← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 80

Sashe 46

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka yayi ya shirya sosai yayi kyau tare da haurawa Part dinsa domin daukan Wayarsa ya hango Salma gefen Bed sai hawaye take,kallo daya kawai ya mata ya dauki wayarsa yayi waje abinsa,abin ya dameshi bai son Ganin Kukanta musamman da ya San bata da kowa yanzu na iyaye,Embassy yaje yayi abinda zaiyi ya dawo.
Salma ya hango tana bacci tayi dai dai saman Bed dinsa daga ita bm short da yar riga cikinta gaba daya a waje,nan take Hankalin Na'im ya fara tashi ya taimakawa kansa tare da shigewa Toilet ya fara wanka,yasan Koma ya nemi Salma ba yarda zatayi ba indai ba wajen danginta taje ba yaga ma hankalinta baya kan komai sai danginta.

Bayan ya shirya sai lokacin ta farka idonta yayi dan ja,gashinta ya rufe mata rabin Ido sai ya bada wani sexy look,Na'im ya kalleta nan take yaji wani farin ciki yana ratsashi Salma bata laifi a wajensa,bare da bata da abin Zafi barta idan shagwabar ta motsa to sai kallo,
Yanzu ma tana ganinsa ta rarrafo jikinsa zata hau ya goce ya matsa tare da cewa ki kwanta a bed dinki,kina taba ni dole zan miki dole abinda bakya so,ki kiyaye taba jikina,Salma ta wani Kebe zatayi kuka tace dan Allah ka barni naje wajen ko su Affa ne pls,Na'im yace na barki am serious kuje keda Zainura nasan ta fiki baki zata tare miki,nima idan komai yayi settling zanje na gaishesu,amma 1day na baki kacal,bari na miki booking flight sai kije har can Maiduguri suma 1day tal ki dawo,idan kika kara Allah kinji na rantse saina kwankwatsaki wlh,Salma dadi yasa ta rungumeshi tana shakar kamshinsa tare da cewa sai kace wata attaruhu kuma,Na'im yace uhm yanzu ai kin fara magana sabo da zaki tafi unguwa,

Salma da Murna ta sanarwa Zainura zata Rakata nan ta sanarwa Zainura tarihinta kaf,Zainura ta jinjina taji tausayinta tace lallai kinsha wahala Salma,bari na shirya yanzu har jirgi za a hau dani?Salma tana dariya tace ae Zainura tace yau sai nayi Sallar dare Nafeela Alquran.

Yau Salma tana murna gobe zata je wajen yan Uwa da wuri ta shirya cikin wata tsiyatacciyar Night Gown ta fito kamar Amarya tana zuba uban kamshi,harda shiga kitchen ta hadawa Na'im tea me kamshi da dadi ba madara ciki yanda taga yana Sha da dare.
Ta shigo sanye cikin Hijab dinta,tun kafin tazo kamshinta ya bigi hancin Na'im,Aiki yake a System,ya dago ya kalleta tayi wani irin kyau na mamaki,Tea din ta ajiye a kasa cike da nutsuwa ta zare Hijab dinta,Na'im ya kusa shakewa sabo da yanda yaga Salma kamar a Indian Film, gefensa ta zauna a kasa itama tare da wani kasa da murya barka da aiki,Na'im yace wato Salma sai na barki abu zakiyi abinda ya dace,tace me ka gani?yace yaushe ma rabon da kizo wajena haka sai na rokeki hakanma da kyar kike zowa sai kin ga dama,dan na barki kije Wajen Family naki shine zaki wani zo,to Bana so tunda badan Allah kikayi ba,ni dan Allah na barki zuwa can,tashi ki tafi room dinki kici gaba da kwana ke daya,

Salma taja ajiyar zuciya tace Wlh badan haka bane kawai yau nishadi naji ban san dalili ba kuma ma ai ina so dama na gyara halina,idan kace a'a taya zan gyara to,Allah yau ma Zainura tayi min fada sosai kuma naga ban kyauta ba shi yasa,amma tunda kace na tafi shike nan,ta Mike tana jira yace ta tsaya taji shuru har ta kai bakin kofa ta juyo da kanta tare da cewa zan tafi fa,yace ok,tace Sai da safe,yace Allah kaimu,tace Ameen tayi shuru kuma taki tafiya,ta kara cewa uhm ni dai zan tafi kuma,ta bashi dariya ya gimtse yace to a gaishesu.

