← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 66

Sashe 66

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A bauchi Aunty hauwa ce ta sauƙi mutane, inda Aunty Fatima da su Aunty Ummi da Aunty Indo ne suka ɗaukoni, kai ranan gaba ɗaya ahalin Baban Narabi ƙannen Kakana duk sunzo, inda duk yadda akayi da Uncle sabo da Uncle Abdallah kada su mun komai ƙi sukayi, domin Mota ko wannen su ya saya mun, domin Daddy na da Ummi da Abba sun cika mun gida na da gadaje masu tsadar gaske, ita kuma Aunty Fatima cewa tayi kada kowa ya sayi kayan kitchen, don itace uwa ita zatayi, lokacin dana leƙa kitchen ɗina kuwa ba ƙaramin kuka nayi ba, domin nikan yanzu bazan iya cewa nayi maraicin uwa ba, dama Daddy bai taɓa barina nayi kukan rashinta ba, yanzu kuma da ya sakewa zuciyar shi yabarni cikin familynta sai naji duniya bani da abinda yafi so.

Abin dariya Uncle Hassan da baby suma sukace dole abar musu side É—in Baby, wai suma zasuyi kayan uba a matsayin su na yayun Mummy, kowa ya ga irin kayan da suka zuba a ciki sai yayi santi, domin É—aki biyu ne da parlour a side É—in baby, kuma babu irin kayan alatun da basu zuba a ciki ba.

Side É—ina ma parlour ne da 3bedroom, shima babu irin kayan da Daddy na bai zuba ba, nidai gaskiya naga gata a wurin Æ´an'uwa na, inda kuma dama anyi zama domin magana su Amaal da Faisal, haka Abbu yace ya bada Amaal wa Affan, amma ya sanar musu sickler ce, haka su Uncle Auwal suka bada Jeedderh wa Faisal, an tsayar da maganan aure har sai Amaal ta gama karatu, ana gama biki washe gari su Abbu suka wuce saudi, inda mukayi kuka nida Amaal kaman ba nan da 1week zamu haÉ—u ba.

Bayan kowa ya watse ne Uncle Hassan ya rako Baby, har parlour na suka shigo, abin dariya ya bani inda Baby yazo "wai ke ƴan mata ki fito ki gaisa da abokai na suna parlour," ɗago da kai nayi na ɗaga mishi kafaɗa alaman bazan fito ba, murmushi yayi ya ɗaga murya da ƙarfi yace, "Uncle Hassan tace bazan fito ba ka tafi saida safe" da gudu na tashi nayi hanyar parlourn ina, "uncle Hassan Allah bance ba, gani na fito", dariya dukkan su sukeyi inda Baby ya fito ta bayana yana ta dariya.

Wuri ɗaya suka zauna, inda ban taɓa tsayawa naga irin kamanini su ba irin na yau, domin kayan su iri ɗaya ne, zaman da sukayi ma iri ɗaya ne, gashi dukkan su yau fuskar su ɗauke da farin glass yake, murmushi nayi nace, "uncle kuna kama fa".

Dariya yayi ya fara bani labarin lokacin da suke school, yadda yake zuwa yace wa yarinya yana sonta, ranan da ta ganshi da wata sai yace bashi bane É—an'uwan sa take nufi, kuma basu gane su, hakan sukayi ta ban labarin yarintar su ina dariya, duban uncle Hassan baby yayi yace.

"Bros ka tashi ka tafi wurin mama Fatima, domin ni yau aikin furta I luv u ne akaina har asuba, inda hali ka taho mun da maganin ciwon baki, don tabbas yau leɓe ne sai sun kunbura da furta I luv u wa baby da zan tayi", dariya suka saka gaba ɗaya, Uncle Hassan yace, "gaskiya ban mantaba, kasha gaya mun duk daren da kayi aure kwana zakayi kana gayawa mai sa'ar matar ka kalman so".

Na ɗauka wasa baby yakeyi, bayan tafiyar Uncle hassan wanka mukayi, ya ɗauko mun wata white rigar bacci, shima kuma white ɗin ya saka, duk muka feshe jikin mu da wasu turaruka masu ƙamshin gaske, haka na zauna a tsakiyar gado inda baby ya umurceni da na zauna, zama shima yayi ya tanƙwashe ƙafan shi irin tadda nayi,don har gwiwarmu suna haɗuwa dana juna.

Tun ina ɗaukan abin wasa har na fara karaya da irin kalaman soyayyah da baby yake gaya mun, sannan duk bayan wasu lokuta zai nuna wani wuri a jikina yace, "baby idon ki yamun kyau, baby ƙwayar idonki yafi komai kyau a jikinki, baby ban taɓa ganin kyaun lips irin naki ba, baby dubi kyaun gashinki, ban taɓa ganin mace mai kyaun tsari na halittah ba irin naki," kuma duk inda zaiyi misali da shi sai hannun shi ya kai wurin.

Duk yadda nake tunanin zan iya bacci amma kasawa nayi, gaba É—aya ma sai naji wani hawayene mai masifar yawa yana bin fuskana, a hankali na furta mishi, "ina sonka Baby! Ina sonka baby nerh!!.

Rungumeshi nayi da ƙarfi bayan munji an fara ƙiran sallan asuba, ranan gaba ɗaya familyn mu suka zo mun sallama, kowa ya koma inda ya fito, nidai duk inda naga baby sai naji anƴa akwai matar da tayi dace da soyayyan miji kuwa irin nawa? Gaskiya ina son Baby.

