← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yan matan naka duk jagwal dasu ina mata anan,fuska kamar Aljanu sura kamar an daurawa Sanda zani,Irfan yana kallon yanda Zainura take zaro zance yana mamaki ba a kureta a magana,yace naji jeki,har zata fita, girman turai ba kunya yace ke Virgin ce? Zainura tana ji ashe tasan Kalmar ta zaro Ido waje tare da cewa kaifa? Yace ni ba shi bane tace shi yasa Ashe ranar lahira akwai tsomen lipton a wuta,hhh wlh sai an maka tsomen lipton kaga dai yanda ake sa lipton a cikin ruwan Zafi a cire ko?tace to ko zaka shiga Aljanna sai an ma haka an wanke ma najasa tas hhhhhh Irfan yace ke wlh fitar min a daki kina mun mugun fata,Zainura tace za a gani ai tunda naga Alama gidan nan ba na gari a ciki sai me kyau shima naji tarihinsa ai.

Tana fitowa taga Aisha anci wanka za a fita Zainura tace uhm Aisha ba kudi ba gadara,ke baki da kudin kanki sai gadara,komai sai dai ayi miki amma gani kike kinfi Dan Gote kudi,Aisha ta kalli Zainura tace ki shiga hankalinki tam,Zainura tace da cikin hankalinki nake? Kina fita dai zaki ga wacce tafiki kyau wlh,ni tun a Tafa naga wacce ta fiki tana nan cikin yan tuwo tuwo na tasha farkon layi.
A wai ke fa nan ji kike da kanki ko?matar da ko saurayi baki dashi ban taba ganin anzo wajenki zance ba,wlh idan muka gaji sai na zuga Mummy ta hadaki da Muhammadu me gadi,ko Ilu me goge windows,Mummy tana jinsu a gefe suna ta cacar baki da Aisha da Zainura wannan ta fada wannan ta fada,Zainura tace Insha'allah sai an cire miki tallafi a gidan nan,kuma sai nayiwa Ilu albishir,Aisha tace kanki ake ji dakikiyar banza dadin abin dai kayana na baki kwance,Zainura tace kuma idan nasa nafi wacce ta bani kayan kyau a ciki ba,domin ni fam nake cika su wata kuwa sanda take dawowa a ciki basa mata kyau Shi yasa ta bawa me kyan diri su tace kadan suka yi mata.

Aisha taji haushi tace Mummy wlh kiyi mana tsakani da ita bani ba ita ta daina min magana wlh zan zaneta fuuu tayi waje,Mummy tace Zainura kyale masifaffiya,Zainura kuwa an Kware da kisisina tace Mummy ita wai bata San wasa ba daga wasa sai ta maidashi fada ina so mu dinga zumunci amma ita sai fada,Mummy tace ai ita haka take daban take cikin yarana sun fita wayewa ai yanzu ne ma Allah ya shirya min Aisha amma da Ai abin ba kyau.

Zainura tace ai ko ni bazan daina kulata ba ana zaman tare zaman mutunci dole na dinga kulata ina mata wasa har ta hakura mu shirya,Mummy harda jin son Zainura a ranta ita kuwa Zainura so take ta dinga cusawa Aisha takaici shi yasa tace sai sunyi zumunci dole hhh

6:30pm Na'im ya shigo a gajiye Salma tana part dinsa tana jiransa taci uban wanka tana ta kumbura kamar zata fashe,Da Sallama ya shigo ta Mike tsaye ya nuna shi Sam bai San tana fushi ba,ya rungumeta tare da dagata sama ya direta saman Sofa yana dariya tare da cewa kinyi kyau Wifey,wa ya taba min ke naga kamar fushi kike,fada min shi nayi maganinsa,Salma tace kaine,ya zaro Ido yace da me?kaki tafiya dani,idan naje dake wa zai gyara min part dina? Wa zai min abinci ko yan aiki kike so suyi min? Salma tace to ai ni nayi ma yau Zainura ce tace haka nake ma a kauye wai naci gaba,Yau dai sai mun kalli CD da wayarmu da album na kauye muga me akayi ciki.

Da kanta ta shirya Na'im yau da kyar tana kunya ta sa masa kaya yaci abinci ya dauko wayar Kauye Cd plate da Album,ya kira kowa na gidan suka taru a Palo ya kuna Cd yasa plate kowa ya nutsu za a fara kallon shagalin biki.

