← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 66

Sashe 49

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu ɓata lokaci Baban Narabi washe gari da ƴan'uwanshi mutum biyu, sai uncle sabo ƙanin uncle Abdallah dayaja zuwa misau. Bappah ba ƙaramin karɓa ya musu ba, bayan sun gaisa sun sha ruwa Baban Narabi yayiwa Bappah bayanin abinda ya kawosu, Bappah tashi yayi ya ƙira ɗan'uwanshi wanda yake mahaifi wa Aunty Ummi da Dr Alƙali, da yake shi bamai son wargi bane yace su tsaya ana sallan azahar a ɗaura aure kawai, babu maganan jeka ka dawo a tsakanin su, Bappah ma yayi na'am da batun ɗan'uwan shin, suma su Babam Narabi sunji daɗi ba kaɗan ba da irin dattakun da aka musu.

Ana sallan azahar aka ɗaura auren Aunty hauwa da Uncle Abdallah a masallacin ƙofan fada da yake garin misau, hattah su Mama dasu Addagana sunji daɗin wannan auren ba kaɗan ba, domin farin cikin yaxama musu biyu, inda Uncle Auwal yazo musu da labarin aikin shi daya samu da NNPC, inda Baban Misau, kuma ɗan Mutanen Misau, Dr maikanti baro Allah yajiƙanshi da rahma ya sama mishi aiki a wancan lokacin. *ALLAH KAJIƘAN DR MAIKANTI BARU, ALLAH KASA YANA CIKIN RAHMAR UBANGIJI, ALLAH KA DUBA BAYAN SHI KASHIGA AL'AMURAN SU YADDA SHINA YA SHIGA NA MUTANE, ALLAH YA HASKAKA RAYUWAR IYALANSHI*

Lokacin da aka gama ɗaura aure Baban Narabi da kanshi ya ɗaga waya ya ƙira Abdallah yana murmushi yace, "Albishir Abdallah!" cikin zaƙuwa ya amsawa Baban nashi da "goro".

"Toh yau dai Allah ya nufa an É—aura aurenku da Hauwa, sai ka shiryah mana goron Albishir É—inmu", Baban ya faÉ—a mishi cike da murna, ae babu shiri Abdallah yace, "Baba nabaka kujeran zuwa umrah kaida su Bappah, insha Allahu ku uku kushiryah tafiya zuwa nan da sati biyu", murmushi mai cike da dattaku Baban ya amsa mishi da sun gode, tukun yace ya bar maganan tarewar har sai ita hauwan ta shiryah, daga nan sukayi sallama ya kashe wayan.

Saida akayi sallan La'asar tukun su Baban Narabi da bappanun Abdallah suka dawo Narabi cike da murnan abinda ya faru, suma mutanen gidan kowa ka ganshi cike da murna a fuskar shi.

Bappah ne ya ƙira Dr Alƙali yagaya mishi an ɗaura auren Aunty Hauwa, sannan kuma yace ya sanar mata, sannan ya ƙira su Ummi ya sanar musu, ita dai Ummi taji daɗin wannan haɗin, don ko baɓu komai, baza'a rabawa Aisha hankali yadda zata fahimci wani abuba, duk ranan da taje wurin Aunty hauwa zataje ne a matsayin gidan Ummanta, Abdallah kuwa Mijin Ummanta, kenan komai zai zo mata cikin sauƙi, gaskiya Ummi taji daɗin abun ba kaɗan ba.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/27, 12:09] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1442H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 40📑*

*__________📖* Dr Alƙali yaji daɗin al'amarin ba kaɗan ba, dama yana zaune a office ne, kawai sai yaji kaman yayi tsuntsuwa ya koma gida, haka ya daure ya gama duba patients ɗin da suke gaban shi, yana gama ganin su ya kamo hanyar gida.

A parlour ya samu Aunty hauwa tare da Aunty uwani suna cin abinci suna kallo kuma, yana murmushi yace, "Æ´an mata sai yanzu kuke cin abinci? Laillai kuna jin daÉ—i fah", ya nemi wuri gefen matar shi ya zauna.

Bayan sun gaishe shi ne, suka cigaba da cin abincin sun hankali kwance, shidai sai duba abu yake a wayan shi batare da yace uffan ba kuma, suna gama ci Aunty hauwa ta miƙe zata bar wurin domin mata da mijin su samu sakewa, ganin haka yasa ya ɗago da manyan idanunshi yana murmushi yace, "amaryah dawo ki zauna, tafowan da nayi ae duk don ke ne".

Wurin data tashi ta koma ta zauna tana kallon shi, "yauwa Hauwa ɗazu Bappah ya ƙirani yake gaya mun cewa na gaya miki yau ya ɗaura miki aure da ƙanin mijinkin nan Abdallah"........ Wani irin miƙewa tayi da murya mai ƙarfin gaske tace, "a wani hujjan za'a ɗaura mun aure da mutumin da bana so" wallahi auren nan bai ɗauro ba, ko sama da ƙasa zasu haɗu toh aure bai haɗu ba", ta faɗa tana zare ido kaman zata kai duka wa Dr.

"Saboda ke kin isa da kanki ko? toh ki sani bawai barinki ake yi ba kike abinda kika gan dama hauwa, kuma baki isa kija da iyayen mu ba, aure an riga da an ɗaura ya rage naki kiyi biyayyah wa mijinki ko akasin hakan", yana gama faɗa ya miƙe yayi ɗakinshi, ita dai Aunty uwani sai juya kanta take tayi alaman bata so hakan ba, tafi so abi komai a hankali, hakan yasa ta fara rarrashin Aunty hauwa, ita kuma bata sararara ba kawai ihu da kuka ta fara, daga baya ta fita da gudu zuwa ɗakinta, inda suke tare da yaran Aunty uwani, kwanciya tayi ta fara rera kuka mai azabar taɓa zuciya.

