← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 66

Sashe 48

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyan zuciya Umma halima tayi, "Amina wallahi tun rasuwar Umar Allah yaga zuciyata naso Abdallah ya auri matar nan hauwa, saboda gaskiya ƴar mutuncine, amma Abdallah yaƙi ɗaga kai, toh ni muna zumunci da iyayenta sosai, yau baifi sati ba Mamanta ta ke gaya mun wani likita a wurin aikin su ya tura manyan shi domin neman auren ita hauwar, kuma iyayenta sun amince da shi, yanzu maganar danake miki ma zuwa nanda wani watan auren za'ayi".

Share hawayen ta Aunty hadiza tayi ta dubi Umman su tace, "toh Umma ayi wa Baba magana mana a tura maganan yayah Abdallan, ina ga ae zasu fi sun na yayah Abdallan akan wani daban", ta faÉ—a kaman zatayi kuka.

Shima Abdallan shiru yayi yana jiran yaji mai Umma halima zata ce, amma abin mamaki sai Umma Halima tace, "gaskiya bamu isa yanzu mu tura maganan Abdallah ba, bayan tun farkon rasuwar Mahaifinta sai da yayi magana da Baban ku akan ko zai tuntuɓi Abdallah akan Hauwan? Amma firr Abdallah yaƙi maganan, toh yanzu kuma ae bamu da bakin cewa muna so".

Tashi yayi bai ce musu uffan ba ya bar cikin É—akin Umma haliman, dukkan ido suka bishi da shi babu wanda ya hana shi fitan da zaiyi.

Aunty hauwa tana zaune a gidan wani cousin ɗinta wani likitane, yayah Aunty Ummi matar uncle auwal, yana zaune a cikin drs quaters da take kusa da asibitin, da yake night duty ta keyi ranan tana gida babu inda taje, suna zaune da matar yayan nata mai suna Aunty uwani, matace mai matuƙar kirkin gaske, duk yadda mutane suke nuna mata illar zaman Aunty hauwa a gidan ta bai dame ta ba, kowa yana ce mata mace kyakkyawa kuma yarinya ƙarama bata tsoro ta aure mata miji? amma ko kaɗan bata kula su, a haka har Aunty hauwa ta haɗu da wani Dr ɗan garin Azare wato Dr basheer.

Suna zaune akan dinning ita da Æ´ar Aunty uwani mai suna Nabeeha, tana ta mata assignment É—in da aka bata, ita kuma Aunty uwani tana cikin parlourn tana zaune tana kallon wani indian film.

Ringing wayan Aunty hauwa ya fara, ganin baƙon number ta daɗe tana kallo har sai da ya kusa tsinkewa tukun ta ɗauka, "idan kina gida ki fito ina ƙofar gida", abin mamaki ya bata, ɗago wayan tayi ta duba numbern sannan ta mayar da wayan kunnenta tace, "ban gane da wa nake maganan ba, don banida number"?, "Baban Aisha ne, kina gida ne"?

Jiki a sanyaye ta amsa mishi da "ehh" bai jira wani abu ba ya kashe wayan, shiru tayi tana duban Aunty uwani da ta ke kallon ta ita ma, ta gane mai wayan tun ɗaukan ta taji irin muryan Baba Umar, amma tsoronta shine, bai taɓa ƙiranta ba a rayuwar shi, toh ko lafiya yau yazo har inda take"?

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/25, 13:41] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1442H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 39📑*

*__________📖* Bata daɗe ba ta fito daga cikin gidan, hannunta ɗauke da tray, har inda yake ta ja table ta ɗaura akai, juq ne cike da zoɓo mai ƙamshin gaske, sannan cooler kuma cike yake da jaloop rice, wanda yaji kayan haɗi har da hanta, bayan ta zuba mishi ne ta koma cikin gidan ta barshi a wurin.

