← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 80

Sashe 25

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana Uku da gama shagalin kauyen,Salma yanzu ta iya girkin gargajiya da yawa komai ta iya,haka Umma tana koya mata dabarun mata idan sunyi aure,dole take sata tana amfani da ruwan zafi da gayyen magariya tana tsarki dasu,har wasu tsumin tana dan bata irin na yan mata Sabo da lafiyarta ta zauna daram tare da maganin infection na ciwon Sanyi da dawwamar da Ni'ima a jikin mace.
Na'im yana zaune yana duba wani littafin musulunci ya rufe fuskarsa da littafin Amma a zahiri ba karatu yake ba idonsa ya leko ta yar kafar littafin yana ta faman kallon Salma,ji yake kamar ma ya jawota jikinsa ya maidata cikinsa su zauna har abada,
Salma tana wankin kayansu da nata da nasa tana kallon abinda yakeyi idonsa har ya canja kala Sabo da jarabar Na'im, Salma ta kalleshi suka hada ido ta saki murmushi me tsada da birgewa,dimple nata ya loba,Umma na kallonsu ta tashi cike da kunya ta fada kitchen tana aikin abincinta,Salma ta dago masa hannu da kumfa a hannunta,dariya ya mata tare da yafito ta wai tazo,sanye take da English wears riga da skert sun mata kyau,cikin lafiyarta ta jan hankali da birge me kallo ta karaso wajensa ta tsuguna megidana gani,Na'im yaji wani sanyi,ya kalleta tare da mika mata tafin hannunsa yace mu danyi kadan kafin Malam ko Umma su gani,Salma tace me fa? Yace dan sabon mu danyi kadan Malam yace Sabo ne taba mace ba muharramarka ba ko?Salma tace eh,why not yau na taba kadan mu danyi kadan? Salma tace gaskiya hakane mu me mukeyi ma na Sabo ai mu salihai ne,to mutane da dama suna ganin basa aikata Sabo ko me sukeyi ai kadan ne,baka sani ba da kadan din sai yafi me yin babba a wajen Allah,Allah Sa mu dace.
Salma ta mika masa Hannun ta me santsi da laushi shima Na'im haka ya hade hannun waje daya gam yana murzawa Salma tana lumshe ido,yana kare mata kallo kamar me,da kyar ta kalleshi a kunyace yace me kike ji?da dadi?Salma ta rumtse idon kunya tace uhm...wani zir..zir...Kamar tafiyar tsutsa a jinina,A hankali Na'im yace nima haka,Malam ya mana auren ko?,Salma ta daga kai wai ae idan ya dawo ka fada masa tunda idan anyi aure ai zamu iya rike hannu da rungumewa ma Na'im yace hakane bari ya dawo je ki karasa aikin ya sake mata hannu ta koma wajen aikinta shi kuma yaci gaba da kallon abarsa,Salma tace au munyi Sabo to muyi istinghifari,sai ko kowannensu ya fara astaghafirillah wa atubu ilaih a hankali suna ta mus..mus..da baki.

Da dare Na'im yaje har dakin Malam suna tare da Umma ya sanar masa cewar ayi musu aure shi da Salma,Malam yace nafika son na hada wannan auren Amma ban san ko Salma ta taba aure ba taya zan hadaku azo a shiga matsala,Salma tana labe a jikin kofar harda goge hawaye anki yarda ayi musu auren,ta leka ta jikin labile tare da cewa Malam ni ban taba aure ba fa,Malam yace taya kika sani tunda bakwa tuna baya?Salma tace koma na taba auren ni wlh ko memory na ya dawo ni bana son wancan mijin nawa na farko wannan nake so Muhammad dashi zan zauna.
Malam yayi dariyar Manya sannan yace to ni dai Bazan daura ba sai Kwakwalwarku ta dawo dai dai.

Na'im kamar zaiyi kuka ya mike ya bar dakin,yana fitowa Salma ta tareshi harda janshi can wajen zauren kofar gida tace yanzu dai kayi hakuri tukunna muga abinda Allah zaiyi,ka daina fushi kar kasa damuwa ko ina da aure dole dai kai zan aura in dai muna raye,mene abin damuwa kuma? Na'im yayi shuru yana jin yanda take kwantar masa da hankali ba shiri ya jawota jikinsa cikin duhu ya rungumeta kam suna jin kamshin juna,bakinsa ya saka cikin nata suka fara kiss so deep Salma ta kara kankameshi a jikinta,sai kuwa suka ji motsin Malam zai fito daga daki zai je toilet,da sauri a tsorace suka saki juna Salma tayi waje kofar gida tunda 8pm na dare ba a dade da yin Sallar Isha ba,Na'im kuma yayi cikin gidan suka ci karo da Malam,yace ina kaje kuma Muhammad?yace wani...wani...uhm.....wani na duba ko zan ganshi akwai abinda yace zai fada min,Malam yace anya kuwa kana da gaskiya Muhd? Murmushin rashin gaskiya yayi yana sosa kai yace Ba komai fa,Ina Salma? Malam ya tambaya amma Na'im yace tana dakinta tace bacci zatayi yanzu.

