← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 66

Sashe 63

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutumin da ake ƙiran shi Abban Aisha shine ya saka hannu yana share hawaye ya riƙe ni, a taushashe yace, "kayi haƙuri mohd, Aisha ta amsa ƙiran wanda yafi mu sonta, kayi haƙuri kaje kamata addu'a yanzu za'a sallaceta", yana gama faɗin haka na juya na fita a parlourn, har inda ake shiryata na shiga, sunkuyawa nayi kan gawanta da nufin yi mata addu'a, amma sai zuciyata tayi rauni, kuka na saka ina riƙe da ita, da ƙyar na daure na mata addu'a, ina riƙe da ita naji maganan Aunty hauwa tana kuka, "shikenan Aisha bazamu rayu da ke irin na uwa da ƴarta bake nan har abada, da gaske mutuwa kikayi Aisha?" miƙewa nayi na bar wurin saboda wasu surutai da Aunty hauwa take tayin su babu tsayawa.

Kwanan Aisha bakwai da rasuwa kowa ya watse, a ranan kuma akayi sunan yarinyar da ta haifa, wanda taci sunan Aishan, amma mukayi mata laƙabi da Humairah!", dakatawa Daddy yayi da bamu tarihin shi ya ɗago da fuskana da nake ta kuka tunjin lokacin da Daddy na ya fara kuka, ƙura mun ido yayi yana ɗan murmushi yace.

"Sweet heart! kece yarinyar da Aisha ta haifa mun, kece farin cikina sama da komai a duniyata, kece farin cikin zama dake ya maye gurɓin baƙin cikin da na shiga a rayuwar baya", sannan ya juya ya nuna mun Dr Hussain yace, "wannan shine ɗan'uwan mamanki da take burin zaki nemo mata shi, gashi kuma kin nemo shin, wanda soyayyah ya shiga tsakanin ki da shi har ta kai ku da tunanin aure, ni dai zan cigaba da baku labarin yadda na reniki, daga baya zamuyi tambayan shin akwai aure tsakaninki da ɗan'uwan mahaifiyar ki? Kuma wanda yayi soyayyah da ita"?

Da sauri na juya na dubi Dr mu, duk sai najini a tsorace kada ace babu aure tsakanin mu da baby, amma sai kawai naga ya kashe mun ido ya mun alaman kada na razana, a hankali kuma naga saitin bakin shi yayi alamar furta mun, "I luv u babyn baby"! Murmushi nayi na maida kaina inda Daddy ya cigaba da bayanin shi.

Washe garin sunan Hummy su Ummi sukayi shirin tafiya da ita, amma da ƙyar na daure suka ɗauke ta, bayan na ɗaura ta akan cinya na ina duban tsantsan kaman da sukayi da Aisha, wanda har tsoro yake ban, nayi mata addu'a ina kuka kaman zan shiɗe, a haka Babana ya saka hannu ya ɗauke ta ya miƙawa Ummi da ita ma kukan take tayi.

Amma abin mamaki lokacin da suka isa bauchi sai Ummi ta ɗauki Humaira ta ɗaura akan cinyar Aunty hauwa, tana dubanta tace, "hauwa bazan tauye ki a karo na biyu ba, ki riƙe ƴar Aisha ko zaki ɗan samu sauƙi a zuciyarki kada abin ya haɗu ya miki yawa, ni kuma zanji da jinyar da yake damuna, don tabbas rashin Aisha wani giɓi ne na lafiya a jikina, inaga banida ƙarfi da kuzari a zuciyata na iya wani abu mai muhimmanci, don idan naji kukar ƴar nan, zai iya tarwatsa mun zuciya na", ta ƙarasa maganan tana share hawayenta.

