← Book details Kamar Da Wasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 67

Sashe 47

Kamar Da Wasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan bakin naki na rashin kunya nakusa nayi maganinsa....sai na kasheshi murus tayadda bazai kara fada min bakar magana ba...." Ita kanta saida taji tsikar jikinta tana tashi saboda yadda yayi maganar, su da suke fada amma voice dinshi tayi sanyi takoma cool sosai sannan tasauya tana fita a rarrabe sabanin dazu kodan kusancin dake tsakaninsu ne oho,kasa bude idanuwanta tayi sai dai tana ta kokarin kwace kanta daga rikon da yayi mata saboda hatta bugun da zuciyarshi keyi tana jinshi kamar yadda shima yake jin nata kasancewar manne suke da chest din juna wani karin takaicin ma shine babu fa komai ajikinta sai iya yar doguwar rigar da ta zira sai hijabi....

*_Ummi Shatu_*

*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*

44****Dariya ma shi taso bashi saboda yadda ta runtse idanuwa tana jiran taji abinda zai biyo baya, afirgice ta bude idanuwanta tana kallonshi saboda jin yadda ya take mata babban dan yatsan kafarta, muryarta na sarkewa tana rawa tafara hankadeshi tana cewa,

"Meye haka... ? Dallah ni sakeni..."

Sake damketa yayi yana kokarin saita kanshi, rikon da yayi mata ba karamin riko bane domin da irinta guda biyar zasu hadu ba lallai su iya kwatarta ba,

"Kin san me? Ina raga miki nefa saboda wani dalili wanda nabarwa kaina sani amma wallahi idan kikayi wasa...."

"Kadaina raga min din, kayi duk abinda zakayi....."

Tafada cikin jin haushin abinda yayi mata, juyi daya yayi ya canja musu position ita takoma jikin bango,

"Karki damu kiyi tayi min rashin kunya akwai ranar fanshewa, duk ranar da natashi hukuntaki kisa aranki ranar sai kinyi kuka da idanuwanki...."

"Dan Allah idan katashi yin hukuncin ka kasheni har lahira...."

Murmushin mugunta yayi wanda itama dakanta saida ta fahimci hakan domin da alama bai kai har zuci ba duba da yadda ya cure baki,

"Bazan kasheki ba amma zaki wahala over..... Sai kin gane ke karamar yarinyace ranar..."

"Kaine karamin yaro bani ba....."

Wata matsa yasake yimata hakan yasata kokarin tureshi tana ta huci saboda bacin rai,

Saida yabari tayi nisa wurin kokarin tureshi ta gama sakar jiki ya murde hijabin ya yar, nan sabon fada yatashi domin da iya karfinta take kokarin dauko hijabin daga kasa shikuma yasa kafa ya take, durkushewa tayi awurin tahada kai da gwiwa bayan tasaka kukan zuci,

"Matsoraciya kawai..... " yafada yana murmushi, daga haka yafice yabarta sai faman kuka take kukan bakin cikin rainatan da fahad yayi domin yanzu tagane yagama rainata tsaf sam baya ganin girmanta gashi duk maganar da tazo bakinshi sai yafada mata sai kace wata mate dinshi,

"Ni Bilkisu naga takaina.... Wannan wacce irin rayuwa ce..."

Haka taketa fada cikin kuka har tsawon wani lokaci, saida tagama kukanta ta share sannan tashiga wanka tafito duk sai faman kumbure kumbure takeyi ita kadai ahaka su ammah suka dawo suka sameta duk bata da cikakkiyar walwala sai cika take tana batsewa ita dai ammah idone nata batace uffan ba.

Washe gari awurin aiki khulsum tabi ta dameta akan takira fahad ta tambayeshi idan yabarta sai su wuce duba Christy basai sun koma gidaba saboda idan suka bari aka sallameta har tadawo aiki ba karamar kunya zasu jiba, agaba khulsum tasata da naci dole ta tashi tafita waje itafa bama ta da no dinshi dan rainin hankali, maama takira tana dagawa tace,

"Maama kinada number din wannan dan rainin wayon ko?"

Dariya maama tayi tana cewa,

"Adda labour amarya...."

"Maama ban son rashin kunya ina tambayarki kina yimin wasa..."

"Wai number waye kike tambaya?"

"Ban saniba ai kin san wanda nake nufi munafuka, kituro min yanzu"

Daga haka ta katse wayar takoma wurin khulsum, babu jimawa taji text yashigo sake tashi tayi tafita har khulsum na tsokanarta tana cewa,

"Ohh su labour yau lobayya ce ta motsa koda yake ai amarya kike..."

Bata kulaba tafice takira number fahad tanata ringing amma ba adaga ba harta katse, sake Kira tayi anan kuma sai aka daga amma ga mamakinta sai taji anyi shiru, ahankali kamar bata so tayi magana,

"Hello... Idan natashi daga aiki zanje dubiya...."

Kafin takarasa taji wata zazzakar murya tayi magana,

"Sorry mai wayar baya nan idan yadawo zan sanar dashi...." Batare da jiran amsar da zata bayarba kawai taji ankashe wayar, wani kululun bakin cikine ya tokare mata kirjinta kawai sai taji tana dana sanin kiran da tayi masa, shine dan walakanci zai barwa mace wayarsa? To ko wannan din itace wannan yarinyar da suke yin waya da ita? Kai ba ita bace, ita can ai tasan muryarta, ita dai tasan mutane da yawa suna yaba baiwar muryar da Allah yayi mata but gaskiya ta wannan har tafi tata zaki da taushi da kuma sanyi domin kana jin muryarta kasan irin matan nanne da suka yi nutso cikin kogin daula jin dadi da hutu ya ratsa ko ina ajikinsu su akewa kirari da hurul aini na duniya,

Tsaki taketa ja tana kwafa tarasa ina zata saka ranta taji dadi amma fa abisa dukkan alamu ita wannan dinma babbace domin kamar zata girmeta, shiru tayi tana tunani, itafa takanas mutane suke wanko kafa suzo gidan radio ganinta saboda kawai dadin muryarta da sukeji to amma muryar wannan ko ita mace saida tajita har cikin kwakwalwarta, to wacece ita? Meye hadinta da fahad?

Kafin tasake yiwa kanta wata tambayar da batada amsarta khulsum tafito rikeda hand bag dinta,

"Labour yadai?"

"Nothing, na kirashi ne ban sameshi ba shine nake jira ko zai kira..."

"Ok to kafin kugama bari naje nayi voicing din report din can... Ke kinyi nakine?"

Girgiza kai tayi cikin sanyin murya da na jiki gaba daya tace,

"A'a ni koma fassarar banyiba tukunna... Jeki kiyi nakin kawai...."

Daga haka takoma cikin office ta zauna tasoma juyawa kan kujerar da take kai.

FAHAD

Sosai Bilkisu taso rikita masa lissafi yau saboda kusancin da sukayi har yayi yawa jinta ajikinshi tana half naked yasaukar masa da wata irin kasala da sha'awarta mai karfin gaske amma koda yatuna ta auri wani kafin shi ahalin yanzu sai duk yaji bacin rai da bakin ciki sun rufeshi wadanda sune sukayi sanadiyyar gushe sha'awar data taso masa shiyasa ma yabar wurinta babu shiri yanufi gida, dakyar da sauraron karatun kur'ani yasamu yaji daidai. Washe gari dayaje asibiti sunada tarin ayyuka masu wahalar gaske wadanda zasuyi shiyasa dole sai mutum ya nutsu sannan yayi taka tsan tsan wurin fitar da result din, office din Dr murja yashiga yakai wayarshi da laptop domin suna yin good time da ita tana mutukar ji dashi duk cikin daliban da aka turo babu kamarshi awurinta shiyasa sauran students din ke zargin wai sonshi takeyi gashi ahaife ma zata girmi Bilkisu matarshi, system dinshi yasaka a charge ita kuma wayar yabata ajiya yafita shiyasa lokacin da bilkisu takira bata sameshi ba Dr murja ta daga, bai samu kanshi ba sai around 3 duk agajiye yake yashiga office din Dr murja yakarbi wayarshi da laptop domin tafiya gida, har zai tafi yaji tace,

"Soul mate takiraka..."

