← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 66

Sashe 46

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙofar gida kuma tun Baban Narabi da Bappah suna rarrashin Abba har suka gajji suka zuba mishi ido, sai addu'a kawai suke mishi a zuciyar su, uncle Baba ma gaba ɗaya ya shiga wani yanayi, da yake shiɗin dama mai rauni ne, ko gaisuwa aka musu sai ya share hawayen shi, a na ɗan ɗaukan wani lokaci kuma zai tashi ya shiga har ɗakin da Aunty hauwa ta ke zaune, har gabanta yake ƙarasawa ya tambayeta ko tana son wani abu? amma haka cikin kuka ta ke nuna mishi bata buƙatan komai, haka zai fito jiki a sanyaye.

Aisha kuma gaba ɗaya sai kukan rikici ta keyi wa mutane, firr ta ƙi karɓan kowa sai nida Hassan, idan taji yunwa mu haɗa mata tea tasha, mu sake fita da ita, nono kam zan ce a ranan bai fi sau uku muka kaita ta sha ba, shima tana sha, ƙafanta yana ɗaure akan cinyan ɗayan mu, saboda kada mu gudu mubarta.

Idan muna zaune a waje kuma duk yadda mutane abokanan Babanta suka zo, zasuyi tazo wurin su sai ta ƙi, idan kaga ta karɓi mutum toh daga ni da Hassan sai Abban mu, sai kuma Baban Narabi da wani ƙanin Baba Umar mai masifar kama da shi, duk inda yabi zaka ga tana ta bin shi da kallo, idan ya karɓeta kuma kuka zai fara, ya kifa kanshi akan ta yayita kuka, dole zakaji Baban Narabi yace, "Abdallah! Na haneka da zubar da hawaye wa ɗan'uwanka, shin ba addu'an mu Umar yafi buƙata ba? Don Allah ayi haƙuri da kukan nan, baka ga ita kanta Aishan kuka kuke sakata ba"? Haka Uncle Abdallah zai share hawayen shi, ya kuma kasa riƙe Aishan saidai ya miƙo mana ita, amma yana barin wurin kuma zata fara kuka, a dole Abba yace mu koma cikin gida da ita.

Rayuwa babu wuya, a kwana a tashi kwana sai tafiya yake tayi, yau har an wayi gari Baba Umar ya cika sati É—aya da rasuwa, inda kowa ya fara shirin tafiya.

Baba Umar shine babba a wurin mahaifiyar su da mahaifin su, sannan aka haifi mace tukun Uncle Abdallah, sannan aka sake haihuwar wata macen, a lokacin kuma Baban Narabi ya ƙara aure da wata ƴar cikin Narabin, inda suka sake haihuwa tare da mama Aisha, bayan ta haifi yara mata guda biyu, wanda ƙaramar su itace sa'ar Aunty hauwa, wacce taje musu hutu lagos, wato indo, a haihuwarta maman su Allah ya karɓi ranta, inda aka maida sunan maman su.

Aunty Amina ita ke bin Baba Umar wanda yanzu ta ke aure a cikin jos, sai uncle Abdallah, sai Aunty Hadiza wanda ita ma ta ke aure cikin garin jos É—in, sai mai bi mata kuma Aunty Umaimah, wanda ta ke aure a cikin garin bauchi, duk cikin su mijinta yafi wadata sosai, sai Æ´ar auta kuma Aunty indo, wanda itama ake shirin auren ta kwanan nan, da wani É—an Azare, amma mazauna garin kano, shiÉ—in kuma abokin uncle Abdallah ne.

ÆŠayan É—akin kuma, wanda take amaryar Baban narabi mai suna Baba kaltum, tana da yara guda huÉ—u, babban su shine, uncle sabo, wanda shi sa'an Aunty umaima ne, sai mata uku da suka biyo bayan shi,Aunty asma'u, Aunty Nana khadija, Aunty Zahra, duk gidan basu da irin halin Æ´an ubancin nan, don ko kaÉ—an Baban Narabi bai yadda da wannan a gidan shi ba, shi mutum ne mai tsayin daka a gidan shi sosai,.

