← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 66

Sashe 42

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suwaiba kuma haɓa ta riƙe tana mai matuƙar jin tsoron furucin Baba umar, gashi ta sha dukan tsiya, ga rashin iya maganan ta da kula da miji ya jawu ko ta kan maganan ta ba abi ba, juyawa tayi ta dubi ƙofan ɗakin Aunty hauwa da ta leƙo ta ƙurawa suwaiba ido tana murmushi, a hankali Aunty hauwa ta ƙaraso cikin parlourn ta zauna gefen suwaiba tana ta jujjuya idon ta tana rausaya jikinta, ta gefen ido ta kalli suwaiba tana murmushin iskanci tace, "suwie darling! Wato ke baki san ta yadda ake bariki ba kuma kice zakiyi bariki? ae ba'a kishin banza yanzu, an waye suwaiba, ana kishi ne na nuna kulawa da miji da tsafta da kyautatawa, bawai banzan kishi irin naki ba, idan kince irin shi zamuyi toh ina mai tabbatar miki kece a ƙasa, gara ma ki saduda mu zauna lafiya, don ni babu mugunta a zuciyata, idan kace zaka shiga gona nane kawai zan taka maka burki iya sanin ka, so ina mai jan kunnen ki da babban murya suwaiba, idan kunne yaji toh jiki ya tsira", bata jira mai suwaiban zata faɗa ba ta wuce ɗakinta ta barta tana share hawayenta.

Wani irin kulawa Aunty hauwa ta ke nunawa Baba umar, har sai da yakai ranan da zata karɓi girki dole sai ka gane rawan kan shi, don ko zaman parlour ba ya iya yi, a haka har hutun Aunty hauwa ya ƙare, tazo gidan mu yakai kusan sau biyar, wani lokacin Ummi zata je damu gidan mu ɗauki Aunty hauwa muje shan iska cikin lagos, wataran muje gidan abokan su Abba da Baba umar, a haka har Aunty hauwa ta koma Narabi, ko kwana biyu bata wuce ba ta koma school.

Ten october 1980, shine ranan da aka haife mu nida Hassan, yau kuma ya kama 10 october 1985 Aunty hauwa ta haifi ɗiyar ta mai masifar kama da ita, lokacin da Aunty hauwa ta haifi ɗiyarta munyi tsalle da murna nida Hassan badon komai ba, sai don jin daɗin date of birth ɗinmu yazo ɗaya da sabuwar ƙanwar mu, ranan Aunty haiwa saida ta gajji da amsan wayan mu, don ko ta ajiye bata wuce 1hr zamu sake ɗauka muce, "Aunty ki saka mana kukan sistern mu", ita dai dariya kawai ta keyi, a dole sai ta ɗan bugi babyn ta fara kuka.

Munajin muryan kukanta zamu fara tsalle nida Hassan muna tambayan Aunty, "Aunty don Allah muryan babyn irin na waye a cikin mu"? Dariya Aunty ta keyi tace, "muryan kukanta na rikici irin na Babana hassan ne, idan kuma tayi muryan wasa na Aminina Hussain ne, saboda haka muryan kune dukan ku", dariya zamuyi tayi muna murna, chan kuma sai Hassan yace, "AuntÆ´ dani take kama ko"? Nan ma dariya Aunty hauwa ta keyi tace, " toh maganan gaskiya baby kam da Ummi ta ke kama".

Mu kuma jin tace da Ummi take kama sai duk muka fara tsalle muna cewa, "yehhhh Ummin mu tayi baby mai kyau", ita dai ummi da ta gajji sai ta karne wayanta tama kashe gaba ɗaya ra ɓoye.

