← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 66

Sashe 65

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yayi ya kamo hannu na na dawo kusa dashi yace, "ki kwantar da hankalin ki uncle babyn baby naki ne ke kaɗai, kuma daga yau na baki shi kyauta, ni zan biya sadaki ma kafin Umma taje tayi kwaskwarima ta ƙwace miki shi, kuma Ummi ni da Aisha ne kaɗai ƴaƴanta, ke kuma jikace ke da baby, Aunty hauwa ce maman Baby, nida Aunty Fati kuma mune iyayenki, ni yanzu Baby ma ɗa yake mun", ya faɗa yana wani ɗaure fuska yana hararan Aunty Fati irin kada ta kawo mana wargi.

Tsaki Umman misau tayi ta harari inda Drn mu yake zaune tace, "ni kuwa idan kun kwantar da hankali ku me zanyi da wannan tsohun tuzurun? Mutum saida ya ninka shekarun mijina a duniya kafin ya rasu zan so? Ni ae ko kyauta aka ban Hussaini bana so, kede da kika ga zaki iya kije chan ki ƙarata da sauran majina", .......... Parlourn kowa dariyan maganan Umma akayi, inda aka zauna aka cigaba da hiran bayan rabuwa.

Bappan misau ne ya ƙara mana bayani akan hallacin da yake tattare da auren mu da Dr, inda kowa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali, kai wannan rana baxan taɓa mantawa dashi ba a tarihin rayuwata, don kuwa naga zumunci na ƴan'uwan mahaifiyata, don kuwa dukkansu da ƴaƴan su suka zo.

Uncle Auwal yana da yara shida Aunty Ummi guda huÉ—u
Affan, Aisha mai sunan mummy nah, Zahra mai sunan Ummi, sai khalifah mai sunan baban su Aunty ummi.

Uncle Baba kuma yaran shi guda uku ne, Babban mai sunan Bappah ne inda suke ƙiran shi da Ammar, na biyun kuma mai sunan Baba Umar ne, inda suke ƙiran shi da Khalifah, sai ƙaramar kuma mai sunan Aunty hauwa inda suke ƙiranta da Jiddah, kuma naga alaman ba ƙaramin su Uncle Baba yakeyiwa yarinyar ba, don duk abinda yakeyi zakaji yace na Jeddah ne, duk abinda yaro zai taɓa zaice kubari na jiddah ne, ita kuma yadda kasan Aunty hauwa da faɗa haka ta ke.

Washe gari zuwa dare su Aunty hauwa suka iso garin Abuja, da ƙyar suka kwana da safe suka kamo hanyar garin bauchi, da yake jirgi suka biyo da wuri suka iso, don wasu ma basu tashi a bacci ba suka iso.

Gdan su Ummi yana da girman gaske, ga guest house mai kusan threebedroom har biyu, Ɗaya aka sauƙe su Ummi da su Abba a chan, ɗaya kuma mutanen misau aka ajiye a wurin, shi kuma Daddy na a ɗakin da yake parlourn Abbaha kuma side ɗin su Drn mu da Uncle hassan, inda ana uncle Baba da Uncle Auwal suka sauƙa, uncle Hassan gidan su suka tafi tare da Drn mu, side ɗin mummy na kuma Umma da su Mama da Addagana suka sauƙa, nidai ƴar lele a ɗakin Ummi na kwana tare da Amaