← Book details Kamar Da Wasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 67

Sashe 5

Kamar Da Wasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalaman saleem sune suka sanyayar mishi da zuciya sannan yasashi jin nutsuwa ta saukar masa, cigaba da kwantar masa da hankali saleem yayi har saida yaji acikin ransa zai samu bilkisu, cikeda farin ciki suka rabu da saleem yana tsokanarsa,

"To kai ka isa aurenne?"

Girarshi guda daya ya dage masa yana kallonsa cikeda mamaki,

"Nine ban isa aureba? Kabari abani matar a lokacin zaka fahimci na isa ko ban isaba"

Daga haka yamike yakama hanyar gida yana jin saleem har lokacin yana tsokanarsa amma bai tsayaba.....

© _*HASKE WRITERS ASSO.*_ _(Home of expert & perfect writers)_

*KAMAR DA WASA.....!*

***Hannayensa gaba daya ya aza cikin aljihun wandon bakin jeans din dake jikinsa, jar rigace ajikinsa mai rubutu kamar haka, _All the best_,yana tafe yana kallon dukkan jama'ar da kowa hada hadarsa yakeyi, wayarshi ya zaro daga cikin aljihun wandonshi domin duba ko waye ke kiransa sunan Nazifi yagani abokin aikinshi domin shagonsu daya, yana dagawa yaji yace,

"Prince ga wasu sun kawo dinki wai nanda next week suke so"

"Gaskiya bazasu samuba dunkuna sunyi min yawa"

"Hakane but amma naga ka karbi na wasu jiya ai"

"Ehh hakane amma ai kadai fi kowa sanin yawan dinkunan dake zaman jirana ko"

"Babu damuwa bari nakira hamza naji"

Katse wayar fahad yayi aransa yana cewa "yadai fi domin ita wadda kaga jiyan na karbi nata daban take bazan iya bari wani yayi mata ba shiyasa"

Ahaka yakarasa gida direct cikin gidan yawuce domin cin tuwo baba yahango kofar dakin mamuh yana magana dasu maryam wanda baya iya jiyo mai yake fada,durkusawa yayi kasa yagaida shi sannan yawuce dakin ayiyah yana dallawa Mariya harara saboda laifin da tayi masa da sassafe tun kafin tatafi makaranta, zaune ya iske ayiyah tana damawa baba fura acikin kwanon sha na silver da ludai ga sukari agefe cikin wani kofi madaidaici, zama yayi gefenta yana fadin,

"Ayiyah kamar kuwa kin san yunwa nake ji"

"To ai ga tuwon tsari nan miyar kubewa da mamanku tayi sai ka saka kaci idan kaci sai kasha fura"

"Ai kibar tuwon nan kawai ayiyah iya furar kadai zansha"

Kafin tayi magana baba yayi sallama yashigo, matsawa fahad yayi yabashi wuri ya zauna kan lallausar dardumar dake shimfide awurin,

"Muhammadu wai yaushe dan uwanka zai bullo ne?"

Murmushi fahad yayi domin yagane Abba yayansa baba yake nufi, gyara zamansa yayi yana daukar cup din furar da ayiyah ta zuba masa,

"Dazu munyi video call dashi baba yace insha Allah cikin karshen satin nan zaizo gida"

"To Allah yakawo shi lafiya muna zuba ido, ai saika yanke masa wadancan barun naka ko ko kaji ayi masa sauka"

Murmushi yayi bayan yazare cup din dake bakinsa ya hadiye furar da ya kurba.

"A'a baba,zan dai siyo masa akasuwa sai ayiya ta dafe masa su amma wadancan na kiwone bana ci ba"

Ayiyah tana mikawa baba furar da ta dama masa ta daga kai ta kalli fahad,

"Ni ban taba ganin irin wannan kiwon ba sai awurinka ayita kiwata abubuwa amma baza aciba..."

