Sashe 9
Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowan mu yana shiga yayi hanzarin ɗalewa gado, ranan da ƙyar na tashi nayi sallan asuba, sannan na sake komawa baccin, bani na tashi ba sai after 10, a razane na buɗe ido na ina kallon time, ganin da gaske haka lokacin ya yi ya sakani tashi da sauri na shiga toilet na yi brush na yi wanka, ina fitowa na ɗauki waya na na ƙira number'n Amal.
Yana fara ringing bai daɗe ba aka ɗauka, naji muryan Amal a hankali ta ke mun magana, haƙuri na fara bata ina gaya mata wani irin bacci ne ya tafi dani, don sai yanzu ma na tashi daga bacci, amma tayi haƙuri me zan kawo mata tayi breakfast?
Sautin dariyan ta naji sannan ta ce,
"Ki kwantar da hankalinki sister, komai da ka ke buƙata asibitin suna maka, kuma already ma Dr Hussain tun 7:30am ya kawo mun break, amma yasamu ma har suna bani, so kar ki damu kan ki, kawai kizo na ganki kafin su Abbu na su iso".
ta faÉ—a tana mun dariya a hankali.
Ina ajiye wayan na wuce kitchen na haɗa tea cikin sauri-sauri, ina gama sha na fito nayi ɗaki na, shima da sauri na shirya na fito domin tafiya duba Amal, ina fitowa na harari gidan Dr Hussain sannan na murguɗa baki na, dai-dai lokacin Peter ya fito daga nashi gidan, sauƙa nayi na ƙarasa inda yake muka gaisa, yana duba na da tausayi yace,
"jiya a can ki ka kwana Preety?".
Dariya na É—anyi kaÉ—an na ce,
"gida muka dawo ni da Dr Hussain saboda hospital É—in basu bari a kwana da patient".
sai naga ya yi sauri ya duba gidan Dr Hussain sannan ya juyo in da na ke yana murmushi yace,
"Dr yana kishi akan ki Preety, halan yana so ya É—auke sister shi ba zai bari ma kowa ba".
Baki na buÉ—e cikin mamaki ina duban shi, sannan nima na kalli gidan Dr da wuri nace,
"rufa mun asiri, ni kuma mai ya kaini auren tsoho? Kasan Dr nan ya kai 40yrs kuwa, kuma baka ga matar shi mai kyau ba ce, me zai yi da ni Æ´ar cukala dani, kawai masifan shi ne ya sa ka ya bimu bawai so ba".
Peter yana duba na da mamaki yace, "dama yana da mata ne bamu sani ba?".
Zaro ido nayi na ce,
"tuntuni kuna ta re da shi baku san wife É—in shi ba sai ni dana zo daga baya? To Dr Khadija ce fa wife É—in shi".
na faÉ—a kaman zanyi kuka.
Dariya mai ƙarfi Peter yayi sannan yace, "your not serious baby, ai Dr Khadija kowa yasan tana son Dr, amma shi bai taɓa kula ta ba ma, kuma kin bani haushi da ki ke cewa wai tafi ki kyau, ke kinsan irin kyaun ki kuwa?".
Yana bina da kallo yana duba agogon shi kuma, lokacin David ya ƙaraso in da muke tsaye, idon shi cikin ido na sai bina da kallo yake yi, yana ƙarasowa yace,
"Preety kinyi kyau sosai, an taɓa gaya miki babu mai irin kyawun ki kuwa"?... Da sauri Peter ya amsa da cewa, "gaya mata dai tasan irin yadda ta ke da masifar kyau, amma kyawun wata Dr Khadija yana ba ta tsoro".
Ni dai yau wani daÉ—i nake ji a raina, saboda sun yabe ni sunce nafi kowa kyau, sannan kuma Peter yace mun Dr na ba shi bane mijin Dr Khadija, sai wani smilling kawai na ke yi, a haka David yace, "ina za kije? Ko hospital za ki koma?".
ÆŠaga mishi kaina nayi alaman ehh.
"To bari mu kai ki, muma church zamu wuce yau sunday, sai mushiga mu duba jikin friend É—in kin".
muna shiga motan naga Dr ya buÉ—e gidan shi ya fito, kuma daga ganin shirin nashi na fita ne, lokaci É—aya naji gaba na ya faÉ—i, a raina nace,
"Allah yasa kada ya mun masifan na bi su David".
har muka fita idon shi yana kan mu, nima kuma shi É—in na ke gani.
Har ɗakin da ta ke muka shiga tare da su David, suna gaishe ta suka tafi, har lokacin tana kwance ana mata ƙarin ruwa, gefen ta na matso na zauna, na saka hannu na a kan ta ina ƙara gaishe ta da jiki.
Murmushi ta yi tana maida idon ta tana rufewa, alaman wani baccin ta ke shirin komawa, abin tausayi gaba ɗaya kwana ɗaya tayi wani mummunan ramewa, wani irin tausayin ta na keji a cikin raina, na daɗe ina kallon ta cikin jimami, can naji ƙira yana shigowa waya na, da sauri na ɗaga wayan don kada ta tashi.
Daddy na na gani yana yawo a saman screen É—in, da sauri na É—auki wayan na kara a kunne na, gaishe shi nayi, shi kuma ya tambaye ni ya ya jikin Amal?
