← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 80

Sashe 5

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar su Affa suka lallabesu suka yarda Salma ta zauna wajensu shima hakan sai da suka fada musu gaskiyar Aljanun da ke tare da Salma sannan suka amince badan Ransu yaso ba.
Bayan su Affa sun koma Hanyar Abuja Rigarsu da kwana 3 Salma ta fara fuskantar tsangwama kyama da cin mutunci wajen danginta domin sunce ba wani Aljanu,
Salma kullum sai aikin laulayin itace kwadayi,amai,da tara yawu ita kanta abin ya isheta kuma Raheel Bai kara zuwa ba ko a mafarki,yan kudin hannunta duk ta cinyesu a cikinta,wani tsoho dan Uwansu Malamin makarantar allo shi kadai yake tausayawa Salma,malam musa yana da dansa Babba Hashim wanda akayi bikinsa a satin nan.
Hashim dai irin Gabon nan ne wanda Bai waye ba sam,Makarantar Allo ta ratsashi gaba da baya, Salma tayi ta tsokanarsa suna fada basa shiri da Salma,yau aka kawo masa Amaryarsa Maimuna

Maimuna itama bata wayeba bata San komai ba gata yarinya karama,Dan haka Hashim ana rakashi dakin Amarya bayan ya Raka abokai sai gashi ya shigowa Amarya da Lemo Viju kawai guda daya tal sabo da tsumulmula wajensa ba a magana,
Amarya taga iya Viju tace kai Hashim Viju kawai duk kudin da ka nuna a bikin nan har karuwai ka ebo a wajen biki aka Sha party dasu amma Viju,Hashim ya rike haba yace Ke ko kunyar Amare babu Muna,dalla in baza ki Sha ba bani abina nan take ya fisge Viju ya kafa baki ya kwankwade abinsa tare da cewa gobe zan siyo miki kifi karfasa,ko sallah babu bare a sake wanka yace kwance Zanin mana Maimuna,
kafada ta makale wai taki,washe baki yayi yace haba Muna ta,Maimuna taki yarda abin ya bashi haushi kawai ya kwance tazuge tare da Zaro zarmakekiyar Hajiya Babbarsa ya bata rai ba mutunci ya mikawa Maimuna yace ungo ni,tayi banza dashi,yace kina bata min lokaci karbi mana,Maimuna a tsorace ta karba kamar ta damko tsumma ta kalli Hashim zatayi kuka ya bata rai sosai yace karki mun kuka maza Sa a taki ,
Kuka wiwi Maimuna ta fara taki yin komai haushi da takaici ya kama Hashim ya fisge abarsa da karfi yace bani kayata,Maimuna budar bakinta tace kayi a hankali kar dai ka yagata
Harara Hashim ya gasa mata,sannan ya kara Cuna mata ita kamar dodo yace muna taba mana,Maimuna tace Bazan taba ba wlh Allah ta furta tare da dauke kanta,
Dan kafadarta ya buga ta juyo kuwa ya kara cewa Muna taba,ta make kafada Bazan taba ba,Muna taba,bazan taba ba haka suke ta faman yi,sai da ya gaji ya faki idon Muna ya taba mata Boobs ya fice da gudu ya koma palo,nan Maimuna ta fashe da kuka tana ta Allah ya isanta dan Iska shege kuma sai na kaiwa Malam Babanka kara,Yana daga palo yace ki kai karata wlh na daka ki a gidan nan,Muna tace humm uhm kama Isa wlh baka Isa ba,yana dai a palo ya kwallo da karfi yace wullu na dai taba ai komai wayon Amarya sai an kwashi romonta,Muna tace sai dai kasha romon Kaza wlh Danni ba yar iska bace,da nasan hakane wlh Bazan aure yanzu ba,Wlh Baffa ya cuceni dama haka akeyi sukayi mini aure sai kuwa ta rushe da kuka,Hashim ya kyalkyale da dariya yace au....au....au...kuji banza tun ba ayi komai ba to me akayi,wlh ki jirani duk ranar da na kamaki sai na karyaki yanda zan shillaki sama da hannu daya sai na nunawa Allah ke sannan na nanaki saman gado na wargajeki zakiyi me dalili ne,Muna na kuka tace Allah zai saka min.