Ita kuma Aunty hauwa bata ƙi ba, haka suka ƙira ni ita da Uncle Abdallah suka gaya mun zasu tafi da Humairah, ban ƙi ba don nima ina maijin tausayin Aunty hauwa ba kaɗan ba, daba don Aisha tace tafi son riƙon Humaira a hannu na ba da babu abinda zai hanani barwa Aunty hauwa, haka naje na musu sallama, na ɗauki makuɗan kuɗaɗe na bawa Aunty hauwa domin sayen madara dasu pampers ko wani abu da zai taso a sayawa Humaira, amma ranan naga kalan masifar Aunty Hauwa da Aisha ke bani labari.

Dariya Daddy yayi yana duban Dr Hussain da shima dariyan yakeyi, ni kuma na zunɓuro baki ina kallon Daddy, don babu shakkah nasan halin irin masifar Kaka, don idan tazo dubani kullum sai tayi masifar wai su yayah Ahmad basu da mutunci, har sai Goggo mai raino na tayita bata haƙuri takeyin shiru, wani lokacin ceea zatayi ɗakin su zataje ta tsitstsigale su, nidai dariyanta zan tayi har ta huce, nima dariyan nayi ina duban Daddy da yake tayi kaman ba yanzu ya gama kuka ba.

"Aunty hauwa ranan ta balbaleni inda take cewa mai na mayar da ita, Æ´ar Aishan ne zance zan biya ta ciyar da ita?" daga nan kuma sai ta fashe da kuka tana cewa, "me nayiwa Aisha a rayuwar duniya wanda uwa ta keyiwa Æ´arta bayan shayarwa? Duk fa Ummi nane rayi mun hidiman da uwa ta keyiwa Æ´arta, gashi Aisha ta bar duniyan ban nuna mata irin nawa soyayyah ba don ina jin kunyar Ummi na, don Allah kabarni na nunawa Humaira irin soyayyar da uwa ta keyiwa É—iyarta", dole na mayar da kuÉ—ina bayan na zauna na tayata kukan, ina ji ina gani aka tafi mun da sweet heart É—ina.

Da ƙyar na daure sukayi 5month da tafiya nabi bayan su, haka naje na musu 2weeks, naji daɗin ganin irin kulawan da Aunty hauwa da ƴaƴanta suke bawa Hummy nah, kai hattah abokiyar zamanta Fadilah da ɗanta ba ƙaramun so sukeyiwa Hummy ba, haka na dawo cike da kewar ƴata.

Babu wuya a wurin Allah, hummy tana shirin cika 1yr Aunty hauwa ta gaya mun, ae babu ɓata lokaci nayi shirin tafiya tare da mahaifiyata wanda ta matsa da son zuwa ganin jikarta, ranan da muka isa naji farin cikin da bazan taɓa mantawa ba, domin Sweet heart na samu babu inda bata zuwa da ƙafarta, gashi ko ɗaya bata mun ƙiyuwa, cikin jin daɗi akayi partyn cika shekaranta ɗaya, inda mukayi ta ɗaukan pics da ita, kuma abin sha'awa duk inda na saka ƙafa na yarinyar nan sai ta bini, gashi bakinta ta iya furta, Papa, kaka, Dada, mama, wato uncle Abdallah ne papa, yadda su fatima suke ƙiranshi, Aunty hauwa kaka, ita da Aunty fadila, fatima kuma mama, don firr fati tace itace uwarta, ni kuma abin daɗi wai Dada, tana nufin Daddy, naji daɗin da nakasa ɓoyewa a gaban kowa.

Abin haushi da iyalaina suka mun shine ina dawowa nigeria, jikina yana rawa na kai musu pics ɗin Humaira su ganta, amma buɗan bakin maman su Ahmad sai cewa tayi, "kana tunanin cewa ƴaƴana suna da wata chan ƴar ubane? ae sam kada ka fara gigin haɗa su da ƴar matar ka, don kuwa inada labarin bawai ƴar ka bace ƴar matar kane wanda tazo da cikinta gidan nan, domin babu abinda ya haɗa yarana da ƴar ta, babu abinda zai saka mu kalli photon ta chan ta matse muku", tana gama maganan ta bar mun wurin da nake zaune, yaranta kuma suka bi bayanta, ranan nayi kuka kaman raina zai fita, amma haka na bawa kaina haƙuri na shige ɗakina, zuciyana cike yake da tausayin Humaira.

Kasa zama nayi a ɗakuna na wuce chan ɗakin Aisha, inda na fara bin ɗakin da kallo, chan kan dressing mirrow ɗinta na ɗauko wani paper na buɗe, kawai sai ganin saƙon da ta bar nagani.

"Baban Ahmad don Allah nabaka amanan abinda zan haifa, idan namijine kasaka sunan Yayah Hussain, idan mace ce ka saka mata sunana don tunawa dani, kuma bana son kabada riƙon ta wa kowa idan ba a hannunka ba, bana so taje ko'ina da sunan hutu don gudun abinda ya faru dani kada ya faru da ita, Kagayawa Ummi da Aunty hauwa duk mai son ganinta yazo har inda take ya ganta amma ban amince ka kaita inda suke ba, zumuncin yanzu shaiɗan ya shiga, ina tsoron wani yayi mata illar da nawa ɗan'uwan da nake ganin ciki ɗaya muka fito ya mun, bana so kabari rayi sabo da kowani cousin ɗita, ban yadda da kowa ba banda yayah Hussain ɗina, sannan kada kabar matar ka da yaranta su wulaƙanta mun ƴata ko ɗana, don kullum sai ta furta mun na kawo musu cikin shege gidan su, kona rana ɗaya bana son ta zauna a hannunta, kasama mata mai kula da ita mai hankali dattijuwa, nagode Allah ya musu albarka".

A hankali Daddy ya maido da kallon shi kaina yace, "sweet heart kinji tushen da ban barki kin shaƙu da kowa ba, don bin umurni da kuma shawarar mamanki, nima sai naji ina gudun kije wani wurin don kada ki wulaƙanta, kuma ko a gidana ɗana lura basu sonki sqi ban barki da suba, kiyi haƙuri kinji", ya faɗa yana shafah kaina, nima murmushi nayi bayan na mike zaune ina share hawayen ido na nace.

"Daddy! amma mummy na da ta rayu dani baƙa ramin so da kulawa zata nuna mun ba, gashi Allah ya amshi addu'anta na nemo mata yayah Hussain ɗinta, kuma shi kona rana ɗaya bai taɓa nufina da niyyan cutarwa ba, kullum ma ƙara nuna mun hatsarin zuwa inda maza suke yakeyi, ashe zuciyar Drn mu mai kyau ne tun asali", na faɗa ina duban Dr da murmushi cike da fuskana.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
*°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1442H/2020M.*
*AL-MUHARRAM/SEPT.*
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 50🔚📑*

*__________📖* Shekaran Humairah biyu a hannun Aunty hauwa naje na taho da ita, ranan da zamu dawo na tausayawa Aunty hauwa da uncle Abdallah, domin kaman yara ƙanana, zama sukayi suna kuka kaman ance musu mutuwa tayi, haka na baraso cike da jin tausayin su, Fatima kuma ranan barin gidan tayi har saida na bar gidan tukun ta dawo.

Kafin na ɗauko Humairah dama akwai wata goghon mu wanda Allah bai taɓa bata haihuwa ba, ƙanwar mahaifin muce, kuma ita kaɗai mahaifiyarta ta haifa agidan su Baban mu, mijinta ya rasu, tou ita Baban mu yayiwa magana ta taho domin kula da Humairah, tadawo gidan da kwanaki kaɗan na taho ɗaukan Humairah, muna dawowa na danƙa mata amanan kula da Humaira, amma bawai na sakar mata komai na Humaira gaba ɗaya ba.
Chapter 63 · 0% Book details