A ranan su Bappah suka koma misau, inda Bappah ya gana da Baban Narabi cewa Aunty hauwa idan tayi 40dys za su maida ita gida, amma Baban Narabi bai amince ba, lokaci guda hawayen da ya daɗe yana ɓoye su cikin mutane suka fara zuba, yana duban Bappah yace, "Ni da nafi son tayi takabanta gaba ɗaya a ɗakinta, yanzu haka shawaran da muka yanke da ƴan'uwan Umar zata koma gefen shi Umar ɗin, zasu tafi da Indo,da kuma mata biyu wanda zasu tayata zama, kaman ɗaya daga gefen ko, sannan ita ma Uman shi tace zata zauna dasu har su gama takaban, amma idan kace zaku ɗauke ta sai maga kaman akwai kasawan mu", ya ƙarasa maganan hawaye yana zuba mishi babu kakkautawa.

"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wallahi ba haka nake nufi ba, amma tunda kun shawarta hakan babu komai, dama ita Maman suce zata zauna tare da ita, saboda haka duk yadda kuka tsara É—aya ne ae, ae ko babu Umar ae munzama É—aya, ga Aisha a tsakani", Bappah ya faÉ—a cikin yanayin shi na nutsuwa.

Haka sukayiwa Aunty hauwa sallama tana kuka suka tafi dukkan su, gidan yazama babu kowa sai mu, wanda muke shirin tafiya gobe, a ranan muka koma da Aunty hauwa gidanta, da yake tun kwana biyu su Aunty hauwa sukaje suka gyara gidan tsaf, ranan da aka koma Aunty hauwa da su Ummi na sun yi kukan rashin Baba Umar ba kaÉ—an ma.

Washe gari tun safe muka tafi domin zuwa airpot, Aunty hauwa tayi kuka lokacin da zamu tafi, rungume Ummi tayi tana ta kuka, gefe ɗaya kuma Umma Halima da Mama sai haƙuri suke bata, ita kuma Ummi bata iya cewa komai sai kukan da ta keyi, don zan iya cewa Ummi na tayi kukan da ko Aunty hauwa batayi shiba a rasuwan nan, domin cewa ta keyi, ciwon hauwa ae nata ne, kukan haiwa shima na ta ne, Abba fita yayi bai musu sallama ba, domin bazai iya ba, amma ya bada kuɗi mai yawan gaske a hannun Mama akan idan ya tafi ta bawa Aunty hauwa, suma su Maman da Umma halima ya basu masu yawa.

Lokacin da muka ajiye Aisha a parlourn zamu tafi, kuka ta fara nida Hassan sai muka kasa fita, muma kukan muke tayi muna tsaye muna kallon ta, a haka uncle Abdallah yayi sallama ya shigo, ganin kukan da mukeyi sai ya ɗauki Aisha da ganin shi ya sata tayi saurin hawa jikin shi ta kwanta tana ta ajiyan zuciya, hannun shi ɗaya ya saka ya riƙo mu muka fita waje inda motan uncle Abdallah ta ke, wanda dashi za' a kaimu airpot, uncle sabo ne zaune a mazaunin driver Abba yana gefen shi.

Muna tafiya Uncle Abdallah ya koma parlour ɗauke da Aisha a kafaɗan shi, zaunawa yayi suka gaisa da su Umma halima da suke ta share hawayen su, gefe ɗaya kuma Aunty hauwa ce a tsugune a ƙara ta rungume ƙafan Mama tana ta kuka mai ƙarfin gaske, kaman zuciyata zai fito.

Runtse idon shi yayi da ƙarfi na zuwa wani lokaci kuma ya buɗe su akan Aunty hauwa, ya daɗe yana duban ta kaman bazaice uffan ba, chan kuma ya ƙira sunan ta a hankali, " *HAUWA*"! bata amsa ba amma ta rage sautin kukan, bai sake cewa uffan ba har zuwa wani lokaci da yaji sautin kukan nata ya ragu sosai.