Ta gaji da tsaiwa yana ta aikinsa,yace yawwa zo ki dauke tea dinki ma,ta taho kamar gaske zata dauka sai ta rufe system din,harara ya zuba mata,gabansa ta dawo kamar zata shige masa ciki,hannayensa ta riko da nata tare da waresu nan take ta shige kirjinsa ta hade kirjinsu waje daya,Na'im ya fara borin Iska irin baya so wanda a zahiri tuni ya tafi wata duniyar karfin Hali yake.
Salma kamar zata masa fyade haka ta hade bakinsu waje daya ta shiga tsotsa sosai tana masa wasu salon wanda Bai San ta sansu bama,nan Na'im yayi Surrender tare da rungumeta tsam a jikinsa kamar zai maidata cikinsa,dama kadan yake jira, saman Bed suka koma ba tare da sun sani ba,yasa hannu ya kashe light duf,
Nan take ya rabata da kayan jikinta shima haka Deep Romancing sukayi me dumama zuciya tare da tsumata,Salma taji dadi sosai shima haka,saida suka huta,ya rada mata fyade zaki min? Dukan wasa ta masa a kirji cike da shagwaba,a hankali yace da gani kin saba da wannan na yarda da Zainura munayi, yana shafa kirjinta yace ina fara wasa da wannan kika haukace,Salma ta boye fuska a kirjinsa tace nidai ka bata min jiki muje muyi wanka.
Tare sukayi wanka tare da kwanciya,tana manne jikinsa yace kyaleki nayi yau sabo da nan da 2wks zamu koma gidanmu da zamu zauna.
Salma tace hmmm Allah ya kaimu,yana shafa gashinta yace amma idan mun koma kema kin San ba mutunci,Salma tana murmushi tace ba komai nasan ma ka taba yi a kauye tunda kamin abubuwa da yawa yau banji Zafi ba a wajen kaga kuwa anyi ma.
Na'im kuwa wayo yayi mata cikin Romancing ya dubata ya San baiyi komai ba,zai wahala ace yayi Sex Virgin ce still,amma sai yace ai ba sau daya bama,domin da sau daya ne ina taba wajen sai kinyi kuka,Salma tace hakane shike nan Allah kaimu mu tare na daina tsoro tunda dama wahalar ta wuce tuni.

Washe gari Mummy tace ai bazai yuwu Salma da Zainura suje su kadai ba sabo da dole ayiwa dangin Salma bayanin aurenta maganar Aure bata yara bace kuma ba wasa bace,Haka Mummy da Dada suka shirya takanas suka bi flight suka fara Sauka a Borno state gidan su Shehu da Malam Musa,ganin masu kudi Salma tazo dasu ba wasa,Shehu duk da a wulakance suka karbesu amma sun sauraresu,Dada ta musu bayani Malam musa yace Allah sanya Alkhairi,Shehu yace na taba ganin iyaye mata da shiga sabgar Aure? Kuma za a rufe mu yar da take tamu shine za a mata auren bariki sai daga baya za a zo a sanar mana sabo da ba a daukemu da muhimmanci ba,ba a mai damu iyaye ba,to Allah ya bada zaman lfy me kuma zamu yi mu ai sai Ku tafi da abarku,Mummy da Dada suka dinga basu hakuri ana musu bayani amma sukace su fa basu ce komai ba kuma Salma dole dai tasu ce ba uban wani ya haifeta ba dan haka dole ta nemesu aure kuma Allah bada Lada suje kar a cika su da surutu.