"A'a ai kedai babu ruwanki, barni dashi" Inji baba,

Murmushi fahad yayi yakarasa shanye furar da yake sha,

"Baba ayi min hakuri dai har sai sun kara yawa"

"Ni ai bance komaiba muhammadu, Allah yasa albarka"

"Amin babanmu"

Daga haka yatashi yafita,sai da ya leka dakin mamuh ya rarrankwashi mariya sannan yafito yana kunkunin idan tasake zuwa sassafe ta buga masa kofa yana bacci sai ya lakada mata duka. Dakinsa yawace ya rage kayan jikinsa sannan ya kwanta yana nazarin rayuwa, ganin tunanin nasa yana neman yin zurfi yasashi katseshi ta hanyar daukar wayarsa ya fada yanar gizo yana duba labaran abubuwan dake faruwa aduniya.

Har karfe goma saura yana haka zuwa can yatuna da bai turawa rabin ransa good night massage ba dan haka yayi hanzarin tura mata yana lumshe idanu kamar tana kallonshi.

***

Abangaren bilkisu ganin takasa gano wanda yake turo mata da massages dinnan sai tunaninta yabata cewar ya mudan ne cousin dinta wanda sam jininta bai hadu da nasa ba, wani tsaki taja bayan tagama karanta massage din da yashigo yanzu wanda take sa ran nashine, duk ji tayi kunci ya rufeta har saida takira hamood sukayi hira sannan taji damuwa da bacin ran dake tattare da ita sun kau.

Washe gari bayan tataso daga aiki kamar ta biya ta shagon su fahad sai dai tafasa saboda tasan su ammah na can gida suna jiranta saboda gobe za akawo lefen Hindu shiyasa suketa shirye shirye domin bata son lokaci yakure ba ashirya komai ba kuma tasan baza ayi komaiba agidan har sai anjira zuwanta.

***

Shi kuwa fahad yau tunda yafito shago suke tare da husna duk da ba wai yana son zaman nata bane domin kallo daya zaka yimasa ka fahimci haka sakamakon fuskarsa dake hade babu alamun fara'a ita kuwa husna duk inda yayi sai binsa take da kallon so cikeda burgewa domin sosai yau yayi mata kyau,

Yana dinka kayansu Hindu sai labari take bashi na garinsu shi dai kawai jinta yake amma bawai yana son labarin bane.

Yan shagon nasu kuwa kowa sai kallonsu yake yana yiwa fahad dariya kasa kasa,ganin bata da niyyar tafiya shi kuma ta takura masa yasashi fitowa fili yace taje ta tafi da yamma saita dawo, ai tana tafiya babu jimawa yagama abinda zaiyi yabar shagon, shagon su saleem yaje acan suka sha hirarsu wadda kusan rabi ta Bilkisu ce da take can bata san yana yiba. Saida sukayi sallar la'asar sannan suka nufi gida, koda yaje gida abinci kadai yaci daga nan ya kwanta baccin nasa na sabo nan yayishi har na tsawon rabin awa, karfe biyar da wani abu yafarka yayi wanka yafita filin ball duk da yau baya sha'awar buga kwallon amma yana son ya zauna ya kalli masu bugawar, ear piece yasaka acikin kunnenshi yafita yana sauraron wakar fall in love, kamshin oad kawai yake zubawa da haka ya isa filin kwallon yakama katanga yahau ya zauna yabi sahun wadanda ke zaune suna kallo, wayarshi ya ciro yayi dialing number din Bilkisu domin amatse yake da jin muryarta lokacin da ya kirata tana tsakiyar hayaniyar jama'a domin yan kawo lefen basu tafiba suna dai niyyar tafiya matsawa gefe tayi tai sallama cikin muryarta mai mutukar zaki wadda ta saukar masa da kasala mai nauyi cikin sanyin murya ya amsa bayan ya lumshe matsakaitan idanuwanshi sannan yabude su akan masu buga kwallo,

"Mai gado i really loves u...."

Jin abinda yace yabata mamaki duk da bata fahimci wayeba amma tagane itace number din da aketa damunta da turo mata massages dinnan, yanzu kam tagama yarda cewar ba yaya mudan bane wani ne daban wanda bata saniba.

"Uhmmm.kefa? Kina sona?"

Jin abinda yace ta dan nisa kadan sannan tace,

"Yanzu ina cikin wani uzurine amma idan anjima zan kiraka"

Kitt ta katse wayar takoma taci gaba da abubuwan dake gabanta yayinda shikuma tabarshi da faduwar gaba domin bugawa kirjinsa yashiga yi da sauri da sauri......