Umma ce ta tafi zama wa Aunty hauwa, inda Goggo da Addagana sukaje suka ga baby suka dawo, Kawu Auwal ma da Aunty ummi sunje sunga baby tare da Uncle Baba, ranan da sukaje kuma ranan muka zo tare da Ummi ana sauran kwana uku suna, Uncle baba yana kallon babyn yace, kai wannan yariya tayi kwaɗayi kam, dubi bakinta ɗan mitsul kaman ba ita bace tazo ta cinye mana ayan gidan mu, zuɓun mu, ferfesuop, gwaten tsaki, kai Bappah da su Mama sun kashe kuɗi kam a ɗan wannan mutsilan bakin, na ɗauka yara uku ne zasu fito domin irin cin da tayi ashe ɗaya ce me kama da uwa ma bada mama", ya juya yana kallon ummi yana dariya yace, "Adda Ummi nah! Duk da kuna kama da wannan mai kan zabuwan", ya nuna Aunty hauwa da bakin shi yana dariyan neman tsona, ita kuma sai hararan shi ta keyi tana kallon kawu auwalu akan ya saka baki, shi kuma sai kallon su ya keyi yana murmushi, don shi kafin kaji bakin shi a abu toh sai abu ya ɓaci, don dayawa ana cewa na ɗauko halin shi, amma har gara ni sau babu iyaka ina magana fiye da shi, uncle baba ya cigaba da maganan shi yana dariya, "wato ummi yarinyar nan sak ke, kaman ke kika haifeta, wallahi kyaun nan dai naki ta ɗauko, don uwar ta kanta yayi kojeje haka kaman na ƴan gabɗori", ya ƙarisa yana dariya, kowa da yake parlourn dariya yayi, ita kuma Aunty hauwa hararan shi tayi tace, "kuma wallahi kada kazo mun ranan suna, don ban gayyace kaba, kuma ƴar nan ko ta girma bazata ce maka kawu ba, kana ji kana gani zata ce maka Baba ƙarami mai kan kwakwa", ta faɗa tana hararan shi, hattah umma da tashigo da abinci wa su Ummi sai da tayi dariyan maganan Aunty hauwa, nida Hassan kuma duk wanda ya ɗauke ta sai mu koma kusa da shi muna taɓa yatsun ƙafan ta, Ummi ta karɓi babyn a hannun Uncle Baba tana murmushi tace, "naga ranan da zaku girma wallahi Baba, daga kai har hauwa ban san waya fi shiririta ba", ummi ta ƙurawa babyn ido tana duban ta da murmushi, chan ta dubi Kawu auwal tace.

"Auwal dubi ƴar nan babu ƙaryah fa gaba ɗaya da ni take kama, nifa ko su Hassan dana haife su a cikina toh wallahi banji son su ba yadda nake jin son wannan yarinya, don Allah dubeta tun tana ƙarama kamanin ta ya nuna sosai, wannan kam idan ta girma za a daina cewa muna kama da hauwa trouble, sai dai ace ga mai kama dani", Ummi tana dariya tace, "hauwa wannan yarinyar kam ni zan raine ta, don gaskiya ta shiga raina matuƙa, ke kuma na sanki da dauriya zaki haifu wasu kwanan nan", ta faɗa tana duban Aunty hauwa da ta buɗe baki tana kallon ta, kawu auwal yana dariya yace, "maganan ki dutse babbar ya uwa, nima ina bayan ki, kinga su twins sun samu sister".

Kallon Aunty hauwa uncle Baba ya tsaya yanayi, yana jiran yaji abinda zata ce ta tofa, Aunty hauwa ta kalli ummi tace, "gaskiya Ummi kinga wannan ƴa macece, ki bari sai na haifi namiji sai na baki ki haɗa ki zama maman ƴan maza, nikan ina son wannan ɗin, amma kiyi fatan Yayah auwal su haifi ƴa mace sai su baki, don kinga Aunty ummi sai wani ɓoye cikinta ta keyi cikin hijabi, bata san sa'idawa har sun gani sun sanar dani ba", ta faɗa tana dariyan uncle baba daya buɗe baki yana matan kallon marar sirri.