Da dare haka baby ya ɗauko mana wasu kayan baccin masu ruwan sky blue, gaba kyaun su yafi na daren jiya da muka saka, a daren yau na ɗauka baby zai ci gaba da baiyana mun sirrakan zuciyar shine da baki, ashe nayi kuskure, soyayyar da ya ƙunsheta mai zafin gaske a zuciyar shi ce yau ya sauƙe mun ita a aikace, ranan nayi danasanin irin yadda nayita buɗe bakina ina kwwankaɗan tsumin Aisha Garkuwa da gumbarta da na sha, kai hattah wannan haɗin kazarta da haɗin nasha da kankanan danayi amfani dasu nayi dana sanin amsa a wurin Ummi babu musu na dinga ci.

Aunty Fatima nane tazo tayita faman rarrashina ranan, don firr baby ya kasa gane kaina, daga tayi magana tace "haba doughter babyn kine fa", da karfi zan fasa mata kuka nace, "mummy babban mutumin ne zaki ce mishi baby? Na daina ce mishi baby, kawai Baban mutum sunan shi", haka zan faɗa ban lura ba Aunty Fati kuma sai ta ɓingile da dariya tana, "haba babyn baby".

Muna gama school akayi auren Amaal da Affan, Faisal da Jeederh, lokacin kuma da ƙyar nake jan cikina wanda yayi nauyin gaske, haka muka zauna a gidan Ummi don firr naƙi komawa namu gidan, don gaskiya bazan iya da fitinar baby ba, don ko duba yanayina bayayi, haka na zauna a wurin Ummi na.

Ranan talata na tashi da naƙuda mai matuƙar wahala, wanda dama lokacin Uncle Abdallah sun dawo nigeria da zama, suna zaune a cikin garin jos, haka Ummi ta ɗagawa kowa hankali, babu shiri Aunty hauwa ta tattaro ta taho bauchi, itama Aunty Fatima Ummi bata barta ta huta ba, domin ko arba'in batayi da haihuwar ɗanta ba, amma haka tayi ta ƙiran su, Aunty hauwa tana isowa ko rabin awa banyi ba na haifi ƴan biyu na dukkan su mata.

Ummi tana ganin su ta dubi Baby tayi mishi gwalo tace, "mu aka sake zubuwa sak, kai Hauwa nida ke jininmu yana da ƙarfi, ko kuma nace jinina na da ƙarfi, hauwa kika biyo kamanni na, Aisha ta ɗauko mu, Fatima ta biyomu, Humaira ma mu sak, gashi wasu ƴan biyun yauma babu maraba damu kenan".

Murmushi Aunty hauwa tayi tace, "waƴannan sun nuna mana so ne fisabilillah, da yake Adda bata haife mu a ƴanbiyu, kan Baba ƙarami ya fito kafin ni ya shiga tsakanin mu da rusheshen kai, sai yanzu Allah ya hukunta Hussain ɗinmu zai haife mu a tare, saboda haka, wannan da ta fi ɗan cikan fuska da kyaun sajen ita ce ni, wato itace *HAUWA'U KULU MAIJIDDAH* wannan mai ɗan dogon hanci da sirirn fuskar kuma kece Ummi na Adda na, itace *FAƊIMATUL ZAHRA'U*" ta faɗa tana dariya.

Baby ma dariya yayi yace shikenan babu komai, next time masu kama dani za'a haifa Æ´an mazaje a saka musu *ABBA NA DA BABA UMAR*

DaÉ—i Ummi ta keji kaman ita ta haife su, Allah ya gani tana son yara mata, bata haifa amma ga Æ´ar uwarta da zuriyarta suna ta haifa mata, haka suka koma gida akayiwa yaran wanka, kayan sanyi farare masu kyaun gaske aka saka musu, kowa yazo ya gansu sai yaji kaman ya lashe su.

Aunty Fati tana zuwa ta fara santin yaran, haka ta fara cewa ita za ayiwa takwara ita da Mummy na, amma harara ta samu daga Aunty hauwa tace, "har kunfi mune nida Ummi nah"? Haka kowa ya haƙura ymranan suna ƴanbiyu suka ci sunan su Ummi, inda muke musu laƙani da *NASREEN* da *NABEELAH*.

_AYAU NAKAWO ƘARSHEN LABARIN BABYN BABY DA HUMMY, WATO *ƘADDARA TA RIGA FATA* INA ROƘON ALLAH KUSKUREN DA MUKAYI ACIKI ALLAH YA GAFARTA MANA, ABINDA MUKE SO KUMA MU ISAR MAI KYAU ALLAH YASA YA SAMU ISA, WANNAN SHAFI NA SADAUKAR DA SHI WA QUNGIYAR *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ƘARƘASHI JAGORAN CIN BESTY NA *MISS XERKS* GASKIYA BAKI BAZAI IYA FURTA MIKI KALMAR GODIYA DA ƊAWAINIYA DA KIKAYI DANI TUN DAGA FARA RUBUTA WANNAN LITTAFI BA HAR ZUWA YAU, WANDA SUKE ƘIRANA SUYI MUN GODIYA DA JINJINAWA AƘAN WANNAN BOOK, DA WANDA SUKAYI TA WATSA MUN BOOK ƊIN NA DON YA ISARWA MUTANE NAGODE MUKU SOSAI_

*HUSSAIN 80K*
*JIKAR KULU*
*DR MOHD ATK PALACE*
*AUNTY SIS*
*AISHA MUSA BABA*
*DA DUK WANDA SUKA MUN POSTING BOOK NAGODE SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI*

*ƘAWATA BEBI S DAWAKI*
*ZEE YAWALE*
*FATI YAWALE*
*GODIYA MAI TARIN YAWA A GAREKU*

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
Chapter 66 · 0% Book details