Bayan mun ɗan gaisa da shi na ajiye wayan, sai naji an buɗe ƙofan ana shigowa, kafin na ɗaga kai na dube shi ƙamshin shi ya fara isowa gare ni, da faɗuwar gaba na ɗaga ido na nadubi in da ya ke, shi ma idon shi duka biyu sauƙe suke a kaina, kaman ba zai shigo ba ya tsaya ya ƙura mun ido daga in da yake tsaye, ganin haka na sauƙa a kan gadon na ƙara sa gaban shi, turo baki na nayi ina kallon shi, cikin shagwaɓa nace,
"To ba kai bane kazo asibitin ba ka tashe ni ba, shi ne nima na taho ban gaya maka ba".
Na faÉ—a ina É—an kawar da kaina saboda irin kallon da ya ke jifa na da shi.
Kukan shagwaɓa wanda babu ko ɗigon hawaye na fara yi, ina bubbuga ƙafa na a ƙasa,
"to ni me na maka kake kallo na haka? Bayan nasan ban maka komai ba".
na faÉ—a ina kallon shi.
Wucewa yayi zuwa kan kujeran da suke É—akin guda biyu ya zauna a kan É—aya, bayan ya daina kallo na ya maida idon shi kan Amal.
"Aisha baki gaya mun meye gyenotype É—in ki ba? Tun jiya kuma na ke tambayan ki, ko kin raina ni tunda kina da su Peter ko?".
Matsowa na yi in da yake na zauna a ɗayan kujeran ina kallon shi, fuska na ɗauke da murmushi, ƙasa-ƙasa da murya don kada na tashi Amal nace,
"Dr mu kasan yau su Peter da David suka ce wai ina da kyau har ma nafi matar ka Dr Khadija kyau".
Na faɗa ina riƙe haɓa na alaman abin ya ban mamaki duk irin kyawun ta amma a kace na fita kyau.
Harara na yayi sannan yace,
"saboda baki da hankali kinje kin tsaya a gaban ƙattin banza suna ce miki wai kina da kyau, ke kuma don shirme har kina biye musu kina yarda ke mai kyau ɗin ce ko? Har kina haɗa kan ki da kyawun Khadija?".
Tsaki ya ja mun ya maida kan shi kan Amal da yaga tana É—an motsawa.
Ƙura mishi ido nayi ina jin zuciya ta kaman zata faɗo, don wani irin masifan zafi na ke ji, ina kallon shi kaman na tashi na shaƙe shi, murya a hankali domin rawa ya ke mun nace,
"Dr'n mu don ita wife É—in ka ce shi yasa kafi ganin kyawun ta a kaina ko? To kai me ya sa ba ka ganin ina da kyau ne? To wallahi sai na gayawa Daddy ka ce matar ka ta fini kyau".
Ɗauko waya na nayi ina neman number Daddy, sai ji nayi ya ƙwace wayan a hannu na,
"saboda hankali ya miki karanci shi yasa za ki ƙira Daddy a wannan shirmen banzan na ki ko? To ke me ya dame ki idan ni bance kina da kyau ba? Ba sauran wanda kike so suga kyawun ki sun gaya miki ba".
"To ni kai na ke so kace ina da kyau, ai ita kana ganin kyawun ta, ni me yasa baza kace ina da kyau ba, ni kai nafi so ka faÉ—a".
na faɗa ina zunɓuro mishi baki na.
Tsaki ya ja yana duban agogon hannun shi, sannan yace, "ni ai banga kina da wani kyau ba, saboda kyawun Khadija ba ya bari na naga kyawun kowa".
"Dr'n mu ba kace ina kama da Aisha ba, to ita Aishan bata da kyau ne? Ai ya kamata saboda ita kace ina da kyau, tunda ina kama da ita ai ya kamata kana ganin kyau na saboda darajan ta, kasan ko a lahira wani yakanci albarkacin wani".
na faÉ—a ina matsuwa kusa da shi.
"Yayan mu don Allah ni mai yasa baka ganin kyau na ne? Kullum sai kace Fatin Aunty Hauwa tana da kyau saboda tana kama da Aunty Hauwa, to ai nima ina kama da Ummi da Aunty Hauwa, kuma ni nafi Fatiman kyau saboda ita bata É—auka asalin kaman Aunty Hauwa ba, ta É—an É—auko kaman Baban ta ai, ni ma don Allah Yayan mu kace ina da kyau mana".
muryan Aisha ya ji wani lokaci Aunty Hauwa tazo da ƴar ta Fatima wanda bata fi 5yrs ba, yarinyar ta mishi kyau saboda gashin ta da Aunty Hauwa ta gyara, shi dai yana so yaga mace mai gashi sosai a rayuwar shi, shiya sa Fatiman ta mishi kyau, bai iya ya ɓoyewa ba kuma ya faɗa, shine Aisha ta ke mitan ita bai ce tayi kyau ba, wanda ɗabi'an Aisha ne ita kullum ace tana da kyau, gashi kuma yau wannan mai rikicin ita ma haka ta ke.
Tunawa da hakan ya saka ya dawo da kallon shi kaina, ƙura mun ido yayi yana kallo na, can sai yace, "mai yasa ki ka damu dani sai nace kina da kyau?".
Kallon shi nayi kaman zanyi kuka nace, "ni kawai kai kaÉ—ai na ke so kace ina da kyau, kasan me yasa na ke son hakan Dr'n mu"?
Girgiza mun kai ya yi alaman a'a, dariya nayi mai ɗan sauti, sannan na sunkuya ƙasa-ƙasa da murya nace,
"nifa kana mun kyau sosai Dr'n mu, kuma ai ni nace kana da kyau kuma kai mai ƙamshi ne, ya kamata kaima kace Humaira kina da kyau kuma kin iya girki mai daɗi".
na faÉ—a da yanayin kwaikwayon muryan shi, ina duban shi ina dariya a hankali don kada na tashi Amal.