← Book details Kamar Da Wasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 67

Sashe 4

Kamar Da Wasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tallafe kumatunshi yayi da tafin hannunshi na hagu yana kallonsa, hannu takai zata warci wayarshi yayi saurin kaucewa yana harararta,

"Wai bana hanaki tabani ba?? Meyasa bakya jin magana ne?"

Marairaicewa tayi tana kallonshi,

"Am very sorry my heart beat"

Baice komai ba yasoma laluben kayanta acikin tulin himilin kayan dake gefenshi, aranshi yana tunanin halayyar husna ta son tabashi shiyasa baya sakar mata fuska sosai saboda indai zatazo wurinshi to sai tayi yunkurin taba masa hannu ko wani abu mai kamada haka, ciro mata kayanta yayi ya ajiye mata agabanta sannan yatashi ya hado mata kan kwanukanta wadanda take kawo masa abinci duk da bawai ci yakeba dan su nazifine ke cinyewa, saida tagama janshi da magana da wasa sannan ta kwashi kayanta ta tafi, tashi yayi yafita salla ana idarwa yadawo yazo yasoma yanka kayansu Bilkisu.

***

Agajiye lilis takoma gida kamar koda yaushe yauma gidan acike yake da makota da kawayensu meenah amare domin anata shirye shirye,kanta yau har wani ciwo yakeyi sakamakon uban yawon da suka sha a kasuwa itada khulsum ga yunwa da take ji,

Sama sama take amsa kowa ta bude dakinta ta shiga itada hudah wacce ke makale da ita, tana zama Hindu tashigo rikeda lemon roba mai sanyi da ruwa,

"Yawwa yar albarka kamar kuwa kin san kishi nake ji sosai, gaskiya yau mun kwashi rana"

"Sannu anty mai gado, ai duk wanda yaganki yasan kin wahala"

"Kedai bari Hindu" tafada tana balle murfin robar lemun"

"Inkawo miki abincin?"

"Kawo min Dan sai nafara ci sannan zanyi salla" tabata amsa tana kokarin bawa hudah lemon abaki, fita Hindu tayi ita kuma taci gaba da karbar lemon tana bawa hudah.

Shinkafa da wake da ganye Hindu ta kawo mata da manja da yaji nan ta sauko taci sannan tashiga ta watsa ruwa tafito tayi salla, nan inda tayi sallar suka baje itada hudah suka hau bacci.

***

Fahad bai bar shago ba sai bayan sallar magrib domin saida yagama yanka kayansu Bilkisu kaf sannan yanufi gida duk da irin tarin yunwa da gajiyar dake baibaye dashi, lokacin da yaje gida bai shiga cikiba dakinsu yafara shiga yayi wanka sannan yashiga cikin gidan, dukkansu suna falon mamu suna kallon wasan kwaikwayo na aku mai labari wanda ake gabatarwa agidan television din ART, daga bakin kofa yatsaya yagaidasu sannan yawuce dakin ayiyah duk da yanajiyo tsokanar da mamuh keyi masa bai kula ba domin yunwa yakeji dan rabonshi da abinci tun safe.

Abincin dare yazuba yaci wato tuwon biskin masara miyar taushe yana ci yana santi har yagama yafito bai koma inda su ayiyah sukeba yafice ya nufi dakinsa, farar jallabiya yasaka yafita sallar isha'i domin daf ake da ashiga. Koda aka idar yadawo kwanciya yayi da niyyar runtsawa amma sam yakasa yin baccin sai juyi da yafara yi, fuskarta kawai yake gani wacce ke dauke da murmushi tana yimasa magana,bashida zabi illa na yabi shawarar zuciyarsa ko zai samu sassauci.

*_Ummi A'isha_*

11/28, 08:14] Hafsat Rano: © *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_

*KAMAR DA WASA...!*??