Salma ce a tsakar gida take bakin pampo tana ta faman kyara Amai kamar zata mutu ga mutane a gidan kowa na harkokinsa ba wanda yace mata ci kanki,haka ta gama ta lallaba ta koma saman tabarma ta sharbe a Cikin rana tana tofar da yawu.
Still Salma bata iya Sallah sai taga dama ta jefi jefi duk yanda taso yi baza ta iya ba,tana jin haushin Raheel ta wannan fanni.Yanzu kam tasan tana da Aljanu Amma kamar karya take gani Raheel bafa Aljani bane.

AsmaBaffa
[1/14, 5:10 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉

16-20 21-25

Official

By
AsmaBaffa

Na'im ne zaune shida frnd dinsa wata Zahiyya tana palonsu kusa dashi,Zahiyya dai yar gidan wani Gomna ce tana ji da kanta sabo da me kyau ce ga Naira,sabo da sai abinda taga dama takeyi a duniya Iyayenta sun yarje mata itace yawo kasa kasa gidan Frnds mata da maza,a wani Seminar suka hadu da Na'im ta nace masa dole suka kulla kawance duk kuwa da yanda yake wulakanta ta,

Yanzu ma tana gefensa ko kallo bata ishesa, Irfan ne ya shigo cikin shiga ta Alfarma yasha Suit kamar a jikinsa aka dinka, ko Sallama baiyi ba sai Hi guys kawai yace,Na'im cikin wata dakakkiyar Farar shadda fitted dinki na maza, da gwarancinsa yace kana so ka koma ayi mini Sallama kana iya mantu'a(ka koma kayi mana Sallama ka manta)

Harara Irfan Ya watsa masa tare da cewa dan giya kawai kai wani na Allah ne?zaka dinga raina mana hankali,
Wata Beer Irfan Ya mikawa Na'im yace ga favourite naka a wani shopping mall na gani nasan kana son irinta,murmushin Jin dadi Na'im yayi ya karba tare da cewa thanks Bro kamar kasa shi zan fita nema,(kamar kasan shi zan fita nema)

Zahiyya tayi murmushi tare da tsoma baki tace nima ina Shanta a sanmin wai dan su gane itama shegiya ce ta waye a duniya,
Wani kallon Banza Irfan Ya zuba mata yace amma kinji kunya kina mace me daraja Allah shirya,
Na'im ne yayi magana cike da takama shut up Irfan let's her be,tayi abinda tana sho rayuwa nata ne (tayi abinda takeso rayuwarta ne).

Zahiyya tayi shuru shi kanshi Na'im din baya Saurarar inda take sam,game ma suka kunna suka farayi ba ji ba gani sabo da Mummy tana can gidan Dada mahaifiyarta sai dare zata dawo.
Zahiyya taga yanda take wulakanta maza anan wajen su Na'im ko kallo bata ishesu ba,Irfan Juice yake korawa suna game while Na'im yana kora Beer nasa,Zahiyya bata daddara ba ta wani dafa kafadar Na'im tana murzawa a hankali wai tana supporting nasa a game ai kuwa nan take taji an mata wani mahaukacin iba an watsata saman kujera saida Na'im da Irfan suka kalleta amma basu kawo komai ba tunanunsu ita tayi hakan da kanta.
Ita kuwa a ranta tace wulakancin har ya kai Na'im ya kwasheta ya watsar haka nan take ta Mike cikin fushi ko Sallama bata musu ba ta wuce gida Driver dinta yaja ta.

