← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 66

Sashe 56

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyan zuciya nayi na mayar da kaina ƙasa ina wasa da wayan hannu na, kusa dani Ummi ta dawo ta zauna, murya a hankali tace, "Babanah! Aisha nina haifeta, bai kamata kubar sheɗan yayi galaba akan ku ba, ku daure ku ya fucheta a zuciyarku, dama akwai wani yayan matar Baba Umar da yace yana son Aishan har yayi magana wa Baban Narabi, amma ganin da mukayi Aisha yariyace, don yana da mata har da yara kusan uku, shiyasa bamu bada haɗin kai ba, don itama Aishan ta nuna bata so, amma idan munga zaku kawo mana tashin hankali wallahi zamu mishi magana ya fito, don ma yanzu baya ƙasan ne, idan ban da ku Aishan rabata za a yi wa ku biyun, ko kuma yayah kuke so ayi"? ta faɗa tana bina da kallo cikin tashin hankali daya bayyana a fuskarta lokaci ɗaya.

Hannunta na riƙo cikin nawa murya a hankali nace, "Ummi kiyi haƙuri kada abar Aisha ta auri wanda bata so, ni dai kawai bansan meyasa nake jin ta araina ba, amma Ummi baki tunanin ko an chanja miki ne a wurin haihuwarta? Don wallahi Ummi nifa son aure nake mata, nayi na daure naso wata yarinya da ta nuna mun tana sona amma firr Aisha ta hana zuciyata son kowa sai ita".

A razane Ummi take kallona, "Hussain É—ina, Aisha nina haifeta, bakaga irin kamannin da ta keyi dani ba? Babu É—ayan ku da yake kama ni bayan Aisha, wannan ma ae ya isheku ishara".

"hakane Ummi kiyi haƙuri, duk sharrin shaiɗan ne, kuma zamu kiyaye kinji, yaushe Aunty Hauwan zasu iso"?

Ummi tana murmushi tace, "sun wuce Narabi ne, suna fitowa nan zasu taho, kuma kutashi ku shiryah saboda taji daÉ—in ganin kun girma, ga Fatima idan ta girma ba sai a haÉ—aku da ita bama"?

Murmushi nayi ina kallon Ummi nace, "Ummi Æ´ar Fatiman nan wa zai iya jiranta? Maganan gaskiya ae Hassan ya miki É—azu, mu bazamu wani wuce next year ba zamuyi aure, kawai ki fara shiri ke dai", na faÉ—a ina dariyan jin kunya.

Dariya Ummi tayi sannan ta tashi tafita a É—akin.

Ana idar da sallaɓ la'asar su Aunty Hauwa suka iso, a lokacin Ameer bai wuce 11yrs ba, Fatima kuma bazata wuce 9yrs ba, yaran sunyi wani irin girma da kyau sosai, duk inda sukayi kallon su nakeyi, don wani irin kama da Fatima da Aisha da sukeyi har ya ɓaci, Uncle Abdallah kamo hannun Aisha yayi ya zaunar da ita gefe yana duban ta cike da so kaman shi ya haifeta, yana dubanta yace.

"Baby na haka kika girma? Yaushe zakizo mana hutu? Tunda naji Baban Narabi yace wai har mun fara samun surakune, kina son Muhammad É—in?"

Shagwaɓewa tayi ta kwanta a kafaɗan shi tana jijjiga kanta alaman ita bata son shi, ta buɗe baki tace, "Uncle nifa ya mun tsufah, ni nafi son miji irin Yayah Hussain, ni komai irin nashi nake so, don........." sai kuma tayi shiru ta rufe bakinta alaman ta tuna da wani abu, sai kuma tayi sauri ta kalli Ummi da ta zuba mata harara.

Dariya Uncle Abddallah yayi yana buga kafaɗanta yace, "kada ki damu baby nah, bazamu taɓa miki auren dole ba, asali ma wanda kike so zamu baki kinji baby nah".