Malam yace to to madalla ya shige bayi,Da Sauri Na'im ya leka cikin kasa da Murya yace shigo yana toilet, Salma ta shigo da gudu ta fada bedroom dinta tana dariya ta haye Gadonta ta fara baccin karya,Malam na fitowa Na'im yace Malam zo kaganta har tayi bacci ma Ashe,kuji rainin hankalin Na'im,Malam yace ai na yarda daku kyaleta Allah tashe mu lfy ya shige dakinsa.
Washe gari kuwa Umma ta tafi cikin birnin Katsina wajen kanwarta,Malam yana gona,Salma da Na'im kadai ne a gidan suna aikinsu tare kamar yanda sukeyi komai tare,Na'im ya kalli kirjin Salma yace ina son wannan abu naki,me?Salma ta tambaya,hannu ya kai saman boobs dinta da niyyar nuna mata,ta bige hannunsa tare da harararsa da wasa tace kai shiii dodo ne shishi ne,ba a tabawa,Na'im ya tintsire da dariya yace ni yaro ne zaki ce min wai dodo ne,Salma ma dariya tayi tace to kamashi dodo, indai wannan zai kamani to naji dadi cewar Na'im,Iskanci ne fa Salma ta furta,ashe Na'im ya haddace Kalmar zai fadawa Malam gaskiya watarana yana son Iskanci ayi masa aure.

Salma ce ta fara magana cike da nutsuwa serious muyi Sauri mu tuno baya ayi mana aure mu huta kaga idan bamu tuna ba Malam bazai mana auren ba,kullum ni ina kokarin tunawa da dare Amma har yau na kasa tunawa wlh,Cewar Na'im
Wasa wasa sai ga Salma da Na'im sun kwashe wajen wata tara a gidan Malam Magaji basu tuna komai ba.

Ranar Juma'a da dare Salma ta kara zuga Na'im ya koma ya fadawa Malam ayi musu aure,ta kara labewa a jikin labile tana ji,Na'im kalar tausayi yayi zaiyi kuka yace pls Malam ayi muna auren nan mana,Umma tace nima ina bayanku kawai ayi musu wlh nan gaba in sun tuna idan da matsala sai a warware,Malam yace sam basu da hankali bazai daura ba shi dai,kuma Bada yawunsa ba,Na'im yayi tunani ya samo reason dinsa budar bakinsa yace Malam ni dai ina son Iskanci tunaninsa sunan Breast ne hakan wai yana so,Malam ya hangame baki tare da ware hannu ya cillowa Na'im zagin manya dakuwa,ya kara masa ambola yace gidanku Muhd baka da hankali,Malam ya zauna yayi iya kokarinsa na ya fahimtar da Na'im me kalmar Iskanci ke nufi a Hausa Amma sai Na'im yace ai shi din yake so iskancin dai shi yake so,Umma ma tayi bayani kamar bakinta zai ciwo Amma Na'im yace ni dai ina so na zama dan iska tunda shi nake so,Malam sunga dai bazai gane ba kawai sai ma kunya da yake basu Suka ce ya tashi ya tafi,Kafin ya tafi ma saida ya kalli Malam yace ina son Iskancin Salma ni dai,Malam yace to dan ubanka wlh ka sake ka taba ta sai kaci gidanku Allah zai kona ka.shi dai Na'im yayi ficewarsa abinsa.

Malam yace naga ta kaina idan yaron nan yayiwa yarinyar wani abu,ni ya zanyi dasu yanzu idan tana da auren wani fa,kuma aure ba sanin iyayensu wlh Bazan iya ba.
Umma taji haushin Malam tace shike nan wlh alhaki a kanka su fa yanzu kwakwalwarsu a juye take komai zasu iya aikatawa bana son a samu matsala Malam mu zo muna danasani dan Allah ka daura musu auren nan,ni wlh ga raguna guda biyar a gidan Kanwata zan siyar na Bada sadakin,Malam yace ni ance miki bani da kudin ne?ko kyashi nake? Ranar dai sai da sukayi fada Da Umma da Malam tace sai an daura aure Malam yace a'a.

Na'im kuwa yana fitowa idonsa cike da kwalla saura kadan ta zubo shi kadai yasan me yake ji na Sha'awa kuma Salma kadai yake jin hakan a jikinsa.
Salma tana rakube a Bango taji ba nasara yau ma sai sharce Hawaye take ita dai Son Na'im kasheta zaiyi ma ta sani.
Na'im ya karasa kusa da ita yace nasan Solution ki bari sai gobe dole Malam yayi mana auren nan,7:30muke shigowa daga Sallar Isha to gobe kawai ki tsaya a zaure Bazan je masallaci ba a gida zanyi Sallah,Salma ta mike cike da kuri irin shegiyar nan an samo mafita tace za a gani ne wlh sai Malam ya san mune yan zamani mu muka san Zamani, we no dey carry last tayi kwafa. har kofar Bedroom nata Na'im ya rakata tare da riko hannunta yana wasa da yatsunta Salma jiki ya dauki Harama da niyya fa anyi shuru tayi lakato har ya sata a kirjinsa tare da rungumeta kamar suna Aljanna haka suka ji,da kyar ya saketa saida ta tuna masa da Umma ko Malam sannan ya mata kiss a goshi ta shige daki tare da yin juyi ta fada saman Bed dinta na jin dadi,Na'im kuwa yana haurawa saman Bed sai pillow ya jawo tare da rungumewa kam kamar shine Salma yana ta faman murmushi tare da Tafiya tunani Amma baya tuna komai sai rayuwarsa gidan Malam Magaji,haka ma Salma abin yake.

Sharhi fans

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉

71-75

Official

By
AsmaBaffa

Khadija A Hamza,Salisu Aisha,Fatima Abdullah,Naja'atu Aleeyou,Queen kk,Mom twins,Hadiza Hussaini and Agas wannan page naku ne Ku kadai Masoya.

Mrs.M.D.Argungun Ina godiya ina posting zanga comment naki tnx once again.
Chapter 25 · 0% Book details