← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 66

Sashe 19

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya nayi na miƙe tsaye ina kallon shi, a hankali nace , "to muje gida na soya maka egg ɗin da singulura ta kasa yi maka, muje na samu ladan ka".
yana dariya shima ya biyo baya na muka fita a class É—in.

Ko sauƙa a brandan class ɗin ba muyi ba muka ji ihu da buga desk da ƴan class ɗin suka yi, ina jin muryan wani yana cewa wallahi girl friend ɗin shi ce, Ezeh yana ta rantse musu akan uncle ɗina ne.

Kallon Dr nayi baki na a buÉ—e ina nuna mishi yaji mai Æ´an class É—in suke cewa, shima dariyan yayi ya dawo kusa dani yana cewa, "To girl friend É—in ne ko ni Uncle É—in ki ne?".

Tsayawa na yi da tafiyan ina kallon shi cike da mamaki nace, "kai kuma sai ka biyewa abin da zasu ce maka?".

"To ya ya zan yi da rigan da babu wuya? Nikam kawai yau baki isa ba sai kin gaya mun waye ni a wurin ki".

"Nikam ba bu ruwa na Dr, kai kawai Dr'n mu ne, kai malamin mu ne".

"ni dai baki isa ba sai kingaya mun a tsakanin abin da su ka tambaya".

Hararan Aunty Faraa nayi don ganin Hummy zata mishi bayani ita kuma ta wani daka tsalle tana ihu tana cewa,
"sai Dr da Hummy Allah ya bar ƙauna ta gaskiya".

da sauri Miss Xerks ta jawota da ƙarfi tace, "to kin yiwa kan ki, gobe baza mu ta ho da ke ba, kuma yau zan saka *NEAT LADY* ta turo jet ɗin ƴan gaskiya writers a koma da ke nigeria, saboda ihun nan da kika yi gashi kin sa ka sun yi shiru suna kallon mu".

Juyowa ta yi tana duba na irin na hana Miss Xerks sakawa a maida ta gida, hararan ta nayi nace,
"wallah komawa za kiyi yanzu yanzu ma, tun da ihu za kiyi a dinga jinmu, da naso ranan da za ace.........".

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

_*NANA FIDDAUSI, ƊIYAR JIKAR KULU WANNAN SHAFI NA KINE KYAUTA, ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR KI, YA KAWO MIKI ƘANNE MASU ALBARKA*_

*SHAFI NA 15📑*

*__________📖* Kan bed ɗina na faɗa ina kuka mai zafi a zuciya, ni na rasa me yasa na damu da sai Dr ya yaba ni, bayan nasan ba zai ta ɓa yabawa ba, gara ma nayi haƙuri kawai, ina cikin kukan naji an buɗe ƙofan ɗakin an shigo.

Dafa baya na naji anyi, wanda daga dukkan alamu Ummi ce, ban É—ago na kalle ta ba, amma na rage sautin kukan nawa.

"Tashi Aisha Humaira muyi magana kinji".
cewar Ummi, tashi nayi zaune ina ta sauke ajiyan zuciya.

Hannu na ta riƙe gam a cikin nata tana duba na cikin nutsuwa, a hankali ta jeho mun da tambayan da ya kusa sakani dariya, "Humaira kina son Dr ne?".

Kallon ta na yi kaman zanyi dariya nace, "Ummi son Dr kuma? Ni kam ban taɓa jin son shi ba, ni Ummi ba bu wanda na taɓa so a duniya irin Daddy na, sai kuma Amal da na ke son ta, ni bayan su bana son kowa".

"Har maman ki baki son ta?".
Kallon ta na yi ido na yana cikowa da hawaye, juyar da kaina nayi gefe sannan nace, "Mama na ta rasu".

Jawo ni jikin ta tayi ta rungume ni saboda ganin hawayen da ya fara gangaro mun, a hankali tace,

"Allah ya jiƙan ta da rahma, Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya na rashin ta".

ni dai ban ce komai ba ina dai kwance a jikin ta nayi shiru hawaye yana bin fuska na, tun ranan da na bar ƙasar mu na daina zubar da hawaye na rashin Mama na, amma yau kuma kewar ta ya dawo mun zuciya ta mai rauni.

_*ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU DA SU KA RIGA MU GIDAN GASKIYA, TABBAS RASHIN UWA WANI BABBAN MIKI NE WANDA BAYA CIKEWA, DUK WANDA TAYI RAYUWA BABU UWA GASKIYA ABUN TAUSAYI CE 😭😭😭ALLAH KA KAI HASKE A KABARAIN MAMA NAH!* 👏🏻👏🏻

"A hannun wa kika tashi?".
ta jeho mun wani tambayan kuma.

"Hannun Daddy nah da matar shi wanda muke ce mata Mama, tana da yara guda uku, Yaya Ahmad shine babba a cikin yaran ta, sai kuma Yaya Aliyu shike bin shi, sai Yaya kabir shi ne ƙara min su, shi kuma ya bani 2yrs, yanzu haka yana karatu a ATBU, ni kuma ni kaɗai Mama na ta haifa, kuma ni kaɗai ce ƴa mace a wurin Daddy nah, shi yasa ya ke sona sosai".

na faÉ—a hawaye yana É—an bin fuska na kaÉ—an kaÉ—an ina sharewa.