Dariya tayi tana kallon uncle Abdallah tace, "koda yayah Hussain ne uncle"?

"koda kuwa Yayah Hassan ne", ya faÉ—a yana mata murmushi.

"Abdallah kutashi kuje kuhuta, bana son ka biyewa shirmen Aisha, taya zakana biye mata tana danganta kanta da É—an'uwanta a aure kuma? Kasan yaran yanzu ba hankali ne da su ba".

Dariya uncle Abdallah yayi bayan ya miƙe tsaye yana duban Abba yace, "Yayah kanajina da Ummi baka ce komai ba"? Abba yana kallon shi fuska a murtuƙe yace, "me zance maka naji kuna zuba shiririta kaida auta".

Dariya uncle Abdallah yayi ya dubie ni yace, "Hussain idan ka amince ni zan baka auren Aisha don naga babu mai burge ƴata a duniya irinka, tun tana yarinya na lura da hakan, inaga kai ɗin kaine zaɓinta".

"Uncle ae idan aure ne toh nine yakamata na auri Aisha, don nine babba kuma ni nake sonta ba Hussain ba, shi bai taɓa cewa kowacce mace yana so ba har yau, ni kuma ina sonta", Hassan ya faɗa yana duban Aisha da take hararan shi.

Kallonta Uncle Abdallah yayi yace "wai doughter haka ne"? Turo baki tayi gaba tana hararan Hassan tace, "nikan bana son shi yayah Hussain ne yake burgeni, kuma nagayawa Ummi ni kan idan za'a mun aure yayah Hussain nake so, amma tace babu aure a e tsakanin yaya da ƙanwa", ta faɗa tana kallon Ummin kaman zatayi kuka.

Tsawa Ummi ta daka mana da iya ƙarfinta, "ku wace kowa ya tafi ɗakin shi," sannan ta maida kallonta kan Uncle Abdallah, "Bana son haka Abdallah, baka taɓa ganin irin kalan nawa ɓacin ran bako? Haka kawai zaka zo ka ɗaga mun hankali acikin iyalina, kasan ƴan biyu ne su, wa zan bawa........." sai kuma tayi shiru tana dafa kanta, Abba da sauri ya riƙo hannunta, "kanne Ummin su"?

ÆŠaga kai tayi alaman hakan ne, sai lokacin Aunty hauwa da bata furta ko A ba tun lokacin da aka fara maganan sai yanzu, "Ummi BPn ki har yanzu yana yawan hawan ne"?

ÆŠaga kai tayi alaman haka ne yana yawan tashi.

Cikin tausayawa Aunty hauwa take mata sannu da jiki, sannan uncle Abdallah ya dubi Ummi da murmushi yace, "Adda Allah ya baki lafiya, daga baya sai mu gama maganan mu, don wallahi burin Baba Umar kenan, kawai bai gaya muku bane, amma ni nan yagaya mun, shiyasa banga dalilin da zai sa a hana yara su fahimci su É—in yayah suke a juna su ba"?

Ummi ta ɗago ta bishi da wani irin kallon tace, "haba Abdallah kasan yadda nake son Aisha kuwa? Ni so kake na zama bani da ɗiya ta mace? Bayan ko ita Hauwa ta manta da cewa Aisha ƴarta ce, ta haƙura mun da ita duniya da lahira sai kai yanzu zaka taso da abinda bazai taɓa kasancewa ba, idan nace zan aura mata Hissain toh Hassan kuma fah? Baka tunanin rabewan zumumcin yara nane? Gaskiya kubar maganan nan daga yau kuma anan wurin".

"Haba Adda ni baki son haɗa zuri'an ki danawa ne kam? Wallahi Ummi babu abinda nake matuƙar buri irin ace Hussain ya zama miji wa Aisha, amma ke narasa me yasa baki da wannan ra'ayin? Ko dai nice baki son haɗa iri dani"? Aunty hauwa ta ƙarasa faɗa idonta cike da ƙwallah.

