← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 80

Sashe 41

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainura ta fashe da Kukan Dadi haka kawai aka ji tana kuka,kowa saida yayi tunanin wani abu ne ya sameta,Salma tace lfy Zainura?Zainura tana goge hawaye tace ni ya zanyi Allah yana sona ta kara zubo da Hawaye tare da cewa badan ikon Allah ba ya zanyi nazo garin nan har cikin wannan Aljannar duniyar haka cikin turawa,ni iya haka ma ya isheni darasi a duniya,ta kalli Na'im ta goge hawaye tace ni wlh na fasa auren Kanin naka kunnensa yayi ja da yawa gasu nan irinku daya ni jansa yayi min yawa yasin.
Hhhhhhhh gaba daya palon suka dinga dariya kamar me,Umma tace ke dalla zauna sarkin surutun jarabar tsiya ke ko ina bakya kasa magana? Zauna mana cewar Mummy tana dariyar Maganar Zainura,ta zauna kusa da Hunaif ta tashi ta dawo Kusa da Irfan nan ma ta mike ta dawo wajen Na'im tace alquran mijin Salma yafi fuskar Rahma.
Akayi dariya nan ma ta dawo wajen Malam tace ga na gida wanda na sani.
Mummy tace ya kamata kuci abinci ku huta kuyi wanka sai a zauna ayi maganar.
Salma ke da kike yar gida ki dauki Umma da Malam din ki kaisu dakin dake kasa yafi girma za sufi sakewa a can,Aisha ke ku tafi da Zainura dakinki ki koya mata komai ta shirya.
Salma ga dakinki nan dama ba wanda ke shiga gyarawa kawai akeyi,kaima Na'im haka,kuje ku fito aci abinci.Salma ta raka Malam da Umma dama Malam da Umma su wayayyu ne suna mu'amula da yan birni sun iya amfani dasu duk da cewa na gidan su Na'im basu taba ganin irinsa ba saida Salma ta nuna musu, ta wuce dakinta,Na'im tuni yaga yanda Bedroom nasa ya koma kamar wata Aljannar duniya,ya fada wanka,kayansu tuni guards sun kaiwa kowa dakinsa.

Aisha da Zainura suka shiga Bedroom tare,Zainura tace duk wannan dakinki ne? Aisha tayi murmushi tace ae mana Zainura tace cab yo mu a kauye ba sai mu goma mu kwana ciki ba,Kinga gidan su Zahrau kawarmu dakin kamar akurkin kaji Amma su Bakwai suke kwana daki daya,yara suyi ta tsula fitsarin kwance,Aisha tayi dariya tare da cewa mene Akurki? Zainura anyi har Jss3 tace cage na chickens hhh Aisha ta gane tace gaskiya ne,muje kiyi wanka da dare kya bani labarin kauyen naku,nan ta raka Zainura ta koya mata,Zainura ga basira har ta iya,Aisha tace Daura Towel ungo karbi,Zainura ta rufe baki da hannu tace a gabanki ki kallarmin jikina,kuma wannan guntun tawul haka ni dai bani Zani a Cikin jakata ina da abuna,Aisha ba musu ta zuge yar jakar Zainura ta dauko Zani spear har kamshi yakeyi ga brush dinta harda sabulu give guda da mudubi da Powder da jambaki ja har jagira,Aisha tace a ranta wannan a kauyen ma su daban suke gaba dayansu masu Tsabta ne jibi har tasan tazo da brush da toothpaste,harda kayan kwalliya,Nan dai ta bawa Zainura Zani ta cire kayanta tayi wanka tana gama wanka akwai botiki a toilet din ta wanke kayan da ta cire tas ta fito tace da Aisha ina zanyi shanya? Aisha ta nuna mata bayan corido nata ta shanya kayanta har pant data cire bra ce kadai kuma bata sawa.

Zainura ta fito Aisha ta kalli gashinta har kafada baki me santsi na yan fulani yasha kananan kitso sabo,Aisha tace yaushe kikayi kitson nan?tace jiya aka yi min yau sunan Kawarmu Allah yasa Malam ya taho dani nan garin,Aisha tace uhm yayi kyau,ai kema fara ce Amma kina ce mana jajaye? Zainura tace ba irinku ba ni ai bakace ko Salma ban kai haskenta ba bare ku turawa.suna ta hira har Zainura ta gama ta dauko riga da skert dinta shima na sallah ne Lace ba wani me tsada bane Amma dinkin dan dai dai ita tasa abinta harda yin acuci Maza Sabo da kitsonta shuku ne, ta yafa bakin gyalenta bayan ta shafa Powder da jambaki Amma bata Sa ko kwalli a idonta ba,ta kalli Aisha tace to ina zan Sa jakata kar ta hargitsa miki daki,ganin Zainura me tsafta ce Aisha ta karba ta sa mata a sip bari daban da bata Sa kaya,Zainura tace karki gaji dani naga kina danna waya na hau gadonki na kwanta ko shimfida zaki min? Aisha tace gadona fa kika ce? Ki tsaya a matsayinki karki ga na miki mutunci ki zake kuma zan mai dake dakin Salma ba wajena ba kina min kauyanci.

