daga Me kyau sai kai Irfan kunfi kowa kirki amma wannan mai fuska kamar tana Mura bata da kirki,shi kuma Hunaif ya fiye iyayi yanyanyanyan ta gwada maganarsa nan ma suna ta dariya,Na'im sai gani akayi bashi ba Salma a palon,Irfan yace Ina Salma da Bro?Zainura ta tabe baki tace wannan ka daina zancensu da kunga abinda suke a kauye Wlh Allah baza kuyi magana ba yan Iska ne na gaske.Irfan yace ke kinga Illarki baki waye ba da na kaiki yawo tunda kina da hira da abin dariya,Zainura ta rike kugu tace koya min ka gani idan ban iya ba yau din nan zan rikide na koma yar birni,Hunaif yace Aisha ce zata koya miki,Salma baza ta koya miki ba wannan mijin nata bazai barta ta samu time naki ba,Aisha tace kuna dai ji Mummy tace ko zaginta nayi ta rama har duka,Zainura tace kuma kin San ni tantiriyar yar duniyace wlh kina min sai na miki ko Mummy batace ba,ke Allah na tuba da dasu Zainab aka taho ai da tuni kina asibiti Alquran ki godewa Allah ni aka kawo nan, Ke fa Aisha na fuskanci gani kike kinfi sarauniyar Ingila wayewa ko? Ke gani kike ba wacce ta kaiki haduwa ko? Aisha tayi fari tace sosai ma,Zainura ta fara dariya tare da cewa Yasin kinji na rantse tun a Tafa da muka tsaya cin abinci naga wacce ta dameki ta shanye,ke tun a Mararrabar Jos tasha naga wacce ta fiki ki daina bata lokacinki haka Salma nan ta mitsitsikeki a komai,tausayi kike bani yasin,ni kaina duk sanda na Zama yar gayu sai na wuceki.
Irfan da Mummy data shugo suka dinga yiwa Aisha dariya tana Jin haushin Zainura.

Da dare ma da Zainura ta shiga zata kwanta Aisha sai bargo ta jefo mata wai ta kwana a kasa tunda bata da mutunci,Zainura ta shareta ta shimfida abinta ta kwanta ta shaki baccinta.
Bangaren Na'im da Salma kuwa tunda ya janyeta Bedroom dinsa Kuka takeyi wai ta tuna Affa da Ummitu sai ta tafi wajensu,ba yanda Na'im baiyi da ita ba taki yarda,shi dan Iskancinsa ma yake so yayi ko kadan ne amma Salma taki yarda sai wani kukan banza takeyi kan su Ummitu da Yan uwan Babanta,shi yasa ta kasa sakin jiki a gidan tunda suka zo,da kyar tayi bacci ya rungumeta shima yayi baccin,washe gari Zainura ta riga kowa tashi tayi brush da wanka ta shirya ta tayi sallah ta fito Palo da sanyin safiya ko haske gari baiyi ba ta zauna tare da sa wata cikin yan aiki kunna mata TV, taga yan aiki suna ta gyare gyare wasu suna kitchen ana shirya girki,ta shige ciki ta karbi mopper akayi aiki da ita aka gama,ta shige kitchen aka karasa girki da ita tana kallon abincin yan gayu,Irfan ya shigo daga Gym ya shiga kitchen dakko fresh milk da ruwa ya hango Zainura an tsege daurin ture kaga tsiya tana yanka Albasa a cikin kwai.
Shi tana birgeshi yanda take wayayyiya bata duhun kai na yan kauye bata tsoron kowa harkarta takeyi kamar yar gidan,Muryarsa taji yace ke da safe har kin fito? Zainura ta washe baki tare da rufe idonta wai kunya ta ganshi da dan wando short da yar riga,tace Laaaa kai ko kunya haka kuke yawo tumbir billahillazi Rahamanu ni bazan kalleka haka ba,Idonta a rufe tace ina kwana,yace lfy lau yana dariya su Kansu yan aikin dariya sukewa Zainura wai bata waye ba,tace mu dai ka fita sai kace Gambo dan Fulani a kauyenmu haka yake yawo aiko kowa dan iska ake ce masa Yasin,Tabe baki Irfan yayi tare da daukan abinda yazo dauka yayi waje yana ganin kauyancin Zainura yayi yawa.

Na'im da Salma sun tashi Na'im yana zuba murmushi yace wai dan Allah baza ki fada min ba nayi Iskanci ko bamuyi ba?Salma tana dariya tace nifa ban gane ba bazan iya ganewa ba,tana kwance ya hau samanta tare da rike hannayen Salma wai sai ya duba wlh ya gani,Salma tana dariya suna ta kokawa suna dariya,ina wayarka ta kauye da faifan CD ka sa mana mu gani mana cewar Salma,ki bari sai Next weekend sai mu saka a Palo gaba daya a kalla me akayi a bikin,Salma tace Allah ya kaimu.

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉

121-125 126-130

Official

By
AsmaBaffa

ASMABAFFA FANS CLUB wannan page naku ne Ku kadai,love u all.
Chapter 42 · 0% Book details