← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 66

Sashe 22

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*__________📖* Gari na wayewa muka haɗa break, a wani food wormer na zuba na Dr, mu kuma mukaci namu da sauri, muna fitowa muka samu Dr shima yana buɗe motan shi, bayan yagama duk abinda zai yi ya matso kusa da mu, muka shiga kowan mu ya gaishe shi, muna isa school na miƙa mishi breakfast ɗin shi, mu kuma muka wuce class.

Mr Solomon ya shigo mana cost accounting, bayan ya gama lectures yace next week muna da test, duk sai mukaji kanmu ya É—au zafi, kowa ya fara maida hankalin shi kan karatu.

Dr Khadijah ce ta shigo mana ta saka wani yellow sarii, sai wani ƙamshi ta keyi mai masifan daɗi ga wani yauƙi da ta keyi kamar tarwaɗa, ina ganinta naji raina ya ɓaci, amma babu yadda na iya haka muka zauna muna binta, muna haɗa ido zata mun wani smilling, a zuciyata nace, "kazar mayu kawai, tanata wani smilling irin na neman gindin zama, irin ga ƴar uwar miji", tsaki nayi a fili wanda bansan nayi ba ma, har saida Amal ta taka mun ƙafa.

Tana gamawa Dr Hussain yana shigowa, sai wani smilling ta ke mishi lokacin da zata fita, amma shi kaman bai san da ruwan tsironta a wurin ba, amma ita abin haushi sai rangaÉ—i ta keyi.

Yana gama lectures yace mu shirya test É—inshi next week monday, yana fita bai daÉ—e ba naji wayata tayi haske, ina dubawa naga txt É—in shi ya shigo, da sauri na buÉ—e ina muushin ganin abinda ya turo,

_"babyn baby ya naga kaman maganan test É—in nan ya firgita ki? Kada ki rasana babyn ki zai koya miki komai"_

muna tashi Dr yazo É—aukan mu, muna fitowa muka ga Dr Khadija ta fito da sauri ta biyo shi, ganin haka yasa naja na tsaya saboda naga kaman Dr Hussain masifa yake mata, ita kuma ta tsaya a gaban shi kaman zatayi kuka, yana gama maganan ya nuna mu fuskan shi a É—aure yana cewa, " baby kuzo mu wuce gida".

Take-away ya mana muka wuce gida, da yamma ya ƙirani a waya akan na fito na same shi a wurin da muke karatu, wanka na shiga nayi, ina fitowa na yi shiga mai kyau, sai ƙamshi nake zuba mai daɗin gaske.

Cake na ɗauka na tafi mishi da shi, bayan na haɗa da juice na coconut da muka haɗa da kanmu, ina kai mishi ya karɓa yana murmushi, ajiyewa yayi a gefe yana kallona da murmushi yace, "Baby mai kika yiwa babyn ki ne"?

Buɗe mishi plet ɗin nayi ina murmushi, ɗaukan ɗaya nayi na miƙa mishi, "Dr mu muna dawowa fah mukayi baking wannan, Allah yasa ya maka daɗi", na faɗa ina binshi da murmushi.

"Allah yasa ba jagwalgwale kika mana ba" ya faÉ—a yana tauna cake É—in yana murmushi, hararan shi nayi na murguÉ—a baki na.

"Dr Khadija inaga tayi kusan 5yrs ko 6 tana sona, tun lokacin da muka je karatu na fahimci tana sona amma bata samu fuskana a lokacin ba, saida muka dawo daga karatu, a lokacin gidan da aka bani a staff queters itace neighbour nah, yau da gobe na bata fuska muka fara gaisawa, har wataran takan nemi alfarman na shiga da ita school, na amince mata, kawai sai ta takura rayuwata, duk inda nayi tana bibiyata, ni kuma ganin zata ta kura ni sai nazo na kama wannan gidan, nagaya mata nayi aure daga country ɗinmu, a wancan shekarun sai na samu sauƙin ta, amma yanzu kusan 2yrs ta na neman ta kurani, shiyasa nake ƙin amsa gaisuwan ta, domin akwai uncle ɗinta, daya same ni akan ta amma na nuna mishi ina da mata kuma bana ra'ayin zama da two wifes, toh abin yayi ɗan sauƙi, saidai daga zuwanki naga alaman tana neman dawo da abin baya, wanda idan kin kwantar da hankalin ki bazan taɓa cewa ina sonta ba".

"toh meyasa na ganku a wannan mall É—in ranan tare? Kuma me yasa kake tafiya chan ka kwana"?

Murmushi yayi yana kallona, "wallahi idan kin yadda a wurin muka haɗu da ita, kuma na koma gidan ne saboda naga alaman tana son neman inda nake shiyasa wancan lokacin na koma na daɗe a wurin, shi ne lokacin da Daddyn ki ya kawo ki, tafiyan danayi na baya kuma ke kika mun laifi shiyasa nayi yaji", ya faɗa yana faɗaɗa murmushin shi, sannan ya ɗauki coconut juice ɗin ya sha, ina ganin shi ya runtse idon shi ya sauƙe a kaina, sannan yace, "Juice ɗin nan baimun daɗi ba, kaman sugar yayi yawa".

Hararan shi na sakeyi cikin wasa, "Drn mu toh ni bana son Dr Khadijan, ka daina kula ta".

"Duk yadda kika ce haka za ayi, nima bana sonta don bani da burin auren mace sama da É—aya".

Zaro ido nayi ina kallon shi da mamaki nace, "toh kana da matar ne dama"?