Zainura ta kalli Aisha tace toooo ikon Allah sai kice nima na fito da kalar daya halin nawa hali biyu gareki,dana mutunci dana tsiya gidan kikazo nima sune dani,kan Uba na miki kauyanci kikace gadonki din me?an fada miki bamu da gadon mu? Wlh baki Isa ki rainani ba sai dai ki raina tsohuwarki da tace nazo wajenki danma kin mun mutunci ne da farko Amma wlh da na nuna miki wace Zainura,Zainura taja tsaki,Aisha taji haushi kamarta wata yarinya karama yar kauye zata zageta dan kawai ta sakar mata fuska ita dama bata so Mummy tace yar kauye tazo mata daki ba,dama darajar Mummy taci har ta biyeta sukayi hira Amma da badan Mummy ba wlh da sai tayiwa Zainura duka a gidan.

Zainura ta fada saman gadon Aisha tana sani tace sai an hau ma a yankani,Aisha ta matsa gefe can tace ke nafa girmeki ba sa'arki bace Naga kina son rainani banza yar kauye zaki shafa min dirty,Zainura tayi banza da ita tace bazan biye miki ba mu zama daya Amma zanyi maganinki kafin na bar gidan nan,Nan Aisha ta dinga zage zage da mafisa tana ta ciwa Zainura mutunci akan yan kauye ne.

Mummy ce ta shigo ta dauka hira sukeyi ta kirki tsakanin Aisha da Zainura,tace ku fito aci abinci,Sun fito a hanya Aisha ta bangaje Zainura,haka Zainura ta kyaleta kawai.

Malam,Umma,Salma,Zainura,Aisha,Mummy,Irfan,Hunaif, Dada Babar Mummy, Na'im kadai ake jira,idan kuka ga wankan da Salma tasha sai ku rantse daga Misira tazo shigar larabawa tayi.
Abinci aka jera iri iri a palo ba a dining ba Katon carpet aka Sa wajen.
Kamshi ne ya cika wajen wanda yasa kowa kallon inda ake tahowa ba kowa bane face Na'im ya dau wanka cikin tsadajjiyar shadda fara yana kyalli da sheki,Malam da Umma kallonsa kawai sukeyi Kamar ba Muhd dinsu ba Sam ya manta dasu ko tunasu baiyi,haka Salma saida gabanta ya fadi Sabo da kyan da yayi,Mummy farin ciki sosai dasu Irfan da gani Na'im ba wahala yasha a inda yake ba,domin jikinsa hutu da jin dadi ya nuna ba wahala ba.

Kusa da Salma ya zauna tare da dan bugunta kadan a baya irin na tsokana murmushi kawai tayi cike da kunya Sabo da Mummy dasu Malam sun gani,Abinci aka baje kowa ya fara cin abinda yake so,Zainura ce kadai take ta ruwan ido ta rasa wanda zata fara da shi,Salma tace kici mana,Zainura tace ni dai a zabar min,Hunaif ya maka mata harara ya dauke kai, Dada tace yau naga yarinya da tsiya sai an zabar miki ma? Nan Zainura ta fara ci itama har suka gama ci kowa ya koshi

Malam ne yayi bismillah tare da Budewa da addua sannan ya fara bayani akan abinda ke tafe dasu,kowa yayi shuru yana sauraro.
Malam ya basu labari tun a inda ya tsinci Na'im sai Salma,da kuma irin zaman da sukayi cikin jin dadi da kaunar juna har dalilin da yasa ya daurawa Salma da Na'im aure tare da gabatar da shedu masu karfi,har littafin da aka rubuta da shedu ya basu Suka karanta,Mummy da Sauran mutanen wajen murna,farin ciki tare da jinjina sukewa Malam,godiya suke musu ba adadi,tare da fadawa Malam ba matsala dama can Saurayi da budurwa ne kamar yanda Na'im ya fada musu a kauye haka ma su Mummy suka basu labari.
Dada harda Kukan Dadi da tausayi,haka Mummy ma,bayan Malam ya gama bayaninsa ya sanar musu gobe zasu koma kauye,Mummy dasu Dada suka ce sai sunyi sati suna ta rokonsu da kyar suka yarda zasuyi kwana Uku sunki yarda da Sati dayan.
Mummy tace yanzu basu tuna wacce rayuwa sukayi daku ba Malam ina so in ba damuwa a bar mana Zainura a nan zuwa wani dan kwanaki tana tuna musu rayuwarsu ta baya da sukayi a kauye ko Allah zai sa Memory nasu na baya ya dawo gaba daya,idan zuwa wani lokaci bai dawo ba da kaina zan dawo da Zainura gida,Zainura Zaraf tace Allah Baffana bazai yarda ba sai dai idan Malam ne ya masa bayani,ni dai nafi son kauyenmu Yasin kina gani yanda wannan Aisha take min rashin mutunci a dakinta idan ana so na zauna sai dai a hada mu daki daya da Salma idan ba haka ba Alquran kauyenmu zan tafi nima ina da iyaye suna sona ko bamu da kudi na rungumi talaucinmu bana maitar abin duniya.

Na'im yace sai dai a baki Room ke kadai dai amma Salma tana da aure taya zaku kwana tare bazai yuwu ba wlh ni kuma fa?

Mummy ta harari Aisha tare da cewa nasan zaki aikata dama kuma wlh sai ta zauna dake,ke Zainura idan tayi miki ki rama ko zaginki Aisha tayi ki rama ko dukanki tayi ki tabbatar kin rama,Zainura tace an gama Mummy wlh zubarwa yarinya hakora zanyi,Aisha tayi mukus da ita,Malam ya kira Baban Zainura yayi masa bayani cikakke yace ba matsala Malam ai mun yarda da kai.
Chapter 41 · 0% Book details