← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 80

Sashe 20

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Salma da Raheel suna tare a asibitin Mahaukata suna ta hirarsu amma Sam yanzu bata son Raheel tafi son tayi hira da Na'im,sai taji Raheel baya birgeta Sam,Raheel yace na fada miki dama indai kika yarda sukayi miki magani saina haukataki,kuma na daukeki daga gidan,yanzu nan ne gidan zamanki tunda ban gama cika burina a kanki ba sai kin kara ajiye min yara biyu sannan kika gama min aikina,Salma dai tayi banza dashi Na'im kadai take so ta gani a duniya.
Likitoci sunga Salma na magana ita kadai tana Hawaye ta fara shagwaba tana shure shure kawai suka ebo Allurai zasu danna mata Raheel yasa ta shaki daya da karfin Aljanu tayiwa likitoci dukan gaske,amma duk da haka saida securities suka riketa suka tsira mata Allurai har kala Uku ta zube a wajen sharaf sukayi ciki da ita aka kaita can wani daki tare da shinfidar da ita.

Kimanin wata daya kenan da bacewar Salma Mummy ta matsa Na'im dole sai yayi aure duk da cewa yanzu baya kawo mace ko daya gidan sabo da shi ta Salma yake,ya zaiyi ya nemo ta,Mummy ta sameshi har bedroom tace Na'im kasan dai ba wasa nake da kai ba ko? Mahaifiyata nima ita ta bani umarni dole kai da Irfan sai kunyi aure a watan nan,duk kun Rame tunda yarinyar nan ta bace baku da sukuni amma idan kunyi auren zaku ji sauki matarku zata ebe muku kewa.

Na'im ya kalleta nan take ya fara hawaye cike da shagwaba yace ina wani ebe kewa ni Bana son kowa me zata min naji dadi,kawai a daura Min da Salma idan a naso a ganni na samu jin dadi,Mummy tace baka da hankali yarinyar da ta bace bat kuma Aljanu gareta tana yawace yawace shine zaka ce wani zaka aureta,ae ni dai ina sonta haka zan mata magani wlh in dai ba ita ba sai dai ko Dada ta tsine mika Momma Danni ba ruwana.
Fuuu Mummy ta bar masa dakin ta koma wajen Irfan yana kwance yayi wanwar Son Salma ya addabeshi Mummy nan ma ta masa bayani budar bakinsa yace ai sai dai a mutu wlh Dadan me itace Mamanki ai ba tamu bace ni wlh in dai ba Salma ba to ba wani aure da zanyi a kan haka ma kuna takura min zan koma neman matana dama ta dalilinta na shiryu.
Mummy tace to kaima Salman ce kenan?yace yeah,to ai baka dace Da ita ba tunda fada kukeyi,Na'im yafi dacewa da ita Irfan to kuwa indai an bawa Na'im Salma nima sai dai na auro Balarabiya tsohuwar budurwata ta UK wacce kika ce bazan auri yar can ba,Kai kafi Na'im ma rashin kirki Irfan ta bashi dukan wasa a baya bakwajin magana Allah dai ya shirya min Ku addua ta kenan,Allah Zaba abinda yafi Alkhairi.

Haka ake son iyaye ba a dauki Zafi akan yaro ba ayi masa dole karshe abin yazo ya kwabe a samu matsala ana dana sani,wasu kuma a dinga zagin yaro ana masa baki akan ya fadi ra'ayinsa a'a dole abinda iyaye sukace ko na sabon Allah ne sai ace sai yayi,idan ba ayi ba su tsine ma ko su fara kuka Allah yayi fushi,yaron ya lalace karshe rayuwarsa taki albarka.iyaye a daina saurin zagi da tsinewa yaro ko zubarwa da yaro hawaye ayi hakuri a dinga dannewa.

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉

61-65

By
AsmaBaffa

Zainab Atiku Salama Happy Birthday to u,Allah karo shekaru masu amfani,Na'eem ma da Salma sunce HBD.sun bada gift na perfume na saceshi🤣🤣 Sardauna da Ramlat Night wears da kayan daukan wanka kala goma suka kawo a baki gift,Lantan shadda yar gaske,Dafta tare da Hajara sun kawo super Holand kala biyu da readymade ta kasa me tsarki suma du nayi sama da fadi dasu😀

FLOWER,AUTA, ASYCOOL,MARCYCOOL,MAMAN SAMHA,MAMAN MEENAT wannan page naku ne.

Wani Malamin Doctor ne ya gano lallai Salma Aljanu gareta kuma tana da hankalinta,sabo da haka kawai yayi magana da Doctors zai fara gwada mata na Musulunci sabo da asibitin sunayi idan an fuskanci Aljanu gareka.
Sati daya Raheel ya tabbatar za a rabashi da Salma kawai sai ya juyar mata da memory lfy lau take da hankalinta amma bata iya tuna kowa bata gane kowa gaba daya ta manta abinda ya faru baya,Haka Na'im ya fita Office Embassy kawai Ya fito da niyar tafiya gida,Raheel yazo ba wanda ke iya ganinsa kawai yayi sama da Na'im bat suka bace,bai direshi ko ina ba sai can cikin wani kauye can kusa da Katsina state,Kamar anyi masa duka haka aka tsinceshi a gefen titi duk yaji rauni a jikinsa ko motsi baya yi,shima Raheel sabo da bakin ciki kar Salma ta auri Na'im ya raba musu gari sannan shima Na'im ya goge masa Memory na baya,bazai iya tuna kowa ba sai rayuwarsa ta yanzu.