Salma da Na'im aka fara nuna hotonsu tare da adduar aure wani take na Larabawa yana tashi,Zainura tana kusa da Irfan,Mummy da Hunaif ga Aisha a gefe.
Kauyen su Zainura ya bayyana,sai aka nuno wajen Daurin aure,motoci guda 8,ga Malam,su Me gari,Zainura tana laaaaaaaa wlh ga Babana,Baffa gashi ya wuce yeeee Irfan yace yana ina ta nuna musu shi kamar an shigarta Aljanna,daya bayan daya take ga Baban Zainab,yayan Jamila,mijin wance haka take ta yi kowa sai da ta fadi,aka dawo sai ga Ango Na'im cikin shadda Ruwan toka yasha kyau,da frnds nasa duk inda yayi tare da Abubakar,zainura tana musu fashin baki,nan har aka gama daurin aure ana ta hada hada,sai ga cikin gidan Malam an nuno Mata ana saukewa ana dorawa,Umma da Anty Rukayya na hada hada cikin Murna,Na'im da abokai na shige da fice, Anty Rukayya sai kula take da Ango haka Umma da Malam,Na'im yaga yanda suke masa tuni ya fara Hawaye a zaune,Aka tafi gidan yan Matan Amarya Salma,Salma ansha kyau irin color na Na'im,ana ta hira ana cin abinci,sai ga Ango yanda yake manne da Amarya,Haka Amarya tana ta zuba shagwaba yana bata abinci a baki tana bashi,Zainura tana kara karanta abin da wanda ma ba a nuna ba,Har aka zo aka gaisar da su Umma ana ta pics,anzo wajen kida yanda aka rakashe,ana zuwa wajen me rawar Michael Jackson Na'im da Salma suna hawaye suna dariya,yan dakin ma sai dariya suke,ana ganin irin rawar da mutanen kauye sukeyi,ga yanda Amarya take ta faman ji da mijinta shima haka suna daukin juna,kamar su cinye juna, an sa wakar Ado gwanja ko anki ko anso nine gwanja sai ga Zainura ta shige fili tana ta takawa,kowa ya kalleta ana dariya a palon Salma da Na'im suna mata liki,Zainab ma ta shigo tana juyawa haukar Zainab harda girgiza Irfan Ya dinga dariya dasu Aisha,ba kamar Hunaif ma yanda yace sai an taro me rawar Michael Jackson sun kara gani,sai da aka haska komai,Dada tana cikin kallo da Mummy suma sai hawaye sabo da tausayi abin ya taba musu zuciya yanda Malam sukayi halacci da mutanen kauyen tare da frnds na Na'im da Salma,Aisha tace ina son wannan Anty Rukayyan she is wise enough.

Na'im ya kashe bayan an gama,Zainura tace akwai a wannan wayar har wanda ba na biki ba kunna a gani,nan ma aka fara danno na waya daya bayan daya.
Sai next page zaku ji mene a wayar tasu tare da Album.

AsmaBaffa[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉

131-135 136-140

Official

By
AsmaBaffa

Fans kun rage Sharhi gaskiya zan rage yawan typing.❤❤❤❤❤❤

ZEEMAMA wannan page naki ne.

Waya ya kunna tare da sa mata USB ya jona da Computer yanda kowa zai gani,video ta farko Salma da Na'im suke ta hira cike da so suna can bayan gari a kauyen wurin wasu bishiyu na mangoes,Sai wanda take wanke masa kaya da guga yana daukanta shima yana daukan kansa,Sai su Umma da Malam ma suna ciki dasu,wani suna girki a kitchen tare,suna cin abinci,har aka dawo kan na bikinsu,nan ma waje kala kala,sai ranar da aka kawo Salma dakin miji,tana Amarya a lullube ya daukesu tare suna yiwa juna kallon so,sai kuma wanda sukayi bayan bikin da gidan aurensu na kauye gaba daya ko ina,wasu ma kunya suke ji ana gani dasu Mummy suna rashin kunya,Har suka koma kan pics,Malam Umma dasu iri iri,sai nasa da Salma ba kalar da basu dauka ba,har na biki,bayan sun gama na waya suka koma Album aka Sha kallo,wasu abin tausayi wasu dariya haka dai aka gama.

Na'im da Salma sai tunani sukeyi ko zasu tuna amma sun kasa,Na'im yace Allah yasa na tuna ko ban tuna ba sai na koma kauyen nan gaskiya,Salma tace wlh kuwa,nan suka mayar da komai suka boye abinsu,Salma tabi bayan Na'im part dinsa,yana saman bed yana faman kokarin tuna su Malam,Salma ta zauna tare da cewa Dan Allah Honey ka bari naje wajen su Ummitu da dangina,ni yanzu su suka dameni, mutanen da basu damu dake ba shine zaki je suci miki mutunci ko?Salma tace ae naji amma ai iyaye na,kai kana cikin naka dangin ni kuma ina nawa?ya kamata ka tausaya min, kema kin San wahala zaki sha kawai baza su yarda dake ba muyi rayuwarmu idan sun gaji sai su nemeki, Fara sheshekar kuka tayi,Na'im yace akan haka kike wannan kukan?tace ni bazan taba samun kwanciyar hankali ba matukar bani da kowa nawa for God sake wlh bazan iya wani aure ba idan kace bazanje ba sai dai mu rabu gaskiya,ni da dangina kace bazan je ba,kuma Su Affa ko me suka min ai su suka raineni har na girma muka hadu.
Tunanina kai me daidaitani da dangina nane Ashe baka kaunata tunda kace bazan je ba,Na'im yace ikon Allah ni ba hanaki nayi ba Hajiya Salma ga Driver nan a dawo lfy,ni dai bazanje ba su kara wulakantani ba,kin San sau nawa naje nemanki wajensu lokacin da kika bace ba irin wulakancin da basu yi min ba amma na hakura still ina zuwa wajensu.

Amma ai sai ka barni naje haka idan basu yarda dani ba sai na dawo,ban hanaki bafa kije ga Driver nan idan ma da kanki zakiyi Driving sai kin dawo Allah kaiki lfy ya Mike tare da ficewarsa,Wani Bedroom din ya koma can daya part din ya kwanta saman bed yana tunanin halin Salma na yanzu,shi to ya zaiyi da ita ne wai bata Jin magana.
Salma kuma yanda yace taje tasan baya so ma taje kawai bata San manufarsa ba,amma zata ci gaba da rokonsa.
Na'im tunaninsa ma haushin da ta bashi da take wani ambatar wai sai dai su rabu,baza ta iya ba,tama raina masa hankali wlh amma zaiyi maganinta.
Chapter 45 · 0% Book details