Busmillah yayi ya fara cin abuncin yana ɗan sipping zoɓon kaɗan-kaɗan, sai wani lumshe ido yakeyi na jin daɗin zoɓon, haka yayita ci har yaji ya ƙoshi, bayan ya gama ne ya ɗauki jug ɗin ya cika shi da zoɓo, sannan ya ɗauki wayan shi ya danna ƙiran Aunty hauwa, tana ɗauka yace, "ki fito nagama".

Zama tayi a kan kujeran sannan ta fara gaishe shi, bayan sun gaisa ta ce, "naganka kwatsam ina fatan ba wani abu mukayi maka ba ko"? ta ƙarasa faɗi tana duban shi, murmushi yayi mai kyaun gaske yana kurɓan zoɓon yana kallon ta har cikin idonta, sannan yace, "nazo tafiya da ke ne".

Hararan shi tayi, "ni kayace da zaka zo kace zaka ɗauke ni ne"? Murmushi yayi yace, "zanje na aurar da ke ne, don naji ance baki iya zaɓe ba kin zaɓo mana wani sunduƙi", ya ƙarasa faɗa yana ajiye cup ɗin zoɓon.

"Hmmm batun yau ba na ke zaɓo sunduƙan ba kenan, tunda bashi kaɗai na fara zaɓa ba", fuskan ta a murtuƙe ta faɗa masa.

Zuba mata ido yayi batare da yace komai ba, hakan yasa ta kasa cigaba da maganan ta ta sunkuyar da idonta ƙasa.

"Hauwa bana son wannan auren da kike shirin yi, domin ina kishin wani ya aure matar É—an'uwa na, saboda haka ni nan zan aure ki domin kada ki haÉ—a mana zuri'a da wasu irin kuma daban".

Tashi tayi tsaye tana bin shi da wani irin kallon mai cike da raini a ciki, "lallai Abdallah idonka baya cike da kunya, ni matar yayankan zaka duba kace wai ni zaka aura? Toh a wani hujjan? Ina ce ana wannan auren idan da akwai yara a tsakani ne? Toh ni babu wani sauran abu a tsakanina da kai, yarinya kuma ko nayi aure ba wurina zata zauna ba ballantana kace zataje gidan wani baka so, saboda haka gara ka farka daga baccin da kakeyi, ni Hauwa nafi ƙarfin na auri yaro mai raina mutane irin ka, kaje chan ka ƙarita da tsohuwar matarka ni bana so", tana faɗa ta juya cikin gidan ta bar shi zaune a parlourn yana murmushi mai cike da ɓacin rai.

Kuka ta keyi mai ƙarfin gaske inda taje ta samu Aunty Uwani ta zube tana ta kuka, Aunty uwani duk ta ruɗe sai tambayarta ta keyi mai ya faru amma taƙi faɗa mata komai sai kuka da ta keyi, ganin bazata kula ta ba yasa, ta wuce parlour wurin Abddallah, inda ta samu ya miƙe yana shirin tafiya.

Bayan sun gaisane ta tambayeshi abin da ya faru, cikin girmamawa ya gaya mata komai, yana kuma ƙasƙantar da kai alaman yana neman ta tsaya mishi akai, Aunty uwani ta yaba da Abdallah shiyasa ta bashi tabbacin zata samu ɗan'uwanta da maganan, shi kuma godiya yayi mata ya kama hanyar shi sai misau.

Tunda ya isa Bappah yake ta nannan da shi, bayan kuma ya gaya mishi abinda ya kawo shi, Bappah ba ƙaramin jin daɗi yayi ba, ƙiran Uncle Auwal yayi a waya yazo ya same shi, bayanin komai Bappah yayi mishi, shima abun yayi mishi daɗi, domin sanin kirki da karancin iyayen Baba Umar.

