← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 80

Sashe 43

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na'im yana wa Salma magana amma ko daya da kyar take amsa masa sabo da kunyarsa da takeji,shi mamaki yake kamar ba Salma daya sani ta Raheel ba,wanka ma tayi a part dinsa guduwa tayi Bedroom nata wai kar Mummy ta ganta ta kwana wajen Na'im.
Bayan ya hade cikin suit fara Kal kamar a jikinsa aka dinka,wandon pencil yasha kyau,gaba daya turawan dake Embassy ne zasu zo yi masa murnar bayyana,haka Doctors na hospital nasa,da managers na companies nasu duk sunzo anyi musu masauki a palon Mummy suyi mata murna, Mummy ce ta fito cikin shiga ta Alfarma haka su Irfan ma gaba daya an gaisa sun musu murna,Na'im room din Salma ya shiga ya tadda ta hade cikin wani arnen material nata tana fesa turare, ta mudubi suka hada Ido kafin tayi wani tunani taji ya rungumo hips dinta tare da juyo ta suna facing juna,nan tayi kasa da kanta,Hannu yasa ya dago habarta yana kallonta da mayun idonsa cikin salo ya daura lips dinsa saman nata,tuni ta lumshe ido tare da zura hannayenta ta kankameshi suka fara hot kisses abin ba a magana sai da suka gaji ya saketa suna maida numfashi tare da sakarwa juna murmushi,kunya tasa tayi kasa da kanta tana murza yatsunta tana murmushi,mayen nata kuwa tuni idonsa yayi Jajir da kyar yake daurewa,hannunta ya rike tare da furta let's go mu suke jira sauri suke.

suna fita taga mutane da yawa bakake da farare,suka gaisa cikin harshen turanci suka musu murna,Na'im ya gabatar musu da Salma matarsa ce sunyi mamakin kyanta suna tayashi murna sannan suka tafi wajen aikinsu shima yace idan ya huta zai dawo
Breakfast tuni an shirya shi,Zainura tana can tayi wanka ta gama komai Aisha tana faman kwalliya,Zainura tace dole sai ta bata aron kaya in ba haka ba wlh ta kala mata sharri wajen Mummy,Aisha tace kayana zaki sa na baki na karba na sa again sai dai na bar miki du,Zainura tace ae naji bani din,Nan Aisha tace Mayya tare da bude akwatina ta zabo duk wanda suka mata kadan wasu sun dameta daf ta zubosu wajen kala goma ta watsawa Zainura,Zainura ta kwashe ta zabi wata Atamfa riga da skert ta cika su tab dinkin yan gayu tayi kyau kamar ba ita ba,tace to Alhmdllh ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba,Aisha dai tana jinta sai habaici Zainura take mata har ta bar dakin ta fito Palo,kowa ya hallara ana cin abinci,Malam yana can da Umma an kai musu nasu sabo da su sake sosai,Mummy ma tana can wajensu,Zainura tana zuwa taga plate din Salma da Na'im daban tace kai Ku hade shi waje daya a kauye tare kuke ci a plate daya,har ruwa Kofi daya kuke daukowa,Koko ma haka,Na'im ya zaro Ido yace Koko?tace ae Kamu Kamu wai dan ya gane tace to Kofi daya ake zuba muku,Su Irfan suka dinga dariya,Hunaif yace ah kace Koko ne a cikinka, Salma tace dan Allah Zainura da gaske kike?

Zainura tace bari Ku tuna Memory dinku zaku fada,Irfan ta kalla yasha wanka kamar me shirin zuwa party kusa dashi ta zauna tare da kallonsa tace Yasin kamar Ku daya da me kyau kawai,Hunaif yace nifa Baby?Zainura tana dariya tace Alquran kai kam hancinka kamar birona da nake rubutu,bakinka kamar yar ficika,komai naka Siri Siri jikinka kamar raken dan Isiya a kauyenmu,Hunaif dariya ta kamashi wai sugar cane yarinyar take nufi wlh sai nayi maganinta,Irfan yana taunar chewgum dinsa Zainura ta dinga rokonsa sai ya San mata tayi musu Kas Kas,Yace sai dai na bakina,Allah kiyasheni sai kace me kyau da Salma sune yan Jam'iyar kuss (kiss) yake ko me?
Hunaif yace kinyi kyau yau Zainura Ashe dai kina da kyau kema?Zainura ta harde kafa tana yarfe hannu yanda Aisha keyi tare da makale murya ta koma ta yan gayu tace sabo ma kake Man na fi shakira mawakiya,Na'im yace wai ni kam bakya gajiya da surutu? Zainura tace Salmanka ta fini surutu sanda kuna kauye Wlh zanceka takeyi yanzu kalleta sai tayi shuru dan kuturin munafunci billahillazi kai kake wani daga mata kafa wai ita kinibibi gidan Suruka,in kaga rashin kunyar da take tafkawa a kanka sai kayi Salati,Itafa ta Zama namiji kaine macen a kauye,har rawa take maka Allah ya tsinewa me karya wlh sabo da rashin kunyar ta Malam ya muku aure idan karya nake na nutse a nan,ko ka bari Malam ya fito kaji.

Na'im dadi ya kamashi yace na tambayeta munyi iskanci tace bata sani ba,Zainura ta saki Salati tace to Alquran Iskancin da kukayi yaci ace an fada a taskar labarai,billahillazi a gabanmu ma kunsha yi kafin aure amma da kukayi aure shine kuka koma yin Sunnah,sunnah ake cewa masu aure amma iskanci ko a birni babu kamarku,Salma ta rufe ido kunya ta kamata tace Zainura banda sharri.

