Sashe 7
Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aisha ce kaÉ—ai take ce mun Yaya Hussain É—ina, ke kuma kina cemun Dr'n mu keda sauran students É—ina, yanzu kuma kince mun Dr'n ki? To wallahi kece Aisha ta, kina neman yi min wasa da hankali nane, Ki taho wuri na Aisha na!!".
Ya faɗa da iya ƙarfin shi wanda sai da na zubar da books ɗin hannu na, na fita da gudu a parlon nayi nawa gidan ina kuka, da ƙarfi na shiga na mayar da ƙofar na rufe ina kuka, ina jingine da ƙofan naji muryan Dr'n mu yana cewa.
"ki buɗe ƙofan Aisha ki gaya mun wacece ke? Tabbas kece Aisha na, kuma yau zan tabbatar miki da cewa ke ɗin Aisha tace".
Da ƙarfi yake maganan wanda lokaci ɗaya naji tsoro ya rufe ni, a zuciya ta nace,
"ko dai Aisha'n ba mutum bace? Ko shima Dr aljani ne?".
Can kuma nayi sauri na girgiza kaina nace, "Dr na mutum ne, amma Aisha'n ba mutum ba ce".
Buga ƙofan yayi da ƙarfi yana cewa, "ki buɗe Aisha ko na ɓalle ƙofan na shigo".
Jin furucin shi ya saka na ruga da gudu na shige ɗakina na sake rufu ƙofan ɗakin, duk jikina rawa yake yi, tsabar tsoron da ya shige mun zuciya ta.
"Aunty Nice ko ta kitchen zamu koma mu samu hanyar guduwa ne?, don idan wannan aljanin mutumin ya shigo ina ga har da mu zai haÉ—a".
cewar Miss Xerks da tayi zuru-zuru da idon ta tana kallo na a tsorace, nima haÉ—iyan yawun tsoro nayi ina maida numfashi da sauri-sauri nace,
"Miss Xerks ina cikin zama na kika ce anyi sallah lafiya mu fito ɗaukan rahotanni domin masoyan Gaskiya writers su samu goron sallan da bamu basu ba, haka kika izo ƙeyata muka taho har nan spain, tsabar mita bamu tsaya a ƙasar mu ba, da yanzu a nigeria ne kiran Ummu Nabeel zamuyi su taho da rundunan ƴan Gaskiya writers su fitar da mu ko ta saman kwanon gidan nan ne".
na faÉ—a ina fashewa da kuka don wallahi yanayin Dr Hussain ya bani tsoro.
Ƙaran buga ƙofan ya saka naga Miss Xerks ta sandare a wurin, nima daga ganin haka naji komai na hannu na sun zube, babu sauran ɗaukan rahoto sai mun farfaɗo, saboda haka a jiraye mu tukun mu dawo hayyacin mu.
_Masoya na masu bibiya ta godiya nake a gare ku, Kar dai ku manta da danna min vote da kuma yin comment domin jin ra'ayoyin ku._
*©AUNTY NICE•*âœðŸ»âœðŸ»âœðŸ»
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
   *1441H/2020M.*
 Â
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATIONâœ*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
    ```ðŸŽG•W•AðŸŽ```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*ðŸ‡ðŸ¼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICEâœðŸ¼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 6📑*
*__________📖* Nafi awa ɗaya a tsugune a wurin ina kuka, don ina jin hayaniyar sauran ƴan gidan da suka fito suka bawa Dr haƙuri, kuma nayi tunanin ko sun ɗauka laifi nai mishi yasa yazo yake masifan na buɗe ƙofan, a hankali na tashi na hau kan gado na, wata zuciyar ta bani shawarar na gayawa Daddy, amma wata zuciyar tana kwaɓa na da cewa,
"ke Humaira Daddy'n ki yana sanin abinda ya faru zai zo ya canja miki gida ko kuma ma ya canja miki school, kuma daga wannan ranar zai zamo kin daina ganin Dr ki".
ÆŠan juyawa gefe É—aya nayi har lokacin ido na bai daina zubar da hawaye ba, a fili na furta,
"Dr'n mu me ya sa ka ke mun kallon wata ce? Nifa wallahi Humaira ce ba Aisha ba".
na faɗa hawayen ya na ƙara bin fuska na.
Da ƙyar na ta shi nayi sallar azahar na sake komawa gado na kwanta, haka la'asar ta same ni, shima tashi nayi na sake hawa gado, banfi ƴan mintuna ba Daddy ya ƙirani, jiki na har rawa yake don fargaban ko zai gane murya na nayi kuka, ina ɗauka a sanyaye na ce.
"Hello Daddy na".
sannan na yi shiru ina jin bayanin da ya ke mun cikin mamaki.
"Sweet heart jiya wani lecturer ɗin ku ya ƙira ni, sunan shi Dr Hussain ya gaya mun shine yake gefen gidan ki wanda na ce miki mai shi baya nan ne lokacin da mu ka zo, amma ance mun a kwai mutum a gidan, ya gaya mun kin fito za kije school kika yar da wayan ki a ƙofan gida shine ya ɗauki number na, mun gaisa ya gaya mun kina ƙoƙari a school sannan kina kula da tarbiyan da na baki, sannan idan na amince zai dinga miki extra lesson a gida".
Rufe ido na nayi hawaye yana bin fuska na, wanda ni kaina bansan dalilin shi ba, can naji muryan Daddy yana cewa.