Bappah ya ƙira Abba ya gaya mishi duk abinda ake ciki, Abba ya nuna farin cikin shi amma yace a haƙura har sai ita Hauwan ta amince, sannan Bappah ya ƙira Baban Narabi ya zayyana mishi komai, shidai Baban Narabi murmushi yayi, a zuciyar shi yace dama yasan za'a rina wai an saci zani mahaukaciya.

Uncle Abdallah a misau ya kwana, da safe ya kama hanyar bauchi, lokacin da yaje yayi dai-dai da dawowar Aunty hauwa daga duty, tana ganin shi ta wuce bata kula shi ba, ko damuwa baiyi ba, wucewa kai tsaye yayi har parlour yayi salllama, inda Aunty uwani da yayan su Aunty hauwa suke zaune, wurin zama suka bashi cike da kulawa, bayan sun gaisa aka haÉ—a mishi breakfast, amma yace musu yayi a misau.

Zama sukayi shida dr Alƙali, yayan su Aunty hauwa sukayi magana mai muhimmanci, amma firr Aunty hauwa da aka mata maganan taƙi basu haɗin kai, da yake Dr Alƙali ba mai yawan magana bane sai yabawa Abdallah haƙuri akan ya tafi zai shawo kanta daga baya, babu yadda ya iya haka yayi musu sallama ya tafi, Abdallah irin mutanen nanne masu ƙin yadda suga sun faɗi a neman abu, kuma shi idan yaso abu nacin shi yana dayawa, ballanta wannan da yake ganin idan ya rasata toh zai sha kunya, a ransa ya saka duk abinda zatayi zai daure, don shi Allah kaɗai yasan irin son da yake yi mata kawai ƙarfin hali ne da kuma kada a gane ya damu da ita shiyasa bai nuna ba, kuma a tunanin shi ae Hauwa yarinya ce, dole zata koma tayi karatu ne bawai maganan aure ba, hakan da yayi niyyah ya saka shi wucewa Narabi.

A parlourn Baban Narabi ya zauna ya dinga sauƙe mishi rikicin shikan aje a nema mishi auren hauwa, inda hali ma a tafi da sadaki, Baban Narabi ƙura mishi ido yayi har na tsawon lokaci, saida ya karanci ehh tabbas Abdallah da gaske ya keyi son Hauwa ya keyi tsakani da Allah, sai yayi gyaran murya yace, "toh in banda abinka Abdullahi tun yaushe aka bika akan ka aureta kaƙi, sai yanzu da yarinya ta haɗu da wanda ta keso zamuje muce ga zance ga magana? Ina ce Aishan ko ka aureta ba baka ita za ayi ba, toh meye dalilinka na auren Hauwa?"

Kallon Baban yayi sannan ya sunkuyar da kanshi ƙasa, "nidai Baba ina sonta ne, ae nima zata haifa mun irin Aishan, ko basu bani riƙon Aishan ba hala ta haifa mun mai kama da Aishan".

Dariya baba yayi yana duban Abdallah cike da ƙaunan ɗan na shi yace, "Abdallah wato kaima sake zakayi hauwa ta sake haifan me kama da ita ba mai kama damu nan ba ko? Wani irin so kukeyiwa Hauwa ne kam"? Baba ya ƙarasa yana murmushi mai cike da jin daɗin al'amarin.

Sunkuyar da kai Abdallah yayi ƙasa, "Baba don Allah kuje ko gobe nema, naga hauwan so ta keyi ta mun yarinta, gara aje da wuri kada ta auri wancan ɗayan, ni bana son zamanta a bauchi ma wallahi don zasuna haɗuwa".

Wannan lokacin dariya mai ɗan ƙarfi Baba yayi, yana duban Abdallan cike da mamakin irin nashi kishin, "toh ka gayawa ita maiɗakin kane zaka ƙara aure"? Baba ya jefa mishi tambaya.

Abdallah ya dubi Baba yace, "Banida matsalah da Fadilah nidai damuwata a fara zuwa gidan su hauwan".
Chapter 48 · 0% Book details