"ina dai shirin yi yanzu"...
"a ina zakayi auren? Wacece zaka aura"? Na tambaye shi cikin sauri.

"Uhmmm wata yarinya nagani nake so idan ta amince zan aure ta, yarinya ce amma haka nake son aurenta idan ta amince", ya faÉ—a yana dubana idon shi a kanne.

Miƙewa nayi zan tafi na bar shi a wurin, yayi charaf ya riƙo hannu na yana bina da kallon mamaki.

"nidai ka sake ni zan tafi gida", na faɗa ina buga ƙafa na a ƙasa kaman zan mishi kuka.

"Toh ae bamu gama labarin mu ba zaki tafi ki barni"?
ya faÉ—a yana dawo dani kan kujeran da na tashi.

"nidai bana son labarin, kaje ka auri duk matan duniyan ma ni bani da case da kai, kawai ka barni na tafi, bana son ganinka", na faÉ—a hawaye ya fara bin fuskana.

Tashi yayi da sauri ya tsaya yana riƙe da dukkan hannu na, cikin murya mai sanyi yace, "babu ruwanki da ni kuma ina zan saka kaina naji daɗi baby"?

"wurin matan da zaka aura wanda kake son so mana" na faÉ—a ina juyar da kaina gefe É—aya, bana son ganin face É—inshi.

Shiru yayi na wani ɗan lokaci kaman bazai tanka ba, ni kuma sai kuka na ke tayi, kuma har lokacin yana riƙe da hannu na.

"Baby zaki iya ƙarasa rayuwar ki da tsoho kaman ni? Baby zaki iya bani kafaɗan da zan jingino na share hawayena daya ki tsaya a rayuwata na tsawon wasu shekaru? Baby zaki bar zuciyar ki ma wannan tsohon da yayi miki zarra da nisa a shekaru"? Ya faɗa bayan ya kulle idon shi.

_Wayyo na gajji gaskiya yau, kumun haƙuri bazaku samu jin amsan Hummy ba a yau sai a wani karon, don zanyi hutu_

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 17📑*

*____________* 📖 Muna cikin haɗa girkin Amal ta kira brother'n ta Faisal, su ka shiga tsara yadda zasu dinga ɗaga hankalin Dr Hussain, ni dai sai dariya da sha'awan su kawai na keyi, domin a handsfree ta bar wayan, burge ni su keyi kaman wasu friends.

Ina sauraren su ina ɗan dariya ƙasa-kasa, can naji muryan Faisal yana cewa, "ina ƴan mata na ɗin? Bani ita naji muryan ta". dukkan mu dariya muka yi tukun ta miƙo mun wayan na kara a kunne na.

"Hello sweety".
ina dariya nima nace, "hello honey".

dukkan mu dariya muka yi, sannan ya dinga tsara mun yadda zan dinga amsan wayan shi a gaban Dr, haka muka yi ta hira har muka gama girkin mu, ƙamshi kam nasan ba gidan Dr ba, yau ina ga hatta gidan su Peter ma sai sun ji.

8:30pm dukkan mu mun yi wanka, dogon riga muka saka kowa ta yafa É—an gyalen kayan, É—iban abincin muka yi dukkan mu muka fita zuwa gidan Dr.

Bamu daɗe muna knocking ba yazo ya buɗe mana, har zuwa lokacin fuskar shi a ɗaure, haka ya bamu hanya muka kai abincin har kan dinning ɗin shi, wucewa ya yi parlor ya cigaba da kallon shi ba tare da ya kalli in da muke ba, ganin haka Amal ta mun signa, dariya nayi na wuce in da yake na zauna a hannun kujeran ina leƙa fuskan shi ina murmushi.

"Babyn baby yau na maka girki mai daÉ—i, taso muje na zuba maka kaji daÉ—in shi".

harara na ya yi sannan ya juya ya kalli in da Amal ta ke zaune, ganin hankalin ta yana kan wayan ta sai ya dube ni yace, "bazan ci ba ni na ƙoshi".

"Haba baby'n baby! Ko ka fiso yau na kwana banci komai ba? Kuma na kwana ina kuka?".
Na faÉ—a kaman zan fara mishi kukan a lokacin.

Sa ke duban in da Amal ta ke ya yi sannan yace,
"baki damu da ni ba ai, to me yasa zaki damu da cin abinci na?".

"Duk duniya ba bu wanda ya damu da kai bayan ni, kuma na damu naga kaci ka ƙoshi, saboda nafi so na dinga ganin ka cikin kwanciyar hankali".
na faÉ—a ina tashi tsaye domin mu wuce dinning É—in.

Tashi ya yi ya tsaya yana kallo na ido cikin ido yace, "waye darling forever?".

Juya ido na nayi sannan na lumshe su na buÉ—e,
"nafi damuwa da naga kaci ka ƙoshi sama da maganan darling forever, saboda haka muje na samu nutsuwan ka tukun kafin wani ya biyo baya".

Amal ta riga mu gama cin abincin, sai ta koma cikin parlon ta zauna jiran mu, channels ɗin ta ke ta canjawa, muna gama ci na miƙe zan tafi, da sauri yace,

"dawo ki bani labarin shi, kuma daga yau idan kungama girkin ki kirani a waya zan zo gidan ku kawai muna ci acan, bazan so ku wahala kullum wurin É—aukan kaya ba".
ya faɗa yana sauƙe mun kyawawan idon shi a kaina.
Chapter 22 · 0% Book details