← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 80

Sashe 32

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe suka tashi anyi sallah suka dora da hirarsu again har Anty Rukayya ta kawo musu abinci,Waina,sinasir,da tuwon shinkafa miyar egusi tasha Nama,Salma ta hada musu tea da kayan da Na'im ya siya mata jiya suka Sha sannan yan matan suka tafi gida zasuyi wanka su dawo kafin a daura aure,daga Salma sai Rahina suka gyara gidan kwas sai kamshi Sannan ta dafa musu ruwan Zafi sukayi wankansu,Abubakar suna tare da Ango ana shiri.
Cream Salma ta shafa me kamshi a jikinta sannan ta dauko sabon lace dinta ruwan toka yasha dinki me masifar kyau,riga da zani me style sai ka rantse ma skert tasa yanda yabi jikinta,kwalliya ta fara yiwa kanta,ta shafa powder me kyau,eye liner ta zizara a saman Ido,kasan Ido kuma tasa kwalli kadan idon ya koma kamar na larabawa,bata zana gira ba tajeta tayi da Brush ta gyarata sai kace ma zana mata akayi,Red jambaki tasa nan Salma ta kara kyau sosai,daurin dankwali kuwa dama Salma ta iya iri iri kamar gogoro itama dai yanzun bata San ta iya ba kawai ta Nada abinta da yadin gogoro baki gashinta ta fito dashi ta tsakiyar daurin ya zubo a bayansa, takalmi me dan tsini kadan tasa baki shima jaka baka,sai ta rike dankwalin lace din a hannunta,Salma abar kallo ce yau yanda tayi kyau har ya wuce tunani,turaruka ta fesa kala Uku masu dadi,hannun yasha lalle ko wacce kawa tazo sai ta saki baki tana kallon baiwar kyau irin na Salma gashin wani ya kwanto a goshinta me santsi.
Yan matan ma na jiya duk sunyi wanka sun yi kwalliya sunyi kyau abinsu wanda basu zo jiya ba duk sun ci wanka sunzo har ma da wanda ba a gayyata ba,gasu dama Fulani ne suna da kyansu ba munana,yanzu kuma sabo da kallo a TV da waya phone har kauye ma suna wayewa,sai kaga wasu ma sunfi Na birni, Jamila tace Salma kinyi kyau yasin,Salma tace na gode,yau Ango zai sha kallo dama gashi shima me kyau ke kam kinyi dace,Barira tace ke dai bari Allah samu a danshinku,Zahra'u tace Inye Amarya ta Ango ansha kamshi yau dai zaiga yanda za a Mike masa a gado heeeeeee suka saki shewa da guda,su kadai yan matan nan sai da suka sa bangaren Amarya ya koma abin nishadi ayi ta Shan dariya ana hira iri iri,kai kace bikin yar Asalin garince,kowa yasan mutan kauye akwai shishigi watarana,akwai kara da rufawa mutum asiri idan hakan ya taso musamman akace harkar aure ce,har uba sai ayi maka da wani a kauye ba ko sisi kuma a daura bako daga zuwa duk sunayi.

10:30 dai sai ga zainura cikin lace itama tace Amarya bani tukwici,Salma tace fada min sai na baki an daura aure wlh yanzu Sadakin ki Dubu Hamsim Ango ya bayar,sai guda yiriri yan matan,Salma ta bawa Zainura Dari biyu tukwici,nan ma sai shewa,Zainura tace ki godewa Allah Salma ki kara daga hannu ki godewa rabbul samawati Wal ardi Angonki ke ina jin kaf duniya ba kamarsa a kyau,wlh kamar Aljani,ya haske garin nan gaba daya wani wal,kin San sai dana ga kwakwaf,kayanku iri nasa nasa shadda ce yasa yar Ubansu keeeeeeee yau nasha kallo.