Hashim ne kadai ya kai su Mummy bangarensa Maimuna ta musu sauka ta mutunci,kuma ya tsaya ya gane duk abinda su Mummy suka zo dashi ya rufawa Salma baya,haka dangin uwar Salma Ubale da Matarsa Iklima sunyi murna kuma sun fahimci komai tare da sa albarka.
Mummy tace su kwana wajen Hashim Salma da Zainura wajen Ubale da Iklima suka kwana cikin Jin dadi.

Washe gari sukayi shirin Tafiya Mummy ta bawa Hashim Dubu Dari wai idan Maimuna ta haihu ayi suna,ya dinga murna da godiya,haka Ubale ma ta bashi Dari,harda durkusawa dan Murna,ta bawa Malam Musa shima,haka Shehu uban yan son kudi nan take ya canja ya fara nunawa Salma so yana mata fara'a sabo da kudi,matan gidan kuma kaf Dubu Ashirin aka ba ko wacce ta ja jari sannan suka tafi.

Zainura tace Bala'i Wallahi Salma danginki son kudi garesu,jiba rashin mutuncin da suka mana,daga Hashim sai Ubale ne suka karbe mu amma sunji kudi sun rude Allah ya shirya gwara da basu suka raineki ba Alquran da tuni sun jona miki son kudi.

Abuja suka dawo basu koma gida ba Mummy tasa Driver ya wuce dasu kauyen su Affa,suna Sallma a gidan Affa yana gyarawa Akuyarsa igiya ya hango lallai Salma ce da iyayen barikinta,Ummitu ta fito da kwarya da gari ciki,Su Mummy suka mata Kwarjini da gani an San kudi ya zauna musu,shuru sukayi basu ce su shugo ba kuma basu ce ga wajen Zama ba,Zainura ne ta shiga tare da rafka Sallama ta hango tabarma a jikin bishiya kamar gidansu ta jawo ta shimfida tace Ku shugo Mana,Affa dai basu iya magana ba sunga Mummy kalar Naira ba wasa,Bayan sunwa Kansu masauki nan Mummy tace Ku zauna Malam za muyi magana akan hanya muke,da kyar Affa ya zauna can nesa tare da zaburowa da Masifa muna saurarenki.

Mummy ta fara da Nasiha haka Dada ma ta nuna musu hakkin Salma dake Kansu a Matsayinsu na marikanta sannan ta musu bayanin komai har auren Salma,tare da fahimtar dasu su Affa sun San gaskiya amma suka take sani wai dama to mene a ciki sai me kuma dan tayi aure Allah sanya Alkhairi,Mummy sunga rashin Imanin su Affa,Salma kuwa murna tayi tasan an samu ci gaba domin da ace dane basu isa ma sun shiga gidan Affa ba,amma yanzu har sauraransu sunyi ai abin farin ciki ne,Mummy taga harkar ta su Ummitu ba mutunci ciki tace to Salma zamu barki a nan gobe kya dawo ko?
Affa yace ina? Yanda kuka zo da abarku Ku tafi da ita,Dada tace oh Ku kuwa bayin Allah kamar baku San darajar Dan Adam ba?Ummitu tayi tsagal tace kija girmanki iya mun fiki Sanin wace Salma ba ruwanku,Salma tace ya isa a bar zancen nan take Salma ta rubuta address kamar yanda ta bawa su Malam Musa haka ta rubuta Address na inda take da Phone Number ta mikawa Ummitu tace a kyale zancen haka gashi nan duk ranar da kuka huce kuka gane gaskiya zaku nemeni,Mummy Ku taso mu tafi,Nan Mummy ta zaro makudan kudi ta mikawa Affa ya buga tsalle yace bada ni ba,baza a siyeni da kudi ba,na karbi Dubu Dari nazo ina asarar milliyan daya ina dalili kuje da tsiyarku.
Chapter 46 · 0% Book details