"Kin amince da yanayin shi da kuma mutuncin shi? Ko kuma na ba shi haƙuri? Don ni naji daɗi da ya iya gaya mun kanshi da kuma niyyan shi, kuma daga dukkan alamu ba yaro bane, don ban ji rawan kai a al'amuran shi ba, amma ke me kika gani? Saboda shi mugu baida kama, kullum ina gaya miki".
"Daddy ba yaro bane, kuma ina ga ma kaman yana da family shima, aka sari ma yana yawan mun faɗa ko idan na fito da ƙaramar riga, kuma babu shirme a al'amuran shi ko kaɗan Daddy, ni dai ta wuri na ba bu komai, umurnin ka nake jira".
"Ba bu komai sweet heart, sai dai zan ja miki kunne ki kula da tarbiyan ki da kuma mutuncin ki a duk inda ki ka samu kan ki, ki kuma tuna rayuwar mace da na namiji a kwai ban-banci, Allah ya miki albarka".
Bayan munyi sallama da Daddy na ta shi na shiga na sake wanka, ɗauko jaka na nayi da niyyan na yi karatu amma abu ya gagare ni, a hankali na fita zuwa parlor na, na daɗe a tsaye ina jayayya da zuciya ta, shin na leƙa Dr ne ko kuma na bari, kada naje bai huce ba ya sake rarako ni.
Zuwa wani lokaci dai na haƙura na daure, ina zuwa bakin ƙofan shi zan fara knocking sai ɗaya daga cikin ƴan gidan mu mai suna Peter ya fito daga na shi gidan, yana ɗan murmushi ya ƙaraso inda na ke tsaye, yana kallo na da dariya kaɗan a fuskan shi yace.
"Preety me ya faru naga kina gudu Oga kuma ya biyo ki ran shi a ɓace? Any way ba sai nasan me ya faru ba, don nasan almost shekaru uku muna tare da shi anan, ban taɓa ganin yayi faɗa da kowa ba, babu ma mai zuwa gidan shi idan ba ke dana fara gani kin shiga ba, gashi kin saka naga ɓacin ran shi sosai ɗa zu, don na ba shi haƙuri amma naga ya fita a motan shi ran shi a ɓace".
Yana gama bayanin shi naji raina ya ɓaci, wato Dr yayi fushi ne shiya sa ya bar mun gidan? Hala ma wurin matar shi ya tafi domin ta kwantar mishi da hankali, ni kuma zuciya ta ta fashe ni ka ɗai ko? Hmmm dawo da kallo na nayi kan Peter ina murmushi, domin bana son ya fahimci wani abu, ina kallon shi nace.
"kasan shi cousin ɗina ne, so baya son yaga bana karatu, shi yasa ɗazu dana ce ni zanje na kwanta ne ba lokacin zanyi ba shi ne ran shi ya ɓaci, ni kuma na gudu ne ka da ya saka ni yi dole".
na faɗa ina ƙara murmushin fuska na.
Shima murmushin ya yi ya na ƙara gyara tsayuwar shi, yana duban cikin ido na yace,
"gaskiya preety baki kyauta ba, ai duk wanda ya ke so ka yi karatu shi mai son ka ne, kinga gaskiya ki daure kiyi karatu idan kina so ku shirya da brother'n ki, kinga shi mayen karatu ne fa".
Ya ƙara sa faɗa ya na juyawa da dariya a fuskan shi.
Ganin ya juya nima na koma nawa side ɗin zuciya ta cike da tunanin me yasa ran shi zai ɓaci irin haka? Nifa na gaya mishi gaskiya bani bace Aishan amma yaƙi yadda, to ko dai yana da wani problem ne a brain ɗin shi? Kai nasan ma ba shi da shi, kawai hala yana son Aisha ne yasa yake ga kaman mu ɗaya saboda nima suna na Humaira duk Aisha ne, to koma meye ne ohoo, ni dai bazan sake yadda ya mun maganan ta ba, kada wata rana naje ya mare ni, na faɗa ina zunɓura baki na gaba.
Har na kwanta barci babu alamar dawowar shi, ban ji daɗi a raina ba amma haka na kwanta, banda firgici da faɗuwar gaba babu abinda yau na keji cikin bacci na, wanda ko kaɗan bai mun daɗi ba, har a kayi asuba a haka na ta shi nayi salla, bayan nayi azkhar nayi karatun ƙur'ani na koma na ɗan kishingiɗa a kan sallayar.
Da safe ina tashi nayi wanka amma duk yadda na so na daina damuwa da rashin dawowar Dr abin ya ƙi barin zuciya ta, haka naje na dama quaker oats na sha a dole ba don raina ya so ba.
Wuraren ƙarfe 10:00 kiran Amal ya shigo mun, a hankali na ɗauka na kai kunne na, da ƙyar baki na ya amsa mata da sallaman da tayi mun, tambaya na tayi akan da yaushe zamu je shooping ɗin? Cikin kasala nace mata ta bari muje next week domin yau da ciwon kai na ta shi da shi, tausaya mun tayi sannan tace mu bari sai next week ɗin.
Ranar monday da naje school na ji ana cewa Dr Hussain yayi tafiya ba zai samu daman zuwa mana lectures ba, gaba É—aya sai naji na nemi nutsuwa na na rasa shi, haka aka yi ta mana lectures amma bana ganewa.