_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*

*4*

***Kasa nutsuwa yayi sakamakon dukan luguden da zuciyarsa keyi tamkar zata faso kirjinsa tafito waje dan tsananin zafin sonta, ahankali cikin sanyin jiki yatashi ya dauko wayarshi wacce ke ajiye tana charge saboda akwai wutar nepa agari,

Komawa yayi ya kwanta ya lalubo contact dinta, _soul mate_ shine sunan da yasaka mata nan yakurawa number tata ido kamar wanda ke son haddaceta har zuwa tsawon wani lokaci, yanke shawarar tura mata da sakon karta kwana zuciyarsa tayi nan ya rubuta mata ya tura mata cikeda shaukin kaunarta har saida yaga sakon ya tafi sannan yaji ya dan samu nutsuwa, ajiye wayar yayi akusa dashi kamar wadda ake jira nan tasoma tsuwwa amma bai kulaba domin jikinsa yabashi husnah ce wadda ba komai zata fada masaba illah ta kara masa damuwa dan haka yashare yaci gaba da tunanin abar kaunarsa.

***

Jikinta sanye da yar guntuwar karamar riga kalar ruwan madara wacce take marar nauyi da kauri tana tattara wani report da zata gabatar acikin laptop dinta taji shigowar sako, duk da bata dubaba saida tayi murmushi domin tasan bazai wuce hamood dintaba wanda ko mintuna biyar kwarara basuyi da gama wayaba, saida ta shanye sanyayyen lemon dake gabanta sannan ta janyo wayar bayan ta rufe laptop din. Kwanciya tayi tabude sakon, abin mamaki yabata saboda ganin wata number wadda bata hamood ba, cikin mamaki ta soma karantawa kamar haka, _Salam yake kyakkyawa,hakika kinyiwa zuciyata wani tarko mai wuyar Ketarewa, ganinki sau daya tal yana barazanar kawar da tunanina daga gangar jikina, wallahi ban taba ganin wata halitta wacce tayi daidai da ra'ayina kamarki ba, kece mace tafarko da nafara so tun kafin nayi ido biyu da ita, dan Allah karki ki k'i amsar soyayyata domin idan baki amintaba zan iya rasa rayuwata akan sonki, wallahi ina mutukar sonki, ina sonki bilkisu._

Dora wayar tayi akan kirjinta gabanta yana faduwa sannu sannu, aranta tana tunanin to shikuma wannan waye shi? A ina yataba ganinta da har yaji yana sonta? Bata da amsa dan haka tayi watsi da tunanin batare da tabarshi yayi tasiri acikin zuciyarta ba. Addu'ar bacci tayi ta shafa tayi kwanciyarta bayan takashe wayarta, amma me koda gari yawaye tana kunna wayarta sakonshi ne yafara shigowa cikin wayarta inda yake yimata barka da safiya da wasu kalaman soyayya masu sanyaya zuciyar masoya, dan guntun tsaki taja ta ajiye wayar gefe ta kwanta batare da tabi takan mai turo sakon ba.

Aranar ko aiki bataje ba domin sunata soye soye da dafe dafe kasancewar ranar za akawo lefen meenah, itace akan komai gashi gidan ba laifi yayi albarka domin yan uwa na kusa da makota duk anshigo domin karbar kayan, sai misalin karfe uku na yamma aka kawo kayan nan aka shiga tarbar baki da abubuwan da aka tanadar musu basu bar gidanba sai bayan da sukayi sallar la'asar sannan suka tafi nan kuma makota aketa shigowa ganin kaya wadanda suka kasance akwatuna hudu manya sai dan karamin kit na biyar kalar ruwan kasa ita kuma Hindu sai nanda kwana biyu za akawo nata. Ita dai bilkisu yau tunda tatashi kanta adaure yake domin maiyi mata sakon nan ba dainawa yayi ba sau hudu kenan yau yana turo mata sakonni masu dauke da kalaman so da kauna tun tana sharewa har ta zauna tana son sanin waye.

