← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 66

Sashe 52

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh ki ajiye anan zamu kwana" ya faɗa bayan ya fita yana tattara ledodin da suke bayan motan shi, ganin ya ƙura mata ido fuska a ɗaure tayi sauri ta buɗe motar ta fito.

Cikin hotel ɗin suka shiga hawa na biyu, inda taga ya ɗauko key ya buɗe ɗakin da yake number 38, haka tabi bayan shi suka shiga ɗakin da yake da matuƙar kyau da tsari, sai ƙamshi yakeyi ga wani sanyin AC da ya cika ɗakin, gefe ɗaya kuma sai ta ga wani jakan Abdallah a ajiye a gefen table ɗin ɗakin, ajiyan zuciya tayi ta nemi gefen gadon ta zauna a nutse idon ta yana kan Abdallah.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/29, 14:17] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1442H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https:/www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 42📑*

*__________📖* Uncle Abdallah jawo ledan da yayi musu take away yayi zuwa kusa da ita, "sauƙo muci abinci ƴan mata nah", kallon shi tayi ta juyar da kanta gefe, "nifa na ƙoshi, kawai ka mayar da ni Narabi na kwana achan wurin su Mama ƙarama".

Wani kallo ya bita da shi babu shiri ta sauƙo tana murguɗa mishi baki ta jawo nata take away ɗin ta fara chi, bai sake ɗaga kai ya kalleta ba har sai da ya gama chin na shi, tashi yayi ya ɗauki wayan shi ya fita a ɗakin, ita kuma ganin fitan shi yasa ta ja dogon tsaki tana furta, "ni wallahu baka isa ka takurani ba don kaga ina tsoronka, ni idan ba masifah bama ban taɓa ganin wanda nake jin shakkan shi irin wannnan mai fitinannen idon ba".

Miƙewa tayi ta ɗaura sauran abincin a saman fridge, bakin gadon ta koma ta zauna, tana zama yana shigowa ɗakin, ledan da yake ajiye a ƙasa ya miƙa mata ɗaya, "ki tashi ki shiga kiyi wanka, wannan kayan bacci ne", hararan shi tayi ta gefe, "an na taho da nawa kayan baccin".

Bai wani bata amsa ba sai juyowa da yayi ya kalle ta, babu shiri ta buɗe ta ɗauki kayan ciki da towel ta wuce toilet ɗin, wanka tayi da brush, sannan ta gyara jikinta a cikin toilet ɗin, duba kanta tayi ta mirrow, ganin kanta ya saka ta kama haɓanta tana faɗin, "mutumin nan nufin shi da wannan kaya mai kama da net ɗin zan kwanta da shi? Kuma a gaban shi"? Ɗaukan hijab ɗin ta da ta shigo dashi ta mayar jikinta, sannan ta buɗe ƙofan ta fito ɗakin.

Ko kallonta baiyi ba ya wuce ya shiga toilet ɗin, yana shiga tayi sauri ta ɗauki jakan kayanta, fito da turarukanta tayi ta shafa a dukkan jikinta sannan ta fesa hair spray a gashinta, gaba ɗaya fakin sai ya juye da ƙamshi mai daɗin gaske, tana gamawa ta ɗale kan gadon da sauri taja duvet ɗin ta rufe har kanta.

Yana fitowa yayi murmushi daya ganta kwance ta duƙunƙune, wucewa yayi ya saka kayan baccin shi masu matuƙar kyaun gaske, feshe jikin shi da turare nasu ƙamshin gaske yayi, taku kaɗan yayi ya hau kan gadon gefenta ya zauna.

Da sauri ta buɗe ido ta kalle shi, shima yayi sauri ya tamke fuskan shi, murya ciki-ciki yace, "tashi muyi sallah", yana faɗa ya miƙe ya ɗauki carpet ɗin ya shimfiɗa, kallon shi tayi taga babu hanyar jayayyah, kawai sai ta tashi ta ɗauki zaninta dayake jakanta ta ɗaura, hijab ɗin data naɗe ta ɗauka ta saka shi, sannan ta fesa turare a jikin kayan, binshi tayi sukayi sallah raka'a biyu, ya zauna ya dinga jera addu'o'i, suna idarwa ya tashi ya buɗe fridge ya ɗauko goran fresh milk ya wuce gefen gadon ya xauna, bayan ya buɗe ya cika mata glass cup ya miƙa mata, ganin yadda ya tamƙe fuskan har zuwa lokacin yasa ta karɓa babu musu, kafa kai tayi ta shanye, karɓan cup ɗin yayi ya ƙara cika mata, amma sai ta yi fuskan zata mishi kuka, "don Allah uncle na ƙoshi wallahi, kabar ni haka mana".

Hararanta yayi, "nine kuma yau uncle ɗinki? Bazan fasa miƙa miki ba, ki karɓa kada na nuna miki halina", ........babu yadda ta iya kawai ta karɓa ta fara sha a hankali, da ƙyar ta sha rabin cup ɗin, ta juyo tana duban shi cikin ƙaramar muryah, "uncle Abdallah don Allah kayi haƙuri ka barni haka wallahi na ƙoshi ne, kuma kaga dare yayi kada nayita cika cikina da abu".

Hannu ya saka ya karɓa, baice mata uffan ba ya shanye sauran wanda ta bari, sannan ya sake cika cup ɗin ya shanye, ita dai tana zaune har lokacin ta sunkuyar da kanta ƙasa kaman mai jiran a biya mata karatu.

Sun kai kusan 25mnt tukun yace mata ta gyara ta kwanta, babu musu tayi sauri ta ɗale gadon batare da ta cire hijab da zanin ba, "Hauwa meye haka zaki kwanta da hijab da zani kuma"?....... bai gama rufe bakin shi ba tayi sauri ta tashi ta cire su ta naɗe, duk abinda ta keyi idon shi yana kanta babu ƙiftawan ido.

Asuban fari Uncle Abdallah ya tashi cike da farin cikin kasancewar shi da Hauwa a daren jiya, kallon fuskarta da take bacci kawai yake cike da farin ciki, a zuciyar shi ji yake kamar tana tashi ya damƙa mata duk abinda ya mallaka, yana murmushi ya furta, "Hauwa ina sonki! Allah ya bani kyawawan yara masu kama da ke golden girl ɗina", ya miƙe yayi toilet fuskar shi cike da murmushi.

Murguɗa baki tayi bayan taga shigewan shi toilet ɗin, don tunda ya bar jikinta ya tashi ta farka, a bayyane ta furta, "jarababbe kawai, duk wani ɗaure fuskar kan ka na banza tunda bai hanaka cika wa mutum kunne da ihu ba, hawaye ko kamar ranan zai ƙarar da su, amma idan ka tashi a ɗauka kai zaki ne bayan"...... Sai kuma tayi shiru ita ɗaya tana murmushi don tuna wasu sirrikan zuciyar shi da yayi ta amayar mata a daren jiya.

Yana fitowa itama ta miƙe bata kalli inda yake ba ta wuce toilet ɗin, shi kuma har ta wuce binta da kallon yake yana murmushi.

Suna idar da sallah bayan sunyi azkhar sun karanta qur'ani, kawai sai ya miƙe a ƙasan wurin ya kwanta ya ɗaura kanshi akan cinyar ta, rigingine ya kwanta yana duban fuskarta, itama zuba mishi ido tayi tana kallon kyakkyawan idonshi daya sauƙe mata a kanta, murmushi yayi ya saka yatsan shi manuniya yana zagaya shape ɗin bakinta da shi a hankali, bata ce mishi uffanba sai hannun ta data saka cikin gashin kanshi tana shafawa.

"Hauwa ina sonki!" murmushi tayi tana duban shi, "ka gaya mun daga daren jiya zuwa yau yafi cikin buhu, na haddace su ka ƙara mun wani kuma", ta faɗa da yake hauwa barikinta baya gaya mata gaskiya, domin daga jiya zuwa yau tasan Abdallah dai-dai yake da ita, don duk yadda taso ta ƙi ba shi haɗin kai abin ya gagareta, Abdallah yasan ta kan mace wuce tunaninta.

Murmushi yayi mai ɗan sauti, ya dawo da hannunshi dai dai kan haɓanta inda ya ɗan lutsa kaɗan yace, "daɗinki yayi mun yawa hauwa nah, har ya kusa zautar dani", jin haka bata san lokacin da tayi sauri ta ture kanshi akan cinyarta ta miƙe zuwa kan gado tana faɗin, "nikan baka jin kunya na wallahi, ni ba haka nake nufin ka faɗa ba", hayewa gadon tayi tana rufe fuskanta.

Dariya yayi ya biyo bayanta yana cewa, "sweety akwai abinda zan faɗa mai daɗi da ya wuce hakan ne? Ba gashi kina neman na ƙara ba kin gudu kan gado don na biyoki ba, ni yau ban san ta yayah zaki barni na tafi zaria ba?" ya faɗa yana hayewa kan gadon, ita kuma buɗe baki tayi tana kallon shi, amma ganin zai jawota ya saka ta fara kokawa da shi tana cewa.

"Wayyo uncle Abdallah wallahi bance ina son ka ƙara ba, nifa na gajji ka tashi muyi wanka muje wurin Baba, kai kuma sai ka wuce kada kayi dare", yana ƙara jawota jikin shi yana dariya yace, "ni ae bazan iya tafiya ba gaskiya sai dake, don gaskiya ban gajji da faɗawa maliya ba".

Duk yadda taso ƙi amma babu yadda ta iya haka ta barshi ya sake maimaita wa, da kyar ya barta suka tashi sukayi wanka, bayan sun shirya suka wuce zuwa a sibiti wurin Baba, jikin Baba ɗa sauƙi zuwa yau, saboda haka ana sallan azahar uncle Abdallah ya yi sallama wa Baba, yayiwa Aunty hauwa ma da dole saida ta raka shi zuwa jikin motan shi, ita dai sai mamakin shi takeji na yadda duk wannan
fuskan shi yau babu, sai wani shagwaɓa ya ke mata shi baya so yayi nisa da ita, ita dai bata ce mishi komai ba sai mamakinshi kawai data keyi, haka ta lallaɓa shi ya tafi, ita kuma ta dawo cikin ɗakin inda suke zaune da Aunty Umaimah da tazo yau, kuma dama tare zasu juya da ita zuwa bauchi, Aunty umaimah sai tsokananta takeyi da matar so, ita dai batace mata uffan ba sai murmushi kawai ta keyi.

Uncle Abdallah da ƙyar ya daure yayi sati ɗaya ya taho zuwa Narabi ya duba jikin Baba da aka sallane shi yana gida, ko awa ɗaya baiyi ba ya wuce bauchi, ranan Aunty hauwa sai da ta raina kanta, don tunda Uncle Abdallah yazo ya ɗauke ta bata samu hutu ba, har saida ta fara nuna mishi zatayi kuka tukun ya sarara mata, ga duk inda tayi idonshi yana kanta kaman wani tsohun maye.

Da kyar ya barta wurin ƙarfe tara na dare suka zo gida domin ta ɗauki kaya, Aunty uwani tana ganinta ta fara dariya, suna shiga ɗakin Aunty uwani, Aunty hauwa ta turo baki gaba kaman zatayi kuka tace, "Aunty nifa gaskiya bazan bishi ba, kisan dabaran da zakiyi ya tafi, ni na gajji sosai".
Chapter 52 · 0% Book details