Har akayi magrib Aunty hauwa kuka ta keyi bata saurari kowa ba, bayan tayi sallah ne ta shiga wanka domin tayi shirin tafiya night duty da ta keyi, wanda yau idan tayi zata shiga up na 1week, tana wanka ta shirya, lokacin aka ƙira ishaa, babu ɓata lokaci tayi sallan ta miƙe ta ɗauki jakanta ta fito domin tafiya, a parlourn ta samu Dr da Aunty suna cin abinci, yana dubanta yace, "amaryah kinci abinci kuwa"?.

Hararan shu tayi bata ce mishi komai ba tayi hanyar waje, tana fita yayi murmushi ya dubi bayanta yace, "zama ki ɗame ae", suka cigaba da cin abincin su shida matar shi, wanda ta ke ta mitan ya dinga bin ta a hankali da lallaɓi, bawai yayita ɓata mata rai ba, shidai dariya kawai ya keyi bai ce mata ƙala ba.

Tana shiga office ta samu wanda zasu karɓe su suna shirin tafiya, gefe ta samu ta zauna, bayan sun gaisa taji wayanta yana ringing, da sauri ta fito da shi kawai sai taga Baban Narabi ne, jikinta yana rawa ta ɗauka sannan ta miƙe ta bar office ɗin tayi waje.

Bayan ta gaishe shi ne ya fara mata maganan yadda auren ya taso sannan ya bata haƙuri na gaggawan da aka mata, Aunty hauwa ce mishi tayi babu komai ae sun isa da ita ne, amma tana maganan tana kuka, jin haka yasa Baba yayita saka mata albarka daga baya yayi mata nasiha sosai, wanda har saida sautin kukanta ya dinga fitowa, suna gama wayan ta ƙira Ummi har lokacin kuka ta keyi, itama Ummin haƙuri tayita bata tana rarrashinta da kalamai masu daɗin gaske, wanda Aunty hauwa ita kuma tayita mitan yayah zata iya zama da Abdallah bayan ya raina ta, itafa matar yayan shu ne kawai din raini yazo ya aureta?

Ita dai Ummi haƙuri ta ke bata chan ƙasa-ƙasa kuma tana dariyan hauwan da ta je ta maganan wai ya rainata, haka suka gama maganan Aunty hauwa ta koma ciki, nan kuma an kawo masu haihuwa har mutum uku, dole ta zage ta fara aiki.

Tunda Abdallah yaji an ɗaura mishi aure da hauwa, farin ciki ya taso shi gaba, jiki na rawa ya ƙaraso gida wurin Baban shi, inda shi kuma Baban ya fara mishi nasiha da yayi adalci a tsakanin matan na shi, kuma ya gaggauta gayawa fadilah abinda ya faru, sannan ya mishi nasiha sosai.

Abdallah yana fita a parlourn Baba ya ƙira fadila, cikin nutsuwa ya mata bayanin komai, amma abin mamaki bata nuna mishi damuwarta ba, kawai fatan Allah ya basu zaman lafiya tayi, daga baya ta tambaye shi yaushe zai dawo zaria? Jiki a sanyaye yagaya mata zuwa gobe ko jibi, haka sukayi sallama ya shige motar shi yayi cikin garin jos gidan Aunty Amina.

Washegari da safe Abdallah ko karyawa bai yiba ya kama hanyar garin bauchi, amarya tayi ƙira, tunda yaje yake ƙiran wayarta amma firr taƙi ɗagawa, yananan ƙofar gidan saiga Dr ya fito wurin 9:00am zai wuce office, mamakin ganin Abdallah yayi a kofar gidan, cikin mamaki yace, "Hauwan bata san kazo bane?" ya tambaye shi da sauri, yana murmushi kanshi a ƙasa yace, "yanzu na iso ina shirin ƙiranta kenan", Abdallah ya faɗa yana ɗaga wayan shi alaman zai ƙirata.

Da sauri Dr ya koma ciki, inda ya tarar da Aunty hauwa a tsaye gaban dinning tana tattare kayan da yayi breakfast da su, "mantuwa kayi Dr"? "babu wallahi, kawai na fita sai naga mijin yarinyar nan Abdallah tsaye a ƙofar gidan, daga dukkan alama ya nemeta taƙi fitowane, don daga gani ya daɗe a ƙofar gidan", ya faɗa yana wucewa zuwa ɗakin su Aunty hauwa, daga ƙofar ɗakin ya tsaya yana ƙiran sunan ta, amma firr tayi shiru kamar mai bacci taƙi amsawa, ganin haka Aunty uwani ta shiga.

Ganin bazata fitoba yasaka shi shiga ɗakin ranshi a ɓace, kaman zai wanka mata mari yake mata masifah, "ke hauwa wa kika ɗauka yaronki ne a gidan nan? Kinsan Allah idan raina ya gama ɓaci bansan me zan miki ba, banzar yarinya mai masifar tsiya, ke har kin isa iyayen mu su zartar da abu kidawo kina nuna basu isa ba? Ke wacece? Wuce kifita kije wurin mijinki kafin na nuna miki ɗayan halina ɗin".

Fuska a É—aure ta fita wurin Abdallan, shi kuma Dr yazo ya mishi tasss akan kada ya fara sakewan da Hauwa zata raina shi, gara ya rage nuna mata damuwan shi akanta kafin raini ya biyo baya.
Chapter 49 · 0% Book details