Zainab da itama shigowarta kenan tace kan uba kuje kuga Bature a inda yake Salma yar India ce Amma billahillazi huwarrahamanu Bature yana waje ta daki cinya tace an gama daku baku Sha kallo ba,ke kinga jama'a kamar me ke nayi Imani kaf garin nan ba a taba daurin aure me mutanen naku ba Salma harfa na wasu kauyukan,ga motoci,kun San Malam Akwai mutane masu kudi,Zainab ta kalli Salma dake murmushi tace Salma ya kamata kiyi kukan dadi yau duk sabo daku aka taru ikon Allah bako yafi dan gari,dama Zainab badai yabo magana ba.

Zainab har tayi shuru ta kara mikewa tace duk Ku saurara min kuji ai ni yau ba abinda yafi birgeni irin tafiyar da Ango yakeyi yau na kare masa kallo,Jamila tace dan Allah? Zainab tace na rantse da Allan daya halicceni ya halicci tsohuwata da tsoho na,ga Zainura tambayeta kiji,dan Allah zainura ya yake tafiyarsa,nan Zainura ta Mike tana gwada tafiyar Na'im yana basarwa a nutse cike da gadara da takama yana Isa da takama kamar dan Sarki,Salma ta dinga dariya ganin exertly Zainura ta gwada yanda yakeyi kuma hakane.
Zainab tace Zainura basu kala ya yake magana fisabilillah? Nan Zainura ta kara mikewa ta shiga tsakiya tare da dan Yafito Salma a hankali tana dauke kai tana wani basarwa,Salma ta sheke da dariya,Zainura ta duba wrist dinta wai yanda yake kallon agogo,ta make murya a hankali tare da lumshe ido ta shanyesu sosai kamar me jin bacci wai irin na Na'im sannan tace sai yayane kana zuwa min yanzu?,muryar ma saida ta lalata hausar yanda Na'im ke yi sabo da har yau yana magana zaka San ba a kasar nan yake ba hausarsa still bata fita duk kuwa da cewa yanzu ya iya sosai sai dai yanda yake karya words kamar zaiyi turanci,
Zainura taci gaba ta dage gira daya tace ya fa?Mena irin wannan abi haka,kasan Salmaaana tana jirani,wai har yanda taji yace Salma ba normal Salma ba Salmaaa ..sannan yasa na karshe.

Dariya suke Sha sosai domin Zainura baiwace da ita ta iya gwada komai da wani yakeyi indai ta gani ko taji to sai ta iya irinsa haka Allah yayita da abirni take da ta Zama wani abu,amma kauye iya Secondary ake barinsu wasu ma jss3 wasu ma basa yi dan ma yanzu kai ya waye kusan ko wanne kauye akwai makaranta kuma ana zuwa ai an rage.
Suna hira sai ga kiran Na'im a wayar Rahina,da wuri ta mikawa Salma ta dauka,suna tare lfy lfy da Salma suna wasa da dariya sai suka ga Salma ta koma kalar Kuka da shagwaba kamar ka tabata ta rushe da kuka, Cike da shagwaba tace Hello,Na'im cikin muryarsa me dadi ya tambaya lfy dai? Salma tace na gaji ni...kiyi hakuri ai an kusa gamawa kinji yana lallabata tace Ni...ni...Allah kazo to,yace ok ai zanzo yanzu karfa kiyi kuka,fada miki zanyi an daura aure lfy,Salma kamar bata sani ba ta nuna farin ciki tace Alhmdllh,sai ta tuno ta taba Raka Umma gidan biki taji irin adduar da tayi,sai ko ta fara shekowa Na'im addua Allah ya Sanya alkhairi,Allah ya bada zaman lfy,ya bada rai da lfy tare da Nisan kwana me amfani,Allah yasa lfy aka yiwa,Allah ya bada ikon sauke hakkokin Allah,Allah ya kawo kazantar daki musha suna hhhh kunji fa readers ita Salma bata San ma me ake nufi ba kawai dan taji Umma tayi itama tayiwa Na'im amma kuma adduarta tayi kyau.