*_Ummi Shatu_*

© _*HASKE WRITERS ASSO*_

*KAMAR DA WASA.....!*

_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*

*6*

***Bilkisu bata samu kanta ba sai dare bayan sallar isha domin har karfe 9 saura na dare mutane basu bar shigowa kallon kayan ba, sai tara da wani abu ta samu tayi wanka tayi shirin bacci domin a mutukar gajiye take jinta yau tsabar busy din da ta shiga sau daya kawai sukayi waya da hamood, yanzunma bata jin zata iya kiranshi shiyasa kawai ta kwanta taja bargo. Tafara bacci sama sama taji karar wayarta,idonta cikeda bacci ta kara wayar a kunnenta,

"Love..... Bacci kikeyi?"

Jin muryar da bata saniba yasata katse wayar tareda kasheta gaba daya domin bacci take so tayi. Wurin sau biyar fahad yana gwada kiranta sai yaji akashe daga karshe dole sai hakura yayi shima ya kwanta din yana tunata acikin ransa.

Washe gari misalin karfe 10 nasafe ta sauka agaban shagonsu ita kadai domin ta baro khulsum a office tana fassara labaran turanci zuwa hausa itama kawai bikin nan da ya karato ne m d yake daga mata kafa, anutse take takawa babu hayaniya ta nufi shagon su fahad, yana daga waje kofar shagon gaban wani tebur yana yanka uniform din husna da ta kawo masa wuyansa rataye da tape na aunawa, sallamarta ce tafara shiga cikin kunnuwansa yayi saurin waiwayawa ganinta yasashi fadada murmushinsa yana sake bude kofofin hancinsa domin shakar kamshinta dakyau,

"Shiga ciki mana hajiya"

Murmushi tayi tanufi cikin shagon tana cewa,

"To nagode, Allah dai yasa ka cika alkawari"

P cap dinshi ya maida baya yabi bayanta yana murmushi,

"Ah haba hajiya ai ni bana magana biyu"

Kanta tabawa mazauni agaban kekenshi tana kallon cikin shagon wanda babu kowa aciki yau da alama sauran yan shagon sunyi nisan zango.

"Am nace nawane ma ragowar cikon kudin dinkin gaba daya?"

"Dubu biyar banda naki"

Tana kokarin bude jakarta batare da ta kalleshi ba tace,

"Ban gane banda nawa ba, ni baka dinka nawa kayan bane ko yaya?"

Zama yayi a mazauninsa yana wani murmushi mai kayatarwa,

"Na dinka miki, kawai dai ni ka'idata ce haka"

Dan dakatawa tayi daga binciken cikin jakarta da takeyi ta dago ta kalleshi cikin rashin sa,a idanuwanshi suka sarke cikin nata domin shima lokacin tsaka yake da kallonta, ahankali ta janye nata idanuwan ta maida kan jakarta tana cewa,

"Haka ka'idarka take kamar yaya?"

Tallafe kumatunshi yayi da hannunshi guda daya,

"Akaron farko nakan yiwa customer dina ragi ko indinka masa kyauta saboda ina son yakara dawowa so idan yadawo sai infara yimasa na kudi..."

Murmushi tayi tana jijjiga kai alamar gamsuwa murmushin da yakusa sumar da fahad azaune, kasa koda motsi yayi sai uba uban kallon da yake faman binta dashi har ta ciro kudin ta mika masa, karba yayi yana lumshe idanuwana sakamakon kamshinta da ya kusantoshi mutuka.

Sam ita bilkisu bata san abinda yakeyi ba dayake ma lokacin wayarta tana karar neman agaji alamar ana kiranta, ciro wayar tayi ta daga domin amma ce, tana dauka taji muryar meenah na cewa,

"Adda labour ba amma bace nice, dan Allah ko zaki taho mana da kayan kamshi?"

Agogon hannunta ta kalla na silver wanda yayi mata das,

"Meenah kufa matsala gareku,sakonku baya karewa, bari zan dubo"
Chapter 5 · 0% Book details