← Book details Kamar Da Wasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 67

Sashe 56

Kamar Da Wasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shifa yagama lura da Bilkisu yanzu akusa take abu kadan ke bata mata rai tayita surfa masifa, baice komai ba yabar maganar sai da yakai 12 adakinta suna zaman kurame sannan yatashi yakoma dakin husnah,washe gari tunda sassafe Bilkisu ta tashi ta shirya saboda ankirata awaya wai Hindu ta haihu ansamu mace amma suna asibiti saboda yarinyar ba lafiya ansakata cikin kwalba, ganin shiru ango bai fitoba yasata kiranshi awaya amma wayar akashe, tsaki taja ta dauki handbag dinta tafita falo daidai lokacin shikuma yafito daga dakin husnah,

"Ya naganki haka? Lafiya?"

Batare da ta kalleshi ba tace,

"Asibiti zanje Hindu ce ta haihu"

"Masha Allah, Allah yaraya.... Zan kaiki ne?"

"A'a kayi zamanka zan hau napep" tafada ciki ciki saboda harga Allah haushin fahad takeji irin karshen nan,

Adawo lafiya yayi mata bata kulaba tafice bayan ta rufe dakinta,husnah dake tsaye bakin kofa duk abinda yafaru tana ji, komawa dakin husnah yayi nan suka bude babin soyayya wato ansamu dama tunda Bilkisu bata nan shine yau ake baja kolin soyayya. Tunda Bilkisu tabar gidan bata dawo ba sai dare saboda a asibitin suka wuni gaba dayansu,lokacin da tashigo gidan suna falo zaune suna kallo yayi pillow da cinyar husnah amma ganin Bilkisu sai yatashi zaune suna yimata sannu da zuwa ciki ciki ta amsa daga haka tawuce bedroom nan yatashi yabita ciki, bata kalleshi ba ta shiga rage kayan jikinta tana amsa masa tambayar da yake yimata wai ya tabaro masu jiki? Toilet tawuce taje tayi wanka tazo ta kwanta kasancewar tayi zirga zirga yau babu bata lokaci bacci ya dauketa bata ma san lokacin da fahad yazo yimata saida safe ba. Tun daga ranar bata wuni agida acan asibiti take wuni tun safe idan tatafi sai dare,ranar da kwanakin da zaiyi adakin husnah suka kare zai koma dakin bilkisu yaga ikon Allah kasancewar yajima adakin husnah bai fito ba lokacin da yashiga dakin Bilkisu wata uwar harara tarinka zuga masa shi dai baice komai ba katifa ma ya shinfida akasa bai nemi hawa gadonba duk da yasan idan yayi niyya bata isa hanashi ba, bedsheet yaciro sabo daga cikin kayanta nan ta harareshi,

"Malam ajiye min kayana.... Ita matar taka bata baka nataba?"

Ajiye mata yayi yafita zuwa dakin husnah mintuna kadan sai gashi yadawo dauke da Sabon bedsheet harda bargo hakanne yasake kular da ita shiyasa bacci sai sama sama tayi abinda bata saniba shine shi har lokacin ma babu abinda yashiga tsakaninsa da husnah saboda tun ranar da aka kawota acikin period take kuma irin matannan ne masu yawan kwanaki gashi dadin dadawa baya son mai afkuwa ta afku Bilkisu tana nan yafi son sai bata nan sai ya sha angoncinsa hankali kwance, wannan dalilinne yasa lokacin da tace masa agidan Hindu zata kwana ana igobe suna bai hanaba saboda daren ranar ango yake,Bilkisu kam ana can gidan mai jego anata shirye shiryen suna tama manta da rayuwar wata aba wai ita husnah amma abinda yake daure mata kai shine tana yawaita tunanin fahad haka kawai sai taji yafado mata arai. Kamar yadda ya tsara adaren ranar yasamu kasancewa da husna, duk da ta nuna jarumta da daurewa amma hakan bai hanata jigatuwa shiyasa kwana tayi tana yimasa raki abangarensa shikam ya godewa Allah sannan yasake bawa husnah wani gurbi mai girma acikin zuciyarsa saboda yasameta cikskkiyar budurwa wacce kowanne da namiji ke fatan samu. Da safe suna kwance tayi pillow da kirjinsa sai faman rarrashinta yaketa yi yana lallabata yaji kiran Bilkisu yasan maganar dinkice wadda yayi mata wannan dinma da fada da masifa tayarda zaiyi mata amma da wai shagon wasu zata kai ayi mata tareda su maama shikuma yace bai san maganarba idan bazata bari ya dinka mata ba sai dai ta hakura da dinkin gaba daya, ganin yakafe yasata bashi atamfa guda daya daga cikin lefenta shine ya dinka, daga wayar yayi idanuwanshi alumshe,

"Bilkisu... Ya akayi?"

Tun daga yanayin da taji yayi magana tagane akwai abinda suke yi, tsaki taja acikin zuciyarta tana cewa "kwa karaci iskancinku dama ai ba yau aka faraba"

"Ranki yadade ke nake sauraro....."

"Baka yimin dinkin bane?"

"Nayi mana, inkawo miki?"

"Idan baka kawo minba to da waye zai kawo?"

"Yi hakuri bari inkawo miki yanzu" yafada cikin sanyin murya sakamakon jin husna tana tsokanoshi, katse wayar Bilkisu tayi tana tsaki, kallon husnah fahad yayi sannan yashafa kanta,

"Bari naje na kaiwa antynki dinkinta da nayi mata..."

Makale kafada tayi,

"Ni kadai kuma zaka bari?"