"zakuji da shi ae da gulmar ku, kullum kuna ɓatar da mutane akan ku baku zaman lafiya, kuma wallahi Adda Ummin mu, duk gidan mu babu masu gulma na haɗin kai kaman wanda sukayi gware suka zo duniya irin Hauwa da Baba ƙarami, babu garin Allah da zai waye basu ƙira junan su ta waya sunyi gulma ba, kuma duk halin da hauwa ta keyi shiyake ƙara ɗaurata akan network", Kawu auwalu ya faɗa yana duban su yadda suke ta dariya har da tafawa.

Daidai lokacin Baba umar ya shigo suka gaisa da su ummi, inda ummi take gaya mishi yadda sukayi da Aunty hauwa akan babyn, yana murmushi yace, "wallahi babbar ya nidai na baki uwata duniya da lahira, duk ranan da hauwa ta yaye ta ki karɓeta, ko ina raye ko bana raye, na baki ita don na yaba da karamcin ki, kuma wallahi naso saka miki takwara da yarinyar nan, toh sai mahaifina yace yana so nasaka sunan mahaifiyata, amma insha Allahu idan Allah ya sake bamu ɗiya mace toh tabbasa, *NANA FATIMA* zan saka, amma wannan ma bai ɓaci ba in sha Allahu na baki ita duniya da lahira".

Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi, murya a hankali Aunty hauwa tace, "insha Allahu ma hero kana nan sai munyi ƴaƴa goma sha biyu tare da kai, kuma insha Allahu wannan yarinya shayar da ita kawai zanyi, ina yayeta zan bawa Ummi nah, don nima ikon tace ballantana abinda na haifa", hawaye ta share a idon ta ta dubi Ummi da ita ma lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi, "Ummi na miki alƙawari ko nuna so bazanyi wa wannan yarinyar ba, kuma zan nuna miki ni ɗin ƴar halak ce, domin zan kawar da kaina akan ɗiyar nan, dama ni Hassan da Hussain ne nawa ƴaƴan", ta faɗa tana share hawayen ta.

Ranan sunan ƙanwar mu taci suna mai girma da daraja, wato sunan uwar muminai, *NANA AISHA* ƴar uwar da babu irin ta a duniya ƴar'uwar da muke mata son da bamuyiwa kan mu, wanda muka kasance ƴan biyu kyautar Allah, amma bamu son junan mu yadda muke son ƙanwar mu Nana Aisha, wanda yawan ci munfi ƙiranta da Aisha".

anyi suna da kwana biyu mukaje misau muka gaida su Bappah, muka ƙara kwana biyu tukun kawu auwal suka rako mu jos domin mu shiga jirgi mu tafi lagos, mun tsaya a Narabi muka sake ganin sistern mu Aisha, muna cikin farinciki muka shige airpot muka tafi lagos.

Aisha tana da shekara ɗaya Ummin mu ta haɗa mana birthday party a lagos, lokacin Aunty hauwa ta gama school ta dawo lagos da zama, Ranan kaman baza mu mutu ba don daɗi, gashi Aishan mu tana tafiya abin sha'awa, ga wani kyau da gashi da yarinyar ta ke dashi, wanda kowa ya ganta sai ya ƙara ganinta, kaya iri ɗaya Ummi ta saya mana, wani wandon jeans ne Blue da wasu rigunan polo Red colour, sannan Baba umar ya saya mana wasu kuma, namu baƙin wandon jeans da blue riga, ita kuma Aisha blue skirt na jeans da pink riga, ranan iyayen mu sun kashe mana kuɗi ba kaɗan ba, Aunty suwaiban Baba Umar babu yadda ta iya da masifan Aunty hauwa, dole ta dawu kaman wata yarinyar ta don tsoro, duk inda Aunty hauwa ta juya ta haka take juyowa, sai dai kuma Aunty hauwa babu matsalan cutar da mutun, saida buhun bala'i kawai, shima idan an taɓo ne, mun samu kyaututuka kam babu iyaka.
Chapter 42 · 0% Book details