Kowa yaga Mutum kyakyawan gaske kamar Aljani wasu suce bature gashi kalar kudi komai nasa me tsada ba wanda ya daukeshi haka ya kusa yini yashe a gefen titi,sai da Allah ya kawo wani malami kuma maharbi wato Malam Magaji shine kadai yayi shahada a wannan kauyen ya dauki Na'im ya kaishi gidansa,gidane na na bulon siminti ko ina ba kasa a gidan me kyau,daki Uku ne a gidan sai na Malam dake zaure,Toilet biyu ta wanka ma daban,dayar kuma Masai din irin ta flowshing amma ta siminti,Malam Magaji dama yana da wadatarsa a kauyen yana noma me tarin yawa,ga mutunci da hankali sannan kuma yana zuwa daji farauta.
Har yaran kauyen yana koya musu karatun Allo da safe da yamma,gashi wayayye kamar ba dan kauye ba,haka matarsa Haleematu Dattijuwar kirki ce kwarai gata da bala'in tsafta kamar me komai a wanke a gyare a goge tsaf,gidanta kullum kamshin turaren wuta me dadin gaske,dakunan Bedroom sunsha Red carpet masu kyau da bed kanana dai madaidaita,dakin Malam ma haka,store dinsu da kitchen komai akwai na kauye dai dai me karamin karfi.
Koda ya shigo da Na'im kwance kamar gawa Haka Haleematu ta karbeshi hannu biyu biyu wani magani Malam Magaji ya shafawa Na'im a fuska sai ga Na'im yaja ajiyar zuciya ya Mike zaune yana salatin Annabi,sai kallon Haleematu da Malam Magaji yake faman yi,shi Bai iya tuna komai Bai gano shi waye ma a ina yake Sam ya kasa tuna komai,Malam ya tambayeshi yaro tsintar ka mukayi a titi su waye suka dakeka haka?Kuma daga wanne gari kake? Na'im ya fada tunani yayi yayi amma ya kasa tuna komai,cikin hausarsa da bata da kyau yace wlh bani San kowa ba,bana iya tuna komai,ban san kowa ba,Malam yace subhanallah Wala Allah dukan da mutanen suka yi maka shine yasa sun bugeka a kwakwalwa yasa baka iya tuna komai,yanzu samari Kaci gaba da Zama damu har Allah yasa Kwakwalwarka ta dawo dai dai ka fadi inda kake a maida kai can wajen iyayenka,shi dai Na'im murmushin yake yayi kawai yace to Dad,a'a ka dinga kiranshi Malam ni kuma Umma zakace cewar Haleematu matar Malam,yace to kawai yayi shuru abin duniya ya masa Zafi ya kasa tuna mutane da abinda ya shafeshi sai Hausa da turanci yasan abubuwa bai san ma'anar su ba.

Haka Suka dafawa Na'im ruwan Zafi sukace yaje yayi wanka,ya shiga Bai taba yin wanka da ruwa a bowl ba sai yau haka yayi da kyar,toilet din me kyau ce sosai tasha wanki sai kamshi take,abinda ya daurewa Na'im kai shine kayan sawa akwati guda Malam ya mika masa yace wannan akwati a gefenka muka ganta an ajiyeta kuma kayan sawarka ne a ciki,Na'im mamaki ya kamashi,kuma da gaske Raheel ne ya ajiye akwati guda ta kayan Na'im da ya hado masa a bedroom dinsa,komai na kaya akwai kanana da manya na hausawa,kaya na Alfarma,Na'im yasha mamaki kayan size dinsa ne,to ko a mota ya fito zaiyi tafiya aka kamashi?ko iyayensa ne?ko mene oho ya kasa tunawa wannan kayansa ne na gida,harda manyan turaruka a ciki.komai cif kamar shi ya hada kayan,Malam yace ka daina matsawa kanka ga dakinka nan jeka da akwatinka ciki ka shirya,haka yaje ya shirya cikin riga da wando kanana yasha kyau,raunin da yaji duk Malam yasa masa magani a wajen.
Haleematu ta kwashe kayan da Na'im ya cire ta wanke masa su fes ta shanya domin da gani Na'im ba dan nan kasar bane bature ne bai saba da wahala ba,kaddara ta kawoshi nan.
Mutanen gari dai suna ganin gangancin Malam Magaji na daukan Na'im wa ya sani ko Aljani ne,Malam Magaji yace samari bamusan sunanka ba kawai zamu dinga kiranka da Muhammad,ba musu yace to na gode.

Haleematu tuwon danyar shinkafa ta kawowa Na'im miyar gyada da nama sosai ciki,sai ruwa purewater dama Malam a kauyen ma basa Shan ruwa sai pure water daga shi sai matarsa basu taba haihuwa ba a duniya,yayi aure aure da dama amma baya haihuwa suka gudu matan,daga karshe ya auri Haleematu wacce itama mijinta ya saketa sanadiyyar rashin haihuwa shine suke zamansu lfy,kwana Uku tsakani Na'im ya saba da Umma da Malam kamar dansu haka suke har yau Bai iya hausa sosai ba.

Salma kuwa Doctor ya zuba malamansu na Hospital an fara yiwa Salma magani,cikin hukuncin Allah Raheel yaji wuta ya fara magana,yace tun Babar Salma tana da cikin Salma ya shiga jikin Salma sakamakon ruwa da ta tsallaka a cikin Komi zata haura wani kauye a garin Nijar, tun daga lokacin yake jikin Salma kuma yana sonta yama kusa aurenta zasu rabashi da ita a banza Bai cika burinsa ba,
Haka ya dinga fadan duk abinda yake sa Salma tanayi marasa kyau,Sosai Malamai suka bude masa wuta ba ji ba gani sati biyu suka samu Raheel yace zai fita wlh can zai koma wata duniya,da kyar suka samu ya fita daga jikin Salma har abada.
Chapter 20 · 0% Book details