***

Fahad yau tunda yafita shago baiyi aikin kowaba sai nasu bilkisu nata yawuni yana hadawa domin dinki na musamman yayi mata wanda babu irinshi ashagon kuma koda yagama hadawa bai barshi ashagon ba bare har aratayeshi a hangar wurin da suke rataye kayan da suka dinka, shi kansa ya yaba da dinkin da yayi mata shiyasa yake jin zuciyarshi wasai, Abu daya kawai yanzu yake bukata shine yaji muryarta amma yasan hakan ba mai yuyuwa bane. Wata numbershi wadda bai cika amfani da itaba yasa numberta yakirata amma harta tsinke ba adaga ba sai da yasake kira sannan yaji ta dauka cikin sanyayyiyar muryarta wadda kamar tana bacci, sallama tayi amma sai yasamu kansa da kasa amsa mata domin wani irin faduwa gabanshi yasoma yi wanda bai san daliliba,

Sau uku tana fadin "hello.... Hello....., hello"

Jin bai amsaba takatse wayarta, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sai lokacin yaji yasamu kwarin gwiwar yin abinda yake gabansa, tashi yayi ya tattara inasa inasa ya nufi gida lokacin misalin karfe biyar da wurin mintuna ishirin, yana zuwa gida kayan ball dinsa yasaka yafita batare da yashiga koda cikin gidanba acan yasamu ya ragewa kansa damuwa domin sai karfe 6 da wani abu yadawo. Wanka yayi yasha turare kamar wanda zaije zance yafita masallaci can yayi zamansa shida saleem har saida sukayi sallar isha'i sannan suka fito, wani sabon zaman suka sake dasawa akan dakalin simintin dake kofar gidansu saleem wanda wurin yake fuskar mutane ga hasken farin wata wanda ya hadu da hasken lantarkin dake kafe atsakiyar layin wanda ya ratsa ta cikin unguwar tun daga farkon layi har zuwa babban titi can gefe daya kuma yarane dankam masu soya awara nayi wasu kuma gyada suke saidawa da dafaffen kwai da sauransu.

Daga kansa sama yayi yana kallon taurari wadanda suka karawa sararin samaniya ado da kawa, cikin sanyin murya yafurta,

"Abokina am in love....."

Juyawa saleem yayi ya kalleshi yana murmushi sannan ga alamun mamaki nan bayyane akan fuskarshi,

"Yaushe? Kuma wacece?"

Lumshe idanuwa fahad yayi yana jin wata sabuwar soyayyarta tana shigarshi,

"Wata classic beb ce, kuma wallahi najima dauke da sonta"

"Kodai husnah ce?"

Harararsa fahad yayi kasancewar akwai yalwataccen haske yasanya saleem ganin hararar hakan yasashi yin murmushi sannan yadafa kafadarshi,

"Bani labarinta abokinah..."

Saida yayi murmushin da shi kadai yasan dalilin yinsa sannan yafara fada masa,

"Nafara sonta ne tun ban gantaba, tun ranar da nafara jin muryarta a radio tana gabatar da wani shiri naji tashiga raina, kullum da ita nake kwana nake tashi, cikin ikon Allah sai gata jiya a shagonmu ta kawo min dinkunanta..... Amma bana jin zata soni" Yakare maganar yana cizar lips dinsa cikeda damuwa,

"Saboda me kake ganin bazata soka ba? Kanada wani mummunan haline wanda ban saniba?" Saleem yafada yana fuskantarshi,

"Sam bahaka bane, saleem ta girmeni fa, jikina yana bani bazata yi accepting dinaba saboda zatace nayi mata yaro dayawa may be ma zata ji kunyar nunani awurin friends dinta da relatives dinta"

Dariya saleem yayi yana dafashi,

"To kai da waye ya aikeka son wacce ba sa'arka ba?"

"Saleem kenan, shi so ba ruwansa da cancanta,shekaru ko duba matsayi, kawai yakan shigane aduk sa'ilin da yaso koda kuwa ba ashiryawa hakanba, saleem wallahi dagaske ina sonta, ni girmemin din da tayi ba damuwa bace zan iya rayuwa da ita mutukar zata yarda ta aureni"

Shiru saleem yayi yana kallonsa, ganin yanda yanayin idonshi ya sauya zuwa ja yasashi gasgata aminin nashi,

"Abokina ka kwantar da hankalinka, ina kyautata zaton koma wacece zata soka itama domin baka da makusa kuma bakada wani hali ko dabi'a wadda bata kirkiba, kana da zuciyar neman na kanka sannan kana da kyakkyawar mu'amula da kowa, kayi addu'a abokina insha Allah zaka dace"
Chapter 4 · 0% Book details