"Ok tom zan kirata"

"Wacece ita?" Tafada bayan tazuba masa gaba daya idanuwanta wadanda take juyasu cikin salo na daukar hankali shi wallahi kunya ma yakeji idan tana yimasa wannan farin,

"Anty wife dinace fa..."

Yafada yana shafar kai, juya idanuwa tayi ta shagwabe fuska,

"Ashe kanada aure shine ban taba saniba?"

"Wallahi inada aure....."

"To amma tana kula dakai? Zo kafada min mana handsome..."

Dariya yayi cikeda kunya yafice daga cikin office din, tun yana cikin asibitin yake faman kiran wayar Bilkisu amma bata dauka ba kuma tana zaune tana fassara labarai amma taki dauka tana kallon wayar har tayi tagama bata daga ba ita tarasa dalilinta na jin mugun haushinsa yau fiyeda kullum. Wannan dubiyar dai bataje ba sai khulsum ce tatafi ita kuma tawuce gida tana zuwa gida taci abinci tayi sallar la'asar takira Abba ta gaidashi sannan tawuce toilet, wanka tayi tafito tashirya cikin kayan shan iska riga armless zuwa gwiwa da wandonta duk light purple, ta dauko system dinta ta fita zuwa dakin ammah da wayarta ahannu tana zama wayar tasoma ruri sam batayi niyyar dagawa ba saboda tasan ko waye amma sanin ammah na iya yin magana yasata dauka,

"Ke wato shine zanyita kiranki amma dan rainin wayo ki k'i dagawa ko?"

Jin abinda yace yasata tashi sim sim tafita daga dakin amma zuwa nata,

"Ba dake nake magana ba...?" Yafada cikin tsawa,

"Kaga malam ya isheka ni kar kayi min ihu aka, borin kunya kakeyi ba komai ba kuma wallahi sai kafadi wacece matar da ta daga wayarka lokacin da nakira idan bahakaba har kunnensu abba maganar nan dan bazan iya zama da mai kula mata awajeba...."

"An kula matan kiyi duk abinda zakiyi.... Meye naki aciki dan nakula mata? Kabarinmu dayane dake? Ban son shisshigi..."

"Wallahi duk wadannan maganganun akunnen abba, mayaudari kawai...."

Daga haka takashe wayar gaba daya komawar da batayi dakin amma ba kenan, tun daga ranar rigima takice taki cinyewa har tsawon makonni biyu suka dauka suna wannan fadan ta waya domin bai samu zuwa gidan ba ita ta damu akan lallai sai yafada mata alakarsu da matar da ta daga wayarta lokacin data kirashi acewarta tana gudun sake facing irin abinda hamood yayi mata yadauko karuwa ya ajiye mata azuwan matarshi ce ita tunaninta kenan amma sam bata taba zargin kanta da yin kishinsa ba, shikuma hakan da take ta fada ne yake bata masa rai shiyasa yau yashirya zuwa gidan domin ayita takare.

Sai bayan da yayi sallar magrib sannan yaje gidan, kamar koda yaushe iya amma yasamu falonta tana kallo kasancewar mai aikinta tatafi, tashi yayi yafita cikeda kunya zuwa dakin Bilkisu wacce ke zaune kan abin salla, yi tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da tasbihinta,

Agefen gadonta ya zauna harda kwanciya tana ganinsa bata tanka masa ba text yake turawa shiyasa shima baiyi magana ba bayan mintuna biyu da tafiyar text din saiga kiran husnah dama ita yaturawa yana yimata barka da shan ruwa kasancewar yau alhamis,

"Husnah ta....kinsha ruwa lafiya..."

Kamar acikin mafarki Bilkisu taji tace,

"Ya fahad bayan azumin karyewa yayi bayan sallar la'asar saida nagama shan wahalat...."

Bai karasa jiba yaji bilkisu taja tsaki da karfi tamike tana nannade prayer rug dinta,
Chapter 47 · 0% Book details