← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 66

Sashe 13

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon fuskar shi na yi da nufin zan ƙwace hannu na, amma ganin yanayin fuskan na shi sai na nutsu na cigaba da bin shi a hankali, muna zuwa dab da Dr Abdallah, kawai sai yaja ya tsaya yana miƙawa Dr Hussain bakin shi ɗauke da murmushi, hannu Dr na ya miƙa amma fuskar shi bai ko sa ke ba, sai wani ƙara tantame ta da ya yi, suna gaisawa Dr Hussain ya ja hannu na da sauri muka shige ɗakin da Amal ta ke ciki, ko jiran mai Dr Abdallah ya ke faɗa mun bamu yi ba.

Muna shiga Amal ta harare ni ta kawar da kanta gefen da Dr ya ke tsaye tana gaishe shi, ita kuma nurse É—in da ta ke zaune ta tashi ta fita ta bar mu, dariya na yi ina kallon ta nace,

"to laifin me na yi kika ƙi kallo na ballanta na ki amsa gaisuwan da na ke yi miki?".

"ki koma da gaisuwan ki, tunda sai yanzu kika ga daman da wowa".
ta faɗa ta na ƙara ɗaure fuskan ta.

Kallon Dr na yi da yake zaune a wani 2sitter da yake gefen gadon ta yana ta daddana wayan shi, bai ko kalle mu ba, dariya na yi na koma gefen shi na zauna ina cewa,

"Dr'n mu don Allah ka bata haƙuri, ka gaya mata kaine kace muje cin abinci shi yasa ma ban dawo ba ko".
na faɗa ina neman shi ma ya ƙara na shi bayanin.

Kallon ta yayi ba tare da yace mata uffan ba, sai na ji tana cewa,
"Allah ya soki kinci Albarka cin Dr, amma da yau nayi fushi da ke, kinsan ɗazu ƙafana su kayi ta ciwo, har saida aka mun allura kusan guda biyu, kuma Abbu zasu iso wurin 7:30pm, shi yasa duk na damu da rashin ki".

Haƙuri na bata nace mata ina nan har 9:00 insha'Allahu, sannan na matsa kusa da Dr ina leƙa abinda ya keyi a cikin wayan shi.

Juyowa ya yi kaÉ—an ya dube ni ta gefen idon shi, baice komai ba ya cigaba da abinda ya ke yi cikin wayan na shi, a hankali nace,

"Dr nah bani nima nayi game É—in Angellah É—in".

bai kula ni ba ya cigaba da dannan wayan shi, ba'a ɗauki lokaci ba muka ji buɗe ƙofa da shigowan Dr Abdallah, ina ganin Dr babu shiri ya saka hannun shi ya matso dani kusa da shi sosai, yana miƙo mun wayan yana cewa,

"Babyn baby zo ki buga naga irin naki ƙwarewan? Idan kin kaini to zan miki kyautan ban mamaki, idan kuma na fiki to zaki mun kyautan duk abinda na faɗa".
nima murmushin na keyi na karɓi wayan ina buga game ɗin, ko in da Dr Abdallah ya ke ban kalla ba.

Juyawa ya yi ya bar kallon mu, idon shi ya maida kan Amal yana gaya mata isowan su Abbu, yanzu zai wuce airpot, amma wurin 7:30 zasu shigo hospital É—in, yana gama faÉ—a ya juya da sauri ya fita.

Da ido Dr Hussain ya bishi, sannan ya maido da hankalin shi kaina, a hankali yace, "bari na fita mosque nayi sallan magarib da isha, idan na idar zan dawo".

Amsa mishi da kaina ina miƙa mishi wayan, kallo na yayi kaɗan kafin ya saka hannun shi ya karɓa ya fita a ɗakin.

Dawo da kallo na nayi kan Amal ina murmushi nace, "sis ya ya jikin dai?".

Harara na tayi ta ce, "ban sani ba, sai da ki ka gama soyayyan ki da Dr Hussain bayan ya tafi tukun zaki dawo nuna mun kulawan ƙarya".

BuÉ—e baki nayi ina dariya nace,
" me yasa baki yadda da cewa babu komai tsakanin mu da shi ba? Mutumin da yake da mata da buhu-buhun Æ´an mata kyawawa mai zai yi dani Æ´ar cukulan nan?".

"Za kuji da shi ai daga ke har shi É—in, mutumin da ake cewa ko cikin lectures Æ´an uwan shi baya kula su, amma ke gaba É—aya ya É—auki time É—in shi yana baki, kuma har yana fita da ke, yana kuma biye duk wasu shirmen ki, amma kina raina mun hankali wai babu komai tsakanin ku? To kada ki gaya mun, a barshi idan ya yi tsami zanji ai".

Kama baki na yi ina hararan ta, " amma Amal baki da hankali, ki rasa da wanda zaki ce ina soyayya sai da wanda yayi kusan haihiwa na? Bakiga yayi mun girma bane? ak wannan wayo zai na mun isan na aure shi, kawai dai muna shiri ne ki gane hakan".

"Zan gane ai ranan da duk nagan ki a gidan shi".
ta faÉ—a tana kuma tana kwanciya.

Dariya na yi ban ce mata komai ba, sai tashi da nayi na shiga toilet É—in nayi alwala domin yin sallan magrib.

Wallahi yau bazan iya typing mai yawa ba, duk a gajeye na ke, kuyi haƙuri da wannan.