Salma fa ana Jin jiki an karmashe ta kara wani fari kwal,sai tsantsan wahala da take Sha wanda danginta kaf babu wanda ke bi ta kanta sai ma zagi,da kyar ake bata abinci ma,Matar kanin Babanta ce Umma Hani ta fito fuuu tare da fisge kwanon da Salma ke cin shinkafa ta zubar da ragowar shinkafar ta dungurewa Salma kai tare da dukanta a kai tana annamimiya karuwa r banza ni nace kiyi cikin shege matsiyaciya, ubanki ne ya siya min kwanon?jaka kawai,Salma ta saka kuka ita takaicinta shinkafa da manjan take so shi take sha'awa matar Hashim Amarya ita ta zuba mata gashi ko rabi bata ci ba Umma Hani ta zubar mata,
Umma Hani sai zagin iyayen Salma da suka rasu takeyi,Salma tana kuka Lfy normal kawai sai hawayen ya koma jini,Hawayen jini kawai ke tsiyaya idonta jajir ta Mike ta shaki wuyan Umma Hani tayi jifa da ita kamar ta jefar da tsinke,haka kafin mutane suzo Salma ta tayi kasa kasa da Umma Hani ta Sume a kasa sannan Hawayenta ya koma Normal na ruwa,
Kanin Babanta Shehu na shigowa ya kama Salma da duka ba ji ba gani sai da ya farfasa mata jiki da bulala wai tana sani ta daki matarsa,Umma Hani murna kamar me,mutanen gidan da makwafta da kyar suka bashi hakuri,amma cewa yayi sai ta bar musu gida, Malam musa baban Hashim ne yasa baki sannan suka kyale Salma taci gaba da Zama.
Salma ta rasa abinda ke mata dadi a duniya,Raheel da yake fito mata a suffer mutum ya sa mata sonsa da gaske sonsa takeyi bata ganin sa shine damuwarta,

Da tsakar dare Shehu da matarsa Umma Hani suka ji ana ta dukansu baji ba gani mahaukacin duka ake musu basa ganin me dukan nasu,ji sukeyi kamar da bulalar wuta ake Zane su,ihu sukeyi da kururuwa mutane da yan Uwa aka cika a gidan da dare ana ganinsu suna ta faman rawar banjo da ihu,
Sai da suma aka farfasa musu jiki sannan suka ji dukan ya tafi an daina dukansu.

Salma abin mamakin yanzu kuma kullum sai ta tayar da Aljanu kwana takeyi ihu da burburwa,watarana kuma sai dai a tsinto ta cikin bola tana tsince tsince ga cikinta ya fito ya girma.
Akwai wani Matashi a unguwar dake matukar son Salma da aure,shi yace ko a gidan karuwai ya ganta indai ta yarda sai ya aureta,ba ruwansa da wani cikin dake jikinta zai ma fara zuwa zance.
Kamar wasa ranar Salma na zaune ita kadai a wani akurkin dakinta kawai aka turo wai tazo inji Salahu, dama tasanshi yana da shago duk abinda taje siya kyauta yake bata,fita tayi kofar gida ta hangosu shi da abokinsa,

Da fara'a ta karasa suka gaisa,Salahu ya gabatar da kansa a matsayin yana son Salma,suna ta hira yana ta Surutu Bai San kafar Salma ta koma ta Doki Horse ba,Sai abokinsa ne ya kalli kafarta ya ganta ta Doki ce,tsoro ya kamashi ya firgita ya fara ja da baya,yana tafiya sadaf sadaf a hankali,Salahu yana Umaru wai me kakeyi haka ne?kafiyarka kuwa Umaru?
Ka tsaya mana haba Umaru,Umaru dai ko tari baiyi ba jikinsa ne yake rawa yana tafiya da baya baya a hankali sai da yayi nisa dasu Salma sannan ya kwalawa Salahu magana da karfi yace Kalliiiii ......kafarta......da....kofat...sai ya fadi ya Sume a wajen.(kalli kafarta da Kofato zai ce sai ya makale yace kofat ya Sume).

Salahu da gudu ya tafi wajensa Salma ta koma gida da zazzabi nan take ta fara aljanunta ba ji ba gani,Shi kuwa Umaru da kyar ya farfado ya Sanarwa Salahu suka fece da gudu.
Chapter 5 · 0% Book details