Mikewa tsaye yayi yana cewa,

"To ko zaki rakani mu tafi tare?"

Daga masa kai tayi tana bata fuska,

"Sorry yanzu zan dawo.....ai bazaki iya fitaba... Keda naga kina tafiya irin ta yan kaciya..." Yafada cikin sigar tsokana, turo masa baki tayi tahau tirje tirjen kafafu akan gadon, kayan jikinsa yasauya daga na shan iska zuwa jeans da t shirt ta polo yadauki p cap yaje gabanta yayi mata kiss sannan yafita, tashi tayi tabi bayansa har zuwa tsakar gida yadauki machine dinsa yafita, saida taga tafiyarsa sannan takoma gida. Lokacin da yaje kofar gidan Hindu Bilkisu nacan suna aikin abincin suna sunata kukkulla alale da dafe dafen abinci,daga ita sai t shirt da bakar skirt ta fita ta yafa mayafi, yana zaune saman roba roba dinsa yabasar, daga nesa lokacin da take fitowa yake kallonta duk sai yaga tadawo masa wata yar yarinya da ita tayi karama, koda ta karaso kasa kallonta yayi saboda gani yake kamar zata fahimci abinda yafaru acikin idanuwanshi, kasa yarinka yi da idanuwanshi har yabata sakon yatafi bai yarda sun hada idoba,sai bayan da yatafi ma sannan yatuna bai tambayi Bilkisu sunan jaririyar ba, nan yakirata awaya amma har tayi tagama bata daukaba yasan tana can tana cikin aiki sai dai fa sosai yau dinnan tayi masa kyau kawai bai furta mata bane, lokacin da yakoma gida cigaba sukayi daga inda suka tsaya shida husnah sunsha amarcinsu sosai kafin Bilkisu tadawo dan sai washe gari tadawo bayan sun gama komai na soye soye da gyare gyaren gida, tunda ta dawo kuma sai fahad ya daukewa husnah diff sam baya yarda suyi wani abu na wasa ko raha afalo sai dai idan acikin dakine, haka suketa rabon kwana kowa kwana biyu girki kuma kowa nasa yakeyi sam basu ma cika haduwa ba saboda kafin husnah tatashi dasafe Bilkisu tabar gidan ta tafi aiki idan kuma tadawo husnah bata fitowa tana daki a kunshe indai kaganta tafito to tare da fahad ne. Haka kwanaki suka cigaba da tafiya dan yanzu wasa wasa su husnah zasu kai sati shida da aure, dan fahad har yakoma makaranta amma satinsa daya yadawo gida weekend, ranar asabar da hantsi saiga nusaiba matar ya Abba yakawota dama bata taba zuwa gidanba,Bilkisu na falo tasha riga da wando masu taushi blue colour tana aiki a system dinta gefe daya kuma tana sauraren malam Aminu daurawa cikin shirinsa na tambaya mabudin ilmi, ranar fahad zai bar dakin husnah yakoma nata amma baya nan tun safe yafita shago saboda yataho da dinkuna sosai daga kd, tarba sosai Bilkisu tayiwa nusaiba har husnah tafito suna dan taba hira ita dai bilkisu jine nata saboda bata fiya hayaniya ba ita saima ka zauna da ita awa guda baifi tayi magana sau ukuba zuwa hudu sai dai dasu Hindu da khulsum kawarta tana sakewa sosai tayi hira dasu,wanka ta tashi taje tayi tashirya cikin doguwar gown ta atamfa tafito,tambayar nusaiba tayi me zata dafa mata tace komai ma, kitchen tashiga ta dora girki doya da vegetables sos bayan tagama ta zubo mata takawo mata, zance ta iskesu sunayi wanda ya dangancin kishi sai taji husnah daga ganinta tana cewa,

"Ai kuwa wallahi idan baka rike mijiba wata ce zata shigo ta rikeshi dakyau... Wasu matan akwai sakaci dan watama hatta abin shinfidar miji bata san ta adana ta alkinta ba sai dai idan yanada wata matar tabashi..."

"Ai mata sha'aninmu sai hakuri kishi yayi mana yawa..." Inji nusaiba, ita Bilkisu sarai tasan da ita husnah take sai dai bata da ajin da zata zauna tayi kace nace da ita, ita da wanda ya ajiyeta zatayi, akule tawuni har nusaiba tatafi amma bata tankawa husnah ba, la'asar liss fahad yadawo bata kulashi ba yayi shirinsa yafita ball, da daddare tana shirin bacci sai gashi yashigo tashi tayi tsaye cikin masifa tace,

"Malam bana bukatar wannan bargon da wannan bedsheet din acikin room dina ka fitar min dashi and you better warn your stupid wife wallahi idan tasake attempting yimin bakar magana ko gugar zana sai ranta yabaci saboda ni ba sa'arta bace..."

Tunda yaji haka yasan akwai abinda yafaru ko kuma husnah tafada mata wani abu, fita yayi yamayar dasu blanket din dakin husnah lokacin ma ita tajima da yin bacci, sake komawa yayi dakin Bilkisu yatarar tafito masa da bedsheet da blanket. Zama yayi saman katifar da scissors a hannunshi wanda zai yanka wasu dinkuna,

"Me husnah tayi miki?" Ya tambayeta yana auna atamfar da yaware,

"Meya hana ita baka tambayeta ba?" Tabashi amsa tana kokarin kwanciya,

"Tayi baccine ai..."

"To sai ka bari sai ranar da tatashi saika tambayeta..."

"Allah yabaki hakuri dai zanyi mata magana insha Allah"
Chapter 56 · 0% Book details