Na'im kuwa Ameen Ameen yake ta amsawa,shima nan ya sheko tasa Allah bada zaman lfy,Allah baki ikon yi min biyayya,ki sauke hakkokin ki kaf tunda ai haka Malam yace ko?tace ae Ameen,Yace Allah yasa yi nayi bari na bari ai dai kinji me gari ya fada tace hakane Ameen,Me gari yace shinfidar miji idan nace kizo ai kizo ko?yes cewar Salma yace to Allah yasa kizo din,Umma tayi nasiha kan saduwar aure duk basu San me take nufi ba,Na'im yace Allah bamu ikon Saduwa tace Ameen Ameen,yace ki shirya gamu nan zamuzo za ayi pics da video sosai, tace ok ya kashe wayar.

Mintuna kadan sai ga Angwaye sun kai kusan su ashirin duk samari sunyi kyau,Nan aka fara kashe pics da video Camera Man da Anty Rukayya ta kawo yana aikinsa wani kuma ya karbi wayar Na'im yana ta yi musu masu kyau,Salma har Selfie ita da Ango sukayi kala kala,Ango ansha kyau sai kamshi same color da na Salma duk shirin Anty Rukayya ne,Nan Umma ta aiko Rukayya da wasu aka kawo abincin Amare da angwaye Jullof rice tasha nama ko ina nama ne a ciki da vegetables iri iri,sai kuma Alkubus da miya dasu waina,harda zobo da kunun Aya,nan ma ana ci ana pics da video harda video,yan mata da samari sai hira akeyi ana nishadi,Ango da Amarya plate dinsu daya,wani kallon idan Na'im yana yiwa Salma to ba Salma ba har wanda ya gani sai yaji kunya,amma ko a jikinsa shi Bai ma San yanayi ba.

Nan Jamila tace gaskiya wannan rana ya kamata Ango ya bawa Amarya abinci a baki itama ta bashi,Ana ta dariya eh gaskiya hakane cewar sauran,nan Na'im yasa spoon ya ebo ya kai bakin Salma,ta bude bakin zata karba ya janye Spoon din sai dariya Yeee,ya kara kawowa ta gama bayarwa yanzu zai bata ya janye da sauri ta riko hannunsa ta karfi ta cinye,ana ta dariya da tafi raf raf, Salma ta ciko spoon tab da katon Nama Na'im da niyar ya dan ci dai dai bakinsa ya bar mata sauran a spoon ai kuwa ta tura masa du bakinsa ya cika taf,nan ma sai dariya da tafi haka ya cinye da kyar.

Bayan sun gama cin abinci suka ce azo a tafi gaida Umma da dangin Malam,nan Samarin kaf da yan matan suka jero a hanya ana ta rangaji ko wanne da hirar da suke wasu mazan da mata,wasu matan da mata,wasu mazan ma da maza,gwanin sha'awa,ana ta kallonsu a garin ko bako yazo yasan ana biki,Na'im da Amarya Salma ya rike mata hannu ana ta video cov fa ba a gajiya,har Gidan Umma nan mata manya da suka cika gida yan biki suka fara guda ana tsokanar Amarya da Angonta,suka gaishesu Salma taje wajen Umma ta jawota tana dariya tace Umma tun jiya ban ganki ba,Ina Malam fa? Umma tayi dariya tare da cewa ai yanzu kin samu mutumin naki sai da yaje ya taho dake zaki zo,Salma tace Allah a'a Umma,kin dai ci abinci ko?ae naci,Muhd fa? Shima yaci da yawa,aka fara hotuna da dangin Umma dana Malam,Umma Na'im da Salma suna ta daukan pics ,Anty Rukayya ma da kawayenta yan Birni ana ta sambada hotuna,Abubakar ya nemo Malam suka hadu,Malam,Umma,Ango da Amarya sai pics ake musu da video cov abin Shar ko masu iyaye ba kowa zai samu haka ba.
Chapter 32 · 0% Book details