Juyawa yayi ya dubi Umma halima yace, "Ummah ku ae haƙuri zakuna bata bawai idan kunga ta fara kuka kuma kuyita tayata ba, kukan rashin Yayah Umar idan muka ce yin shi zamuyi tayi, toh ina mai tabbatar muka har mu koma ga rabbana bazamu daina ba, domin shi ya zama mana wani jigo acikin rayuwar mu, kuma wani haske ne a cikin zuciyar kowanmu, toh manta shi a zuciyar mu abune mai matuƙar wahala, kuka bashi bane mafita addu'a ne zai zama muna mishi", yayi shiru yana bin kowa da ido, wanda umma halima tana share hawayen ta tana ta amsa mishi da hakane, daga nan ya juya yana duban Aunty hauwa a hankali yace, "Hauwa kina jina"? ɗaga kai tayi alaman taji, sannan ya ci gaba da kwantar musu da hankali yana ta nuna musu ƙarfin addu'a da haƙuri shi zai rage musu zafin a zuciyar su.

Nasiha sosai ya musu sannan ya miƙe ya tako har gaban Aunty hauwa ya sunkuya hannun shi riƙe da Aisha, jin ƙamshi turaren shi ya saka Aunty hauwa ɗago da kanta ta dube sho, zuciyarta ya buga da ƙarfi domin tsananin kaman da sukayi shida Baba umar, bambanci kawai yafi Baba Umar tsawo da farar fata, sannan Baba Umar mutum ne kowa ga fara'a da mutane, amma shi kuma Abdallah sai ya so ya ke kula mutane, kuma kullum fuskar shi a ɗaure ta ke tamau, baya wasa da kowa, a hankali ta mayar da idon ta ƙasa jin wani hawayen mai zafin gaske ya taho mata, don hattah muryar su iri ɗaya ne da yayan shin.

Miƙa mata Aisha yayi akan ta karɓeta, amma firr Aisha taƙi yadda kuka ma ta fara mishi alaman bazata je ba, ganin haka yayi murmushi ya lakuce kumatun Aishan, sannan ya dubi Aunty Hauwa yace, "toh bata nono tasha sai mutafi gidan Baban Narabi", girgiza kai tayi alaman bazata bata ba.

Hararanta yayi murya ƙasa-ƙasa yace, "dole kuma ki bata tasha abincinta, ko na ɓata miki rai", ya faɗa babu wasa a fuskar shi, ganin haka Aunty hauwa ta turo bakinta gaba ta miƙa hannu ta karɓi Aisha, sannan ta dube shi ta gefen ido tace, "toh ka tashi a kusa da ni mana", ta ƙarasa maganan tana murguɗa baki kaman zatayi kuka.

Kallonta yayi na wasu seconds, sannan ya miƙe ya koma gefen Umma halima ya zauna suka shiga magana da shi, wanda da wuya ka dinga jin muryan shi idan yana magana, kawai sai dai kai da kake hiran da shi ne zaka dinga jin muryan shin, ita kuma Mama tashi tayi ta wuce kitchen wurin Indo domin ta yata ɗaura abincin rana, wanda tun jiya Uncle Abdallah ya cika store ɗin da kayan abinci.

Hijab É—inta ta É—aga ta saka Aisha a ciki ta fara bata nonon ta cika, sannan kuma duk bayan wasu seconds sai ta share hawayenta, duk abinda ta keyi a fakaice Abdallah yana kallon ta, kuma zafin kukan da ta keyi ya keji, suna haka har Aisha ta sake nonon ta É—ago da kanta da ya cika da zufa tana kallon Abdallah, da gwalantayin ta ce ,"Dada"! Da sauri ya dubeta yana tambayan Aunty hauwa wai me ta ke faÉ—a ne?
Chapter 46 · 0% Book details