← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 66

Sashe 50

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayawa tayi a gaban motan sai cin magani ta keyi tana harare-harare, tsayawa yayi na wani lokaci yana dubanta, chan ya koma Abdallan shi yana dubanta fuska a murtuƙe yace, "nifa bana son rashin hankali, hakan yayi miki mutunci kizo gabana kina wani jiye-juyen jiki kamar ke kaɗaice mace a duniya? Ko kuma haka aka ce miki ana taryan baƙo? Toh ni bazan ɗauki rainin hankali ba", ya faɗa mata fuskan shi a murtuƙe, da sauri ta juyo da ɓufin ta maida mishi martani, amma ganin fuskar shi ya sakata juya da fuskarta gefe tace, "toh ni nace maka kada ka shigo ne,? Ni ae jira nakeyi ka shigo", ta faɗa tana ta murguɗa bakinta ta gefen shi.

"Nidai koda wasan wasa kada ki nemi raina mun hankali, maganar auren nan nayi ne don samun kwanciyar hankalinki gaba, amma k8na ta wani nuna isan ke wata ce, bayan na samu Baba nace mishi bana son maganan abarki ki auri wanda ki ke ganin kun dace amma firr ya tafi akan maganan, ni bana son nunawa iyayena ban haihu ba a wurinsu shiyasa na amshi buƙatun su da hannu bibbiyu, amma hakan bazai saka ki raina mun hankali ba don ina da wacce ta fiki komai a gida", ya faɗa yana tafiya hanyar shiga parlourn.

Baki a buɗe ta bishi da kallo cike da mamakin shi, tana tambayar kanta dama ba wai sonta yake ba? Har yana nufin matar shin tafita komai da komai, kodai don ita matar shi yana sonta ne yake ganin ta haɗu? amma ita dai taga photon matar da ta je gidan Umaima, kuma bataga ta fita komai ba, banda ma wani bleaching da ya ɓata mata fuska gata gajeruwa lukuta sosai, tsaki taja ta bi bayan shi zuwa parlourn.

Gaisawa ta samu su nayi da Aunty uwani, itama ta nemi gefe ɗaya ta zauna, har Aunty uwani ta fita bata ɗaga kai ta dube shi ba, shi kuma babu abinda yakeyi sai kallonta, domin ba ƙaramin shiga ranshi tayiba, shiru zuwa wani lokaci yace, "ke kam Hauwa baki ɗauki halin kirki irin na ƴan gidanku da iyayenki ba, amma har yaushe baki san yadda ake mutunta baƙo ba, ballantana kuma ina da ƙarin darajar matsayin miji a gare ki, kina son albarka kuwa"? Ɗago kai tayi tana duban shi, murya cike da sonyin kuka tace, "ba kai bane kace dole aka maka ka aureni, kuma wai ban kai matar ka komai ba, kuma wallahi na gani na fita kyau, kawai faɗa ne baza kayi ba don ita kana sonta", ta ƙarasa faɗi kaman zatayi kuka.

Dariya yayi yana dubanta cike da nishaɗi a ranshi yace, " kin taɓa ganin inda aka fi son wata mace sama da uwargidan ka? Toh ki daina ruɗin kanki matar farko baka ganin wacce ta fita a komai, ballantana wanda kukayi soyayyah kana sonta tana sonka", ya ƙarasa yana gyara zaman shi.

Turo baki tayi gaba, " hmmm nidai nasan Hero duk da a ta biyu ya aure ni yafi sona akan Aunty suwaiba, kuma kullum ce mun ya keyi ina da kyau, saboda haka nasan ni mai kyauce, don muna secondry school *Hauwa golden girl* ake cemun", ta faÉ—a tana jujjuya idonta.

Kallonta ya tsaya yanayi a cikin zuciyar shi yace, "wato duk matar mamaci magana ɗaya sai ta kwatanta da mijinta ko? toh yanzu don Allah idan da ba don ɗan'uwan shi bane da yaya zaiji a ranshi?" a fili kuma yace, "shiɗin ae ya aure ki yana sonki ne duk da ma ance Abba ne ya tura mishi ke, shi kuma yayi biyayyah ya karɓa kaman yadda nima nayi yanzu, shi kuma bansan dalilinshi na ganin kyaunki ba? nikan bana gani gaskiya, ko dan banji ina sonki bane ohoo", ya faɗa yana wani ya mutsa fuska.

"Wallahi baka isa kace mijina baya sona ba, don ni nafi kowa sanin irin son da yake mun, kaidai da baka sona kai ka sani, don ni ban maka dole ba, idan baka so akwai mai so kabar mishi ni kawai zai fi mana zaman lafiya", ta faÉ—a tana share hawayenta.

Dariya yayi yace, "nima haƙuri zanyi don kada iyayena suga ban mutunta su ba, amma ke idan kinga zaki nunawa duniya iyayenki basu isa da ke ba, toh kiyi gaggawan taimaka mana ki gaya musu baki sona, ko nima zan samu kwanciyar hankali".

Shiru tayi na zuwa wani lokacin, sannan ta dube shi baki ta murguÉ—a mishi tace, "da yake nice wanda akace jeki kya gani ko? wanda bansan darajan iyaye na ba, toh bazan faÉ—an ba, kai da baka son kaje ka faÉ—a".

Miƙewa yayi yana zurma hannun shi cikin aljihun shi yace, "nidai babu ruwana ban iya jayayyah da yayuna bama ballantana iyaye na ba, ke kuma na barki lafiya da halinki na rashin mutunta baƙo, zanje gidan umaimah nayi breakfast na wuce, domin gobe da safe xan wuce Zaria wurin my luv ɗita", yana dariya ya ajiye mata kuɗin da yakai 20k a cinyarta yace, "ki dinga transport kafin na dawo ko".

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻

[8/28, 14:26] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1442H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 41📑*

*INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, MISS XERKS, NEAT LADY, INA MUKU TA'AZIYYAH DA WANNAN RASHI DA AKA MUKU, ALLAH YA JIƘANTA DA RAHMA, ALLAH YASA TA HUTA*

*__________📖* Duk yadda Aunty hauwa taso ta dinga ƙuntatawa Uncle Abdallah abin ya gagara, domin ya riga da ya tsare gida baya ɗaukan raini ko kaɗan, duk bayan sati biyu yake zuwa dubata, kuma kullum da irin rikicin da akeyi a tsakanin su, shi zaice sai ta bishi inda ya sauƙa, ita kuma ta dinga surutun ya raina ta kenan, haka za'asha dirama a tsakanin su har ya koma.

Wani ranan jumma'a Abdallah yazo Narabi inda ya samu Baban su ya tashi babu lafiya, duk hankalin ƴan gidan a tashe, haka ya ɗauke shi da uncle sabo suka kaishi asibiti a cikin jos, don Baban su bai cika son zuwa asibiti ba shiyasa yaƙi faɗawa kowa bayida lafiya, suna zuwa a ka basu gado, domin an tarar yana ɗauke da hypertension, ga kuma diabetics, duk hankalinsu ya tashi, inda Aunty Amina da Aunty hadiza da suke zaune a jos duk suka hallara a cikin asibitin.

Da yammah Uncle Abdallah ya ƙira Aunty hauwa yake gaya mata suna asibiti da Baba shi yasa bai samu daman ƙarasowa ba, jikinta a sanyaye ta gaishe da jikin Baban, kuma tace mishi gobe insha Allahu zata zo ta duba shi da jikin, bayan sun gama wayan ne ta gayawa Dr Alƙali da Aunty uwani da suke zaune a parlourn tare, Dr yace "babu komai suma zasuje idan yaso sai su dawo a goben ita kuma ta kwana", turo baki gaba tayi tana duban Dr tace, "mu dawo dai tare yayah, ni kuma kwanan me zanyi a can, kawai mu tafi tare mu dawo tare".

Dariya yayi a hankali yace, "Hauwa problem", Aunty uwani dariya tayi tana, "ni dai bansan me yasa kike gudun wannan haɗaɗɗen mijin naki ba, gaskiya hauwa ki gyara halinki da ɗabi'un ki, idan ba haka ba za'a ƙwace miki miji da gaggawa",.......turo baki tayi a hankali tace, "ba sai a ƙwace ba ni na damu da shi ne, yaje chan su ƙarata da buskuɗan matar shi", ta faɗa bayan ta tashi ta kama hanyar ɗaki tana ta mita.

A chan asibiti kuma bayan anyi sallan magarib mama kaltume suka zo tare da uncle sabo a motar uncle Abdallah tare da Nana khadijah da Zahra, don Aunty indo da Aunty Asma'u tare akayi auren su, yanzu kusan shekara 2 kenan, yanzu haka maganan auren Nana khadijah akeyi, suna shiga ɗakin Zahrah ta ƙarasa gefen Baban ta zauna bayan ta riƙe hannun shi, cikin shagwaɓa da nuna ita ɗin auta ce tace, "Baba da wai mama tace baza a zo dani ba, ni kuma nayi ta kuka tukun yayah sabo yace suzo da ni, amma Nana khadijah kam don baƙin hali zuga mama tayi wai kar azo dani, Baba don Allah a airar da ita na ɗan huta".

Ganin autar ta shi ya sauƙar mishi da farin ciki, yana duban ta cike da so da ƙauna yace, "Duk yadda kikace haka za'ayi Fatin Baba, nima na gajji da zama dasu, na fi so gidan yazama daga ni sai ke nayita saya miki abinda kike so, kina walwalanki yadda ya kamata", sannan ya juya gefen Mama kaltum da Nana khadijah yace, "ina mai jan kunnen ku akan autata, na sake jin wani ya ɓata mata toh ni dashi a gidan nan, ke kuma Khadijah tunda kina takura mun yayata danafi so a duniya Nana Fatima toh zan dawo da ranan auren kin baya idan yaso ayi ta samu sakewa" ya faɗa yana hararan Khadija da wasa.

Murmushi Zahrah ta farayi tana gwalo wa Nana Khadija, Mama kuma ta kai mata ranƙwashi tace, "ke ɗin tabbata zakiyi ae a gaban Baban naki ko? Toh ki shiryah ke kam ma baɗi war haka ana shirin kaiki nako gidan, ki bar ma murna", dukkan su ɗakin dariya sukeyi na rikicin Zahrah da Babanta, Aunty Amina tana kallon Zahra cike da kulawa tace.

"Autar Baba Umaimace fah mai sunan maman Baba, amma ke kuma sunan yayarshi kikaci amma yafi ji da ke, kodai don kin zamo auta ne aka fi son ki"? Ta faÉ—a tana bin ta da murmushi.
Chapter 50 · 0% Book details