← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 66

Sashe 16

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya na dingayi na daÉ—i wanda har sai da naji Dr ma ya fara dariyan, don yadda na kasa dainawa, ina wani jin daÉ—i a raina.

"Hummy'n mu kina jin daÉ—i ne?".
Ya tambaye ni murya a hankali cikin nutsuwa.

"Allah Dr'n mu yau daÉ—i na ke ji sosai, to yanzu zaka daina zuwa gidan ta ko? Kuma idan nayi kwalliya za ka ce ina da kyau?".

Rufe idon shi ya yi daga in da ya ke yana ta murmushi, shi kanshi ya rasa yau wace irin rana ce a wurin shi mai girman gaske, shi fa ko lokacin da yake tsokanan ƙanwar shi Aisha baya samun jin daɗi da nutsuwa irin yadda ya keji yanzu idan ya zolayi Hummy, ɗari bisa ɗari Hummy ta canja mishi tsarin rayuwar shi, da ko kaɗan baya jin sakewa a zuciyar shi, idan bai yi ƙarya ba ya kan yi good 1yr wani abu bai saka shi dariya ba, amma yanzu kullum ne, kuma ko wani lokaci sai ya yi dariya ko da shi kaɗai ne idan ya tuno ta a ranshi, yanzun ma wani dariyan yayi sannan yace.

"To ai ke yarinya ce Hummy, bazan iya ganin kyawun ki ba yanzu, ki bari sai kin girma sai na duba naga kina da kyawun, abu ɗaya kawai nasani yanzu, Hummy ta mai hankali ce, Hummy ta mai baiwar ilimi ce, Hummy ta mai sakalci da shagwaɓa ce, Hummy ta mai rikici na, wanda kullum sai ta birkita ƙwaƙwalwar Dr ta da rikici".

"Uhmm ni kan ban yadda ba, wallahi na girma Dr ni kam kace ina da kyau, kace na fi ko wacce mace kyau, Allah Dr'n mu har na kusa iso ka tsayi fa, idan na ƙara 2yrs fa tsayin mu zai zama ɗaya".

Yana murmushi mai sauti yace, "to mu bar shi ya kai 2yrs É—in sai na gaya miki a lokacin".

"To bazan sa ke kula ka ba sai lokacin, kuma kaima ba za ka sake kula kowa ba, sai ka jirani har lokacin".
ta faÉ—a kaman zata mishi kuka ta wayan.

"Wayyo Baby idan kin daina kula ni a mutuwa zan yi, kullum kuka zan ta miki fa Baby".
ya faÉ—a shima yana kwaikwayo na.

Dariya ya sa ka ni sannan nace, "Ba zaka mutu ba insha'Allah sai na girma kace Humaira ta fi sauran mata kyau, Humairah tafi ko wacce macce iya kwalliya da girki, Hummy kin fi Aisha kyau".
na faÉ—a ina rufe baki na.

Shima dariyan ya fara yana cewa, "Hummy har Aisha'n mu baki so nace ta fiki kyau? Lallai ina da aiki a gaba na, anya zaki bar ni na kalli wasu matan kuwa? Hala daga ranan da nace kin fi kowa kyau to ƙwalele na da ganin kowacce mace ko?".

Ina dariya na ce, "Dr'n mu na fiso kai ta ganin ni kaÉ—ai ce mai kyau a duniya, duk ranan da kaga kyawun wata to mutuwa zanyi".
na faÉ—a mishi jiki na a sanyaye.

Ajiyan zuciya ya yi bayan ya daÉ—e dayin shiru,
"Hummy na miki alƙawari duk ranan da nace kinfi sauran mata kyau to bazan sa ke ganin wata nace tana da kyau ba, bazan so ki mutu na zauna a duniya ba bu ke ba, na fi so na riga ki mutuwa, don ke nasan za ki iya riƙe mun yara na ko bayan bana duniya ko Hummy nah".

"To ai baka kawo mun su nagan su ba".
na faɗa ina mishi shagwaɓa.

Dariya ya yi yace, "Hummy kema ai bai wuce na yi rainon ki ba, shiyasa bazan kawo miki nawa yaran yanzu ba, don zasu haukata mun Æ´ar Baby na da na su irin rikicin, ni kuma yanzu karatu na ke so Baby'n baby ta yi".

"Ni dai naƙi wayon, ka kawo munsu a weekend, wallahi ina son yaran ka Dr".

"Nasani ai Baby, duk duniya ai babu wacce zata fiki son Æ´aÆ´ana sai dai Ummi na ta biyo bayan ki, amma bana son yanzu su wahalar mun da ke ne, don nafi damuwa da kiyi karatu sama da kula mun da yaran".

"Kana nufin ko Maman su ma na fita son su"?

"Kema ai Maman su ce, ko baki so suce miki Mama?".

Ina dariya na ce,
"kasan me nake so suce mun"?

"sai kin faÉ—a".

Ina dariya nace, "Mamie, saboda idan na girma na yi aure na haihu haka na ke so yarana su ce mun Mamie".
na ci gaba da dariyan alaman naji kunya.

Shiru ya yi na wani lokaci, sannan yace, "ni kuma Abbie ko? Hummy kin taɓa son wani ne a zuciyar ki?".

Shiru nayi, daga baya nace, "Dr ni ban san ya ya ake jin soyayyan ba, ai sai na girma tukun nasan yadda ake soyayya, kasan Daddy baya bari na naje ko ina, don baya son a cutar dani yace mun, kaga ni ko friends da maza ya hanani, ni kai kaɗai na taɓa sabawa da kai bayan Daddy na, sai na girma idan nayi saurayi zan gane, ko zaka gaya mun yadda akeyi tunda kai ka taɓa yi?".

"Irin wanda ki ke yi yanzu".

Dariya nayi nace, "Dr ance maka ina soyayya ne? Nifa bana kula kowa, kuma zaka na gani, Dr Abdallah ma da kace kada na kula shi, ai É—aure fuska na na keyi kaman na zama Boss".

Dariya ya yi tayi wanda har nima sai da na fara taya shi, a ƙarshe nace, "Dr'n mu yaushe za kaje wurin su Aisha?"

Lokaci ɗaya naji ya yi ɗiff bai ƙara cewa komai ba, magana nayi ta mishi amma bai kula ni ba, har sai da na fara mishi kuka tukun yace mun,
"kada ki ƙara gaya mun haka, ke baki son na zauna da ke ne"?

Ina share hawayen ido na nace, "ina so Dr, ai na tambaye ka saboda bana son ka tafi ka bar ni ne".

"Insha'Allahu bazan bar ki ba har iya ƙarshen rayuwa ta, sai dai ke idan kin guje ni".

Murya ta tana rawa a hankali nace, "Dr nah! Bazan taɓa barin kaba, ko aure nayi da kai zan tafi, bazan bari mu rabuba har abada muna tare".

"Bazan biki gidan mijin ki ba, saboda idan ya ɓata miki rai zan ƙarasa shi, kawai mu zauna tare, ko na miki tsufa?".

"Ni bana ganin ka tsufa, ni kyau ka ke mun sosai, kuma kana burge ni, kai kaÉ—ai na ke son na dinga gani kullum, na fasa auren ma, da kai zan zauna, amma kai ma ba zaka auri kowacce mace ba, mu kaÉ—ai zamu zauna tare".

Tashi Dr ya yi daga kwancen da yake ya riƙe kanshi, idon shi a lumshe yace, "me ki ke ji a kaina Hummy"?

Nima tashi nayi na zauna kaman zanyi kuka, don na rasa ni mai na keji ne yau akan shi, ina jin kaman zuciya ta zata fito, kuma na kasa gane yanayin da na ke ciki, a hankali nace,

"Dr nah! Ni kan kazo wuri na yanzu".
na faɗa kuka yana kuɓuce mun mai ƙarfin gaske.

Dafe kanshi ya cigaba da yi da ƙarfi ya furta, "ya Rabbi".
a zuciyar shi yace, "wayyo Baby nah kin yi nisa ya ya zan miki ne ni Aliyu Hussain".
Shima hawayen ya samu kanshi yana fito mishi.

"Dr kazo".

"Baby kwanta kiyi bacci gobe akwai school, zamu ƙarasa maganan gobe".

"ni kam naƙi Dr'n mu, to zuciya ta tana mun ciwo, zan gayawa Daddy yazo ya kaini asibiti".
na faÉ—a ina kuka.

"Kada ki gaya mishi, ki bari gobe zan kawo miki wani magani zaki daina ji, rufe idon ki na gaya miki wani abu".

Da sauri na rufe, amma sai naji yana mun waƙan wani tsohun film ɗin india, wanda yawanci na kanji Daddy yana jin shi amma ni bai taɓa mun daɗi ba, amma yau sai naji daɗin shi kaman zai saka ni kuka, wani tsohun waƙa ne da Amit ya yi na film ɗin *KHABI KHABI*.

*©AUNTY NICE CE*✍🏼
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

_*MAMAN ABDALLAH*, *MAMAN BASH*, *SA'EEDA SADIYA* *NA GASKIYA FANS D, WANNAN SHAFIN NAKU NE, DOMIN TUKWAICIN IRIN ZAFAFAN COMMENT DA NAKE GANIN KUNA MUN AKAN WANNAN NOVEL, NAGODE ALLAH YA BAR MU TARE, IDAN BA KU BABU BOOK.*_

*SHAFI NA 11📑*

*__________📖* Tun da na idar da sallan ban tashi a wurin ba, har lokacin ishaa yayi na tashi na fara yin sallan, ina cikin yin shafa'i da wutiri naji ana shigowa cikin ɗakin, ina cikin sujuda naji muryan su Abbu da Ummi, suna gaisawa da Amal, daga baya kuma naji Dr Abdallah ya musu sallama ya bar ɗakin.

Ina idar wa na juyo fuska na É—auke da murmushi ina gaishe su, kaman wanda muka shekara da sanin juna mu kayi ta hira da su, in da Ummi ke bani labarin ciwon Amal da yadda yake ba ta wahala,

"yaran mu uku a duniya, daga babba Yayan Amal wanda shi tun yana ƙarami Allah ya mishi rasuwa, kuma shi sai ya kasan ce, AA, sai mai bi mishi shi kuma AS ne, yana karatu yanzu haka a Oxford university, mai suna Faisal yana shekaran shi na ƙarshe kenan, in da ya ke karantar medicine, Amal ita ce mace a cikin su, kuma ita Allah ya ɗaura mata wannan laruran, amma kuma mungode Allah da ya bamu juriya da haƙuri na kula da ita, saboda shi ciwo ne wanda mai ciwon da mai jinyan kullum a wahale suke, mun so tayi karatu a kusa da mu cewar Ummi, amma sai nayi tunanin wata rana fa Amal in tana da nisan kwana, za tayi aure kuma bamu san in da auren zai kaita ba, shiyasa muka yanke shawaran kawota nan tayi karatu, amma kullum a cinkin fargaban ciwon ta muke".

Ummi ta faɗa tana ta daddanawa Amal ƙafa, wanda tun shigowan ta abinda ta ke tayi mata kenan.
Chapter 16 · 0% Book details