Zainura ta Mike tsaye tace bari Malam ya fito ya bani aron wayarsa na kira Rahina da Zainab dasu Barira kuji yanda abinda yake amma fa karku bari Su Mummy suji,Hunaif yace ai iya mu kawai za ayi,Irfan yace ga tawa wayar kira,aiko Zainura ta hadaddace Numbers da dama,nan ta kira wayar Rahina tare da cewa sa min ita a handsfree kowa yaji,Na'im sai murna yake dama ace ya tuno irin dadin da yaji wayyoooo da ya huta,bugu daya karaf Rahina ta daga da Sallama.

Zainura ta tsaya a tsakiya tace Rahina ba gaisheki na bugo nayi ba domin ni yanzu Allah yayi min Baiwa da wayar dan Bature nake kiranki yanzu haka ina cikin daula,Rahina ta sheke da dariya tace Zainura shegiya ya kike,tace da Allah ki adana gaisuwarki sai na dawo kawai mayi irinta, tambaya zan miki tsakani da Allah,ranar da muke Kamun Salma karfe nawa takai wajen Saurayinta kafin ta zo? Rahina tace ai ta kai wajen shabiyu na dare suna daki tare wai yana bata abinci a baki tare da sauran Runguma ta yan Birni,Su Na'im suka fara dariya harda Salma,Zainura tace a saurara Alhmdllh,da ta kirashi a waya me yace mata idan an kai masa ita?
Rahina tana dariya ita da Abubakar tace yace idan an kaita wacce kwanciya zata masa,tace wacce yake so,yace to kar ta lankwashe masa ko wanne joint,Zainura tace Alhmdllh da sunayi wayar tace ya sata bacci me suka dinga yi? Rahina tace kiss iri iri wlh nima har Darasi na dauka,kit Zainura ta kashe wayar,Na'im harda tafawa kansa tare da kallon Salma da take ta dariya tana rufe fuska da gyalenta yace uhmmm Ashe soyayya muka Sha haka?

Zainura tace tafi soyayya ma,nan ta kira Zainab,Zainab cikin muryarta me karfi tace Hallo ya naji kamar Zainura wai? Ke dan uwarki kiyi magana mana Zainura kin San wayar nan kashe kanta takeyi fa,Sadisu yaki canja min wata matsiyaci, Zainura tace Zainab a gaida da kowa ni kam ina cikin Jin dadin duniya,tambaya ce nasan ke kadai zaki iya fadan komai ba kunya,Zainab tace hhhh yo kema kin San mu ina ruwanmu tsage gaskiya muke ko ta mutu ko tayi rai,
Hunaif jin Muryar Zainab ta shegun kauye ya dinga dariya ma,Zainura tace kin taba ganin Salma tayiwa Me kyau Rawa? Da karfi Zainab ta Dafe Kirji tace kutmar wannan yan Iskan da ba ruwa a idonsu wannan murgude murgudene batayi masa ba,ke ai na Rantse da Allah Salma ta kusa kashe baturen nan da salonta,Na'im yace wow hhh yana dariya su Irfan ma haka,Zainab tace Zainura dan Allah ya ranar daura auren nan muna kallo bayin Allah kiri kiri suka makure juna a lungu,sanda muna zuwa gidanta dan Allah wanne kalar ihu ne bama jinsu ta dakinsu,bare Runguma da kiss ai kamar tuwo haka suka daukeshi,kin tuna ranar da muka kai dare a gidansu mutumin nan kiri kiri ya dinga hararar mu mun rike masa Salma,da ya gaji ba zuwa yayi ya sureta kamar ya dauki buhun Omo wani cilll ya cillata sama yayi ciki da ita.

Zainura tace to anan sai wani munafunci take ta sabawa bawan Allah da soyayya amma zata fake da Memory ya goge,shi ya akayi yake so gashi nan gwara tsohon gwauro dashi wai ba memory tana ta gudunsa sai kiga tayi mukus a gefe kamar yar Iska yanzu haka ta koma.
Zainab ta saki Salati tare da cewa ke ki Bari dan Manzo kuji yar bantan uba tace ga Barira a kusa hadasu da Salma ta ladaftar da ita da kalamai.
Nan aka bawa Salma waya Zainab ma ta bawa Barira,Barira tace Salma? Salma tana murmushi da kyar tace Na'am bata iya sanin su waye wasu Barira ba,Barira tace ke dan Ubanki mu ba ruwanmu da Memory ya goge gwara ki saki jiki,aure ba wayar Salula bane zaki ce baya daukan wakoki ba memory, me yasa kike haka? Har zuwa muke kallon soyayyarku wlh wata zata kwace miki mijinki kina biyewa Memory ya goge,ai ance tun farko kuna son juna kuma kun tuna baya me yasa baza ki dawo da son baya ba da kika tuna Ku ci gaba kina ji kina gani wlh zai nemo wata dama ga kudi ga kyau yan matan birni ne zasuyi rubibinsa ya dauko daya ciki ko biyu ma kina haukar banza,wannan mijin naki to mu dai mun San son Iskanci ne dashi wlh idan baki nutsu ba wata zata janye shi,haka Barira ta dinga masifa kamar Salma yarta ce hhh wai akan ta girmesu da 4mnths shine komai su Zainura sai suce itace Babba ita zatayi fadan manya.

Salma dai ta gama ji tace to na gode zan gyara sukayi Sallama sai Salma ta fara Hawaye wai ta tuno Na'im da yana kula mata da yawa suna Romancing yanzu ma Barira ta tuna mata lallai zai kawo su kuwa,ta shiga uku ita,Zainura ta kyalkyale da dariya tace Me kyau ni zan dinga rakaka zance,Salma ta tunzura ta harari Zainura,Zainura tace dauko Album da wayar da CD a sa kowa ya gani wlh , Na'im yace sai jibi bashi da time.
Chapter 43 · 0% Book details