← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 66

Sashe 44

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɗakin su Aunty hauwa kuma Aunty Ummi da take kwance gefen Aunty hauwa ta fara bacci kawai taji Aunty hauwa ta miƙe zaune da ƙarfi tace, "Wayyo Mama zuciyana yana tsinkewa, nikan mama kawai zan bi mijina, ina tsoron wani abu ya same shi", ta tashi da sauri tajawo hijab ɗin da sukayi sallah ta saka ajikinta, tayi hanyar parlour tana faɗin, "nikan sai naje na tashi Abba ya kaini wuron miji na", Adda zuba mata ido tayi tana kallon ta, Aunty Ummi da ƙanwar Baba Umar ma tashi sukayi suka miƙe tsaye suna kallon ta, suma daga dukkan alamu shirin binta sukeyi, Mama da sauri tace, "ke Hauwa kada kije ki tashi bawan Allahn nan, kiyi haƙuri zuwa safiya sai ya kaiki idan Allah ya kaimu", amma ina Aunty haiwa tunin tayi parlour, wanda da sauri su Aunty Ummi suka bi bayan ta, tana fitowa parlourn kuma yayi dai-dai da fitowar Abba cikin gudu-gudu Ummi na binshi a baya a ruɗe tana tambayan shi lafiya ina zaije a cikin daren nan?

Abba yana ganin Aunty hauwa yaja ya tsaya ya ƙura mata ido jiki shi sai rawa yakeyi, itama ƙura mishi idon tayi tana kuka tace, "nikan Abba ka kaini wurin mijina nikan", ta ƙarasa da sunkuyawa ƙasa tana kuka, rufe idom shi gam da ƙarfi ba tare da ya furta komai ba, Ummi kuma sai tambayan shi ta keyi abinda ya faru?

*ZAINAB IDRIS* ta group ɗina mai suna *MUYI NISHAƊI* wannan shafi nakine kyauta na baki, kuma na cika miki alƙawarin yi miki typing mai yawa yau, da fatan zai faranta miki, nagode sosai da kulawanki gareni, da kuma book ɗina.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻

[8/18, 14:07] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*FAUZIYYA A.A WANNAN SHAFIN NAKI NE, INA ƘARA MIKI TA'AZIYAN RASHIN MIJINKI ALIYU BABAGANA ZAKI (ABBA). TABBAS INA KUKAWA KAINA INA KUKA MIKI RASHIN GWARZON MIJINKI MAI MIKI ƘAUNA FISABILILLAH, INA MIKI ADDU'AN ALLAH YA BAKI MADADIN SHI, ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR HIDAYA, ALLAH YA SA MIKI DANGANA A ZUCIYARKI, TABBAS FAUXY NA TAUSAYA MIKI, HAR YAU ABIN YAƘI BARIN ZUCIYATA*.

*SHAFI NA 36📑*

*__________📖* Daidai lokacin su kawu auwal suka shigo daga ɗakin ƙofar gidan shi da uncle Baba, kowan su cikin firgici yake kallon Abba, ganin haka Abba ya buɗi baki yace "duk kanku kuyi haƙuri ku zauna a gida, idan naje na dawo sai kuji me yake faruwa, amma yanzu nima bani da tabbacin me ya faru, amma Auwal da Baba su zamuje tare da su, duk yadda ake ciki zan ƙira na sanar da ku", ya faɗa yana shirin fita daga parlourn.

Ummi ta riƙo hannun shi tana duban shi da kyau tace, " ba haka naji ka faɗa a waya ba, daga dukkan alamu wani abu ya faru kake ɓoye mana, ko wani abu ya samu Baba Umar ne kam"? ta ƙara sa faɗi hawaye na zubu mata.

Da sauri Aunty hauwa ta matso kusa da Ummi tana zare ido, hannun ta duka biyu akan ƙirjinta, "Ummi nah me kikaji yace ya faru da miji na? Ina fatan dai ba hatsari sukayi ba ko?" sannan ta juya wurin Abba da sauri da yake shirin barin parlourn, hannun shi ta kamo murya na rawa tace, "zan bika naje wurin miji na," tana jijjiga kai tana hawaye tace, "nikan babu abinda ya faru da mijina, ka kaini gidan mu nagan shi kawai", ta ƙarasa faɗa jikinta yana rawa sosai.

Kawu auwal ne yazo yakama hannun ta ya miƙawa Mama ita, sannan ya dubi Ummi yace, "haba ummi uwa, keda zaki kwantar wa hankali kuma kece mai son dagula komai? Kuyi haƙuri yadda Abba yace muje duk abinda ake ciki ni da kaina zan ƙiraku ko shi bai ƙira ba" yana gama faɗi yabi bayan Abba da suka fita tunda ya matsar da Aunty Hauwa a jikin shi, suna shiga motan Abba yaja su sai asibitin da aka musu kwatance, suna parking saiga wata motar ƴan custome tana parking a gefen su, Abba zaro ido yayi don ganin shugaban su Baba Umar ya fito da sauri saura suna binshi a baya, ga police sama da goma a asibitin.

Jiki na rawa Abba ya dube su yace, "Allah yasa bai wahala sosai ba, Umar ne suka samu accident a hanyar su, ya faÉ—a ganin yadda duk suka fita a nutsuwar su, babu wanda ya iya buÉ—e baki ya amsa mishi sai binshi kawai sukayi zuwa cikin asibitin.

Suna shiga kai tsaye emergency suka wuce inda suka hango yawan ƴan custome ɗin a wurin, da sauri Abba ya ƙarasa, Dr ne da suke tsaye da police ɗin ya ƙarasu gaban Abba, yana duban shi yakaranto mishi number shi na waya, gyaɗa kai Abba yayi alaman shi ne.

Dr dafa kafaɗan Abba yayi yana ce mishi "am sorry sir, munga number ka a wayan shi da sunan ɗan'uwa, kuma kaine last mutumin da kukayi waya da shi, toh ganin faruwar accident ɗin shine muka neme ka, sannan a aljihun shi muka samu I.D Card ɗin shi da ya nuna mana shi custome ne", sannan ya maida kallon shi kan ogan ƴan custome ɗin yace "mu ƙarasa ku ganshi," da sauri kowa yabi bayan shi.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shi ne kalmar da yake fita daga bakin kowa da ya ɗaura idanu akan Baba Umar da Aunty suwaiba. Jiki na rawa Abba ya ƙarasa kan gawan Aminin na shi kuma ɗan'uwan shi Baba Umar ya kife kanshi a dai-dai inda jini yake ta kwaranya, ya kife yana kuka yana salati iya ƙarfin shi, da ƙyar aka ɗago shi, jiki na rawa ya dubi Dr yace, "meyasa kace mun accident yayi? Yayah kake so na fuskanci dattijon mahaifin mu da wannan mummunan labarin? Yayah ma zanyi na sanar da matar shi wannan batu yadda tun ɗazu bata da nutsuwa? Waye zai iya gaywa ɗiyar shi ƙwalli ɗaya ta rasa mahaifinta data kasa runtsawa a daren yau"? Riƙe shi Kawau auwal yayi yana faɗin kalman "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un", sannan ya samu wuri ya zaunar da shi, a hankali ya dubi Baba ƙarami da ya kife a ƙasa ya ɗaura hannu akai kaman mace yana ta rusa ihu, gefe ɗaya kuma shugaban su Baba Umar ne da girman shi shima kukan yake tayi baya kallon kuwa.

A hankali police ɗin yace," Anyi abu bai daɗe ba mutanen mu suka ƙarasa wajen, domin jin ƙaran harbi, abinda ya faru wato mun fi tunanin kidnafers ne suka aaikata musu hakan, domin alama ya nuna sunƙi tsayawa ne aka harbi mai tuƙa motan, ita kuma matar motar ce data ƙwace suka dinga kifawa, anan kwananta ya ƙare domin babu harbi a tare da ita, saidai wuyanta ya karye, shi kuma ga harbi akan shi kuma ga karaya a kunkuminshi da sauran wurare masu yawan gaske", bayani Dr shima ya cigaba da yi musu, wanda daga uncle Baba har Abba babu mai fahimta, Kawu Auwal ne kawai yake fahimtan abinda suke faɗa, tare da shugaban su.

Abba basu aka basu gawan ba sai wurin Asuba, inda Abba ya bawa shugaban su Baba Umar number Baban Narabi akan ya gaya mishi, da ƙyar yayiwa Baban Narabi bayanin rasuwa, wanda shi kuma Baban mai ƙarfin imani yayi ta godiya wa ubangiji, sannan yace su taimaka su taho mishi da gawan zuwa jos, yana son a rufe su anan, haka shugaban ya bashi tabbacin zasu aikata.

Shawara Dr ya basu akan a musu wanka a asibitin saboda ɗaga hankalin mutanen gidan, kuma su Abba sukayi na'am da hakan, ma'aikatan asibitin suka wanke gawawwakin, aka shirya su a cikin likkafani, sannan su Abba suka wuce gida domin sanar musu, tunda sukayi parking Abba ya kifa kanshi akan sitiyarin motan ya fashe da kuka, Kawu auwal ne ya saka hannu ya riƙo uncle Baba da ƙarfi ganin zai fita da gudu yaje ya tayar musu da hankali, zaunar da shi yayi yace, "ka zauna a motan bari na fara shiga".

Yana shiga ya tarar da dukkan mutanen gidan zaune zuru-zuru a parlourn, gefe ɗaya kuma Aunty hauwa ce kwance akan cinyar Mama sai kuka ta keyi, da sauri ta tashi ta nufi kawu auwal, jiki na rawa ta kamo hannun shi tace, "ka kaini wurin miji na yayah auwal, ina sukaje ne shida Aunty suwaiban"?, duk yadda yaso ya daure kawu auwal ɗin sai ya kasa, kawai samun kanshi yayi da fashewa da kuka ya rungume hauwa gam a jikin shi, Addagana ganin haka ya saka ta sunkuyar da kanta tana ta wasa da ƙasan hijabin jikin ta, ga wani haki da ta ke tayi lokaci ɗaya, Ummi ce ta matso jikin su tana tambayan kawu auwal, "ina sauran suke? Me yasamu Baba umar ɗin ne? Ya samu rauni ne sosai"?.

Buɗe ƙofan yasa hankalin kowa ya koma kan Uncle baba da ya kafe a wurin yana kuka kaman ƴa mace, da gudu Aunty hauwa ta je ta rungume shi tana, "ɗan'uwa na kai ne kafi kowa damuwa dani, nasan zaka gaya mun komai, don Allah ina mijina da ƴar'uwata? Sun koma gida lafiya ko"? Uncle Baba yana ɗaga mata kai yace, "tabbas mijinki da ƴar'uwar ki a yau sun koma gidan su na gaskiya, tabbas sun amsa ƙiran ubangijin mu a lokaci ɗaya, sun tafi sun bar mu da tsananin kewar su a zuciyar mu," ya saka hannu ya dafa shoulder Aunty hauwa ya cigaba da faɗin, "tabbas ƴar'uwata yau kam zuciyar ki ta ƙuna, yau kinyi rashi mafi girma a rayuwar ki, yau kam mun rasa jarumi, nagarin mutum Baba umar da matar shi, sakamakon harbi da iskan gari suka mishi a hanyar komawa gida, lallai sun jefa zukata dawa cikin maraici ƴar'uwata, Allah yajiƙan su da rahma".
Chapter 44 · 0% Book details