"Hummy tunda kince ba son Dr ki ke yi ba, to zan baki shawara a matsayi na na mahaifiya a gare ki, daga yau ki daure ki daina damuwa idan baice kina da kyau ba, ko baice kin iya abinci ba, yaga kin damu ne shi yasa yake bawa zuciyar ki wahala, saboda duk ranan da ya tunkari zuciyar ki bazai samu matsala ba, saboda ya gama lugwaigwaita ta da soyayyar shi, kowa ya ganki yasan tsakanin larabawa da indiyawa sai anyi da gaske a samu mai irin kyawun ki, saboda ranan da na fara ganin ki na É—auka aljanu ne zasu buÉ—e mun ido, Humaira ke É—in É—iya ce mai kyau da daraja, kada ki yadda da ga yau Dr ya sa ke saka ki kuka kin ji, daga yau ki nuna mishi baki son yabawan shi tunda ke mai kyau ce, kuma kin iya girki mai daÉ—i da kwanci a zuciya, domin ina hankalce da shi, lomar farko da yafara yi sai da ya lumshe idon shi don daÉ—i, saboda haka ko ya faÉ—a ko kada ya faÉ—a, girkin ki ya mishi daÉ—i".

ta faÉ—a tana mun murmushi, saboda ganin nima na ke ta murmushi.

"Humaira kin ji daÉ—i ne da nace miki yaji daÉ—in girkin?".

Dariya nayi ina É—aga mata kai alaman na ji daÉ—i.

Lumshe ido tayi ta buɗe a hankali, a zuciyar Ummi tana jin tausayi na, domin tasan babu yadda za tayi na riga da nayi nisa a son Dr, sai dai fatan Allah yasa shi kuma ya riƙe amana, tasan komai zai ta gaya mun ba zaiyi tasiri ba, saboda bani da wayon da zan fahimce ta, saboda shi wayo bawai a shekaru bane, kawai baiwa ne, wasu kuma zama da iyaye suna nusantar dasu abinda ya kamata shi ke sakawa su fahimci rayuwa, wasu kuma irin mutanen da suka zauna dasu yake sakawa su fahimci rayuwa, amma abin tausayi tasan ni nayi rayuwa ne da giɓi na rashin uwa.

"Ummi to ya ya ake jin so É—in?".
Na jeho mata tambayan da ba ta yi tsammani ba.

Shiru tayi na wani lokaci, sannan ta É—ago ni zaune tana duban fuska na,

"zaki na yawan tunanin mutumin, Za ki na yawan jin kishin wata akan shi, za ki na yawan jin tausayin shi, Za ki na son kina yawan ganin shi, ba za ki na gajjiya da jin muryan shi ba, Za ki na so kiga komai ki ka yi ya yabe ki, Komai aka faÉ—a na laifi akan shi baza kina gani ba, zai zama kullum hasken shi ki ke gani
Za ki na ......".
abubuwa da yawa Ummi ta lissafo mun akan yadda za ka ji kana son mutum.

Da sauri na dafa zuciya ta ina lumshe ido na, duk wani tsoro naji ya kamani, a hankali na sa ke buÉ—e ido na ina kallon Ummi, "Ummi daga shekara nawa ka ke ji ka fara son wani?".

Dariya ta yi mai ɗan sauti, sannan ta dube ni tace " soyayya bata da shekaru, ba ta da lokaci, ba ta shawara, bata zaɓe, duk lokacin da Allah ya hukunta za ka fara to babu makawa ko kashirya mata ko baka shirya ba zaka fara".

"Na shiga uku Ummi, to wallahi zuciya ta tana son Dr Hussain, amma ni kam bana son shi Ummi".
na faÉ—a ido na yana cikowa da hawaye, saboda gaskiya ni ban shirya yin soyayya ba, kuma bamuyi haka da Daddy na ba.

"To ita kuma zuciyar ki ta shirya karɓan soyayya'n Dr, to ya ya za kiyi kenan?". Cewar Ummi.

"Ummi ni kam bana son shi".

"Me yasa baki son shi? Yana da wani problem ne?".

"Ummi ni fa saurayi na ke son aure kuma yaro iri na, amma shi fa yana da mata, kuma ya yi mun tsufa, kuma Daddy yace mun kada nayi soyayya da kowa saboda maza basu da kir ki".

Shiru Ummi tayi har zuwa wani lokacin tukun tace, "to ai ke baki da Laifi, tun ke baki san kin fara son shi ba, kawai yanzu abu É—aya za kiyi ki kare kan ki".

Da sauri nace "me zanyi Ummi"?

"Kada ki gayawa kowa kina son shi, ko da Amal ce, shima kada ki bari ya gane kina son shi, don zai gayawa Daddy'n ki, itama Amal idan taji zata gayawa Abbu'n ta, shi ma zai iya faÉ—awa Daddy'n ki".

zaro ido nayi ina duban ta da tsoro, sannan a hankali murya can ƙasa nace, "Ummi to ai bazan taɓa gaya mishi ina son shi ba, ban ma san ina son shin ba".
na faÉ—a kaman zan yi kuka.
Chapter 19 · 0% Book details