Runtse ido Ummi tayi ta cije bakinta, a hankali ta dubi Aunty hauwa, "Hauwa wallahi son da nakeyiwa Aisha ban taɓa jinshi kan Hassan da Hussain ba, asali ma tun ranan da na fara tozali da Aisha Allah ya saka mun sonta, toh ta yayah kike ganin ƴar da nake jin kaman ni na haifeta na barta ɗana ya aureta? Kalan watarana ya ƙuntata mata ni kuma bazan iya ɗaukan hakan ba? Kuma idan na amince yayah kike tunanin Aisha zataji na tsawon lokacin da ban barta ta san kece mahaifiyarta ba? Kuma yayah zanyi da Hassan da Hussain? Wallahi dukkansu sonta sukeyi"., ummi ta karasa faɗi tana share hawayenta.

"Wallahi kamuwan ubangiji ne Adda, bai kamata ki nemi haramta abinda Allah ya hallata shi tsakanin bayin shi ba, ke yakamata ki danni É—aya daga cikin su, sai abawa É—aya, kuma wanda yafi chan-chanta Hussain ne, wanda tun son da ya nuna mata tana jaririya Mahaifinta ya gaya mun Aisha matar Hussain ne, idan sun girma zai haÉ—a wannan auren a tsakanin su", cewar Uncle Abdallah.

Kaman an jeho mu nida Hassan da tun fitan mu muke laɓe muna jin me suke cewa, Hassan da iya ƙarfin shi yace, "Wallahi ni zan auri Aisha, don kawai duk kunfi son Hussain sai kuce shi zaku bawa? Bayan shi ɗin bai taɓa cewa yana sonta ba, kunsan ton yaushe nake sonta"? Ya faɗa kaman zai sha kwalan uncle Abdallah.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[9/8, 11:01] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1442H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 45📑*

*__________📖* Rai a ɓace Ummi ta dubi Hassan tace, "Hassan nace bazaka auri Aisha ba, Aisha ƴa tace babu wanda ya isa ya chanja, ko ita hauwan ce ta matsa saidai mu rabu, don wanda yafita iko da ita ya mallaka mun ita duniya da lahira".

Duk illahirin jikin Ummi rawa ya keyi, nidai ganin haka sai na razana, don ban taɓa ganin Ummi cikin wannan yanayin ba, saboda hakaɓda sauri na ƙarasa jikinta, hawaye ne yafara zuba mun ina riƙe da hannunta nace, "Ummi na Aisha ƙanwar muce dukkan mu babu mai aurenta, Aisha ma baza tayi aure yanzu ba sai ta gama karatun ta, ita da kanta zata zaɓi mijin da ta keso Ummina, ki kwantar da hankalinki" na faɗa ina share hawayen idon Ummi.

"Hakane Aisha ta tabbata zata auri mohd kenan, ƙanin Aunty domin Baban Narabi auren ta kawai yake son ganin, kuma a irin halaccin da ya maku ya kwar da kanshi akan Aisha, ko na rana ɗaya bai taɓa nuna muku ko sa muku ido akan Asiha ba, ya kamata kuma ku daure ka bashi haɗin kai yaga auren Aisha da ran shi", Uncle Abdallah ya faɗa idon shi nakan Abba da Ummi.

Girgiza kai Abba yayi alamar maganan Uncle haka yake, sannan ya maida kallon shi kan Ummi yace, "Fatima naso ace kin haƙura da hukuncin Allah kin yarda an sanarwa Aisha cewa bake kika haifeta ba, idan yaso sai a haɗa aurenta da ɗaya daga cikin yaranki, kinga komai yazo mana da sauƙi, tuwo na maina, amma idan kika bari Aisha ta auri wani daban, tou daga ranan ta fita daga ikon mu, kuma ko ba daɗe ko ba jima zatasan bake kka haifeta ba", Abba ya faɗa da muryan rarrashin Ummi.
Chapter 56 · 0% Book details