_*JIKAR KULU, WANNAN SHAFIN NAKI NE KYAUTA NA BAKI, DUK YADDA KI KE SO KIYI DA SHI, NAGODE DA ƘOƘARIN DA KI KE MUN, ALLAH YA BAR ZUMUNCI.*_

*©AUNTY NICE CE* ✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

_*HAUWA ALHASSAN YUNUS, WANNAN SHAFIN NAKI NE KYAUTA AUNTY NICE TA BAKI, DOMIN TUKWUICI NE DAGA IRIN COMMENT ÆŠIN DA KIKAYI, NAJI DAÆŠI ALLAH YA BAR ZUMUNCI*_

*SHAFI NA 9📑*

*__________📖* Hararan ta na yi ina kaɗa kaina alaman ta faɗi ba dai-dai ba, amma dai bazan kula ta ba, ina duban fuskan Amal da ta rufe kaman mai bacci, amma wani munafukin murmushi ne ƙunshe a fuskar ta, ni kuma sai bin ta da harara na ke yi, can naga abun na ta ya yi yawa, ina hararan ta nace.

"Amal idan kinsan kin warke munafurci ne a zuciyar ki, to ki faÉ—a na tashi na ta fi, amma kin sa kani a gaba sai murmushin munafurci ki ke yi?"

Dariya ne ya kufce ma Amal, daga gani irin wanda ba ta shirya yi ba ne, buɗe ido na yi na ƙura mata ina kallon ta baki na a buɗe, ganin yadda na yi kawai sai ta sake fashewa da dariya.

"Haba Hummy na ƴar rikici, idan ban yi dariyan drammer ko da Dr ba, to dariyan me zanyi? Gaba ɗaya son junan ku ya muku yawa amma kun kasa ganewa, sai wani kishin juna ku ke yi, yau ayi fushi gobe ayi faɗa, amma dai na yi shiru tunda kin ce babu soyayya a tsakanin ki da tsoho, sai ki saurari Dr Abdallah don shi ma na lura yana miki ƙauna zalla".
ta faÉ—a tana ci gaba da dariyan ta.

Tashi nayi nai hanyar waje ina cewa, "na ta fi gida sai ranan da cutan gulman ya sake ki sai na dawo, yarinya in banda shirme, me zanyi da Dr wanda ya mun tsufa, kuma don lalacewa mai matan ki ke mun fata, gaskiya ni kin gama da ni".
Na fita a ɗakin da sauri saboda muryan dariyan Amal da naji ya ƙaru.

Ina shiga compound É—in mu na hango shi ya buÉ—e motan shi zai É—auki abu a ciki, hararan shi nayi a zuciya ta ina cewa,
"in banda tunani irin na Amal wannan mutumin kam ai kaÉ—an ne ya hana shi ya haife ni, amma ta ke ga kaman muna soyayya? Nikam sun kasa fahimta ta ne, burge ni kawai ya ke yi, kuma yana mun kyau amma bana mishi son da suke tunani".
ina ganin ya juyo nayi sauri na É—aga mishi hannu sannan na shiga gida na.

2:00pm naji text ya shigo waya na, da sauri na jawo wayan na duba, "ki fito muje lunch da kika mun alƙawarin zamuje".
da ga Dr Hussain text É—in ya shigo.

Tashi na yi na sa ke yin wanka, wani material gown na saka, baƙi ne mai jajayen flower a jiki, ban ɗaura ɗankwalin kayan ba, na ɗauko red ɗin ƙaramin gyale na yafa a kaina, wanda tuntun gashi na ya ƙara ƙawata yafa mayafin, gashi duk in da na juya sai ƙamshi mai masifar daɗi na ke yi.

Jikin mirrow na koma na sake kallon kaina, ina juyawa ina kallon kaina da sha'awa, a fili nace, "yau kam nasan Dr Hussain zai ce kaiii Hummy kinyi kyau".

ina faɗa ina dariya saboda ni kaina nasan ba ƙaramin kyau na yi ba, ina cikin kallon kaina na ji ƙiran shi ya shigo waya na, ban ɗauka ba nayi sauri na ɗauki pouse ɗina red na riƙe a hannu bayan na jefa handset ɗina a ciki na fita.

Ina fita na hango shi tsaye suna gaisawa da su David, wanda daga dukkan alamu daga service suka fito, cike da mamaki na ke duban shi, domin shima baƙin jeans da red polo ya saka, ƙafan shi ɗaure da baƙin sandal mai kyau, ga glass ɗin shi daya yi matuƙar ƙawata fuskan shi ɗane a fuskar shi.

Ƙura mun ido suka yi ganin na tsaya da tafiyan, shima yau ina ganin shi sai da ya daɗe yana kallo na tukun ya maida kallon shi kan wayan hannun shi, Peter ne yace,

"kai Preety wankan ki ya yi kyau, kaman wata queen? gaskiya duk mijin da ya aure ki ya more da mata mai kyau, don za kiyi ta haifa mishi kyawawan yara".

murmushi na yi ina kallon Dr don jiran shi kuma mai zai ce, amma bai ce mana komai ba, sai kallon Peter ya yi kaÉ—an sannan ya maida kanshi kan handset É—in shi, ganin haka David yayi É—an murmushi ya dube ni yace.

"Ki rabu da Peter ki zo ki shiga mota ku fita, haka ya ke duk in da yaga abu mai kyau sai yayi magana, kaman wacce zai aura ba kyakkyawa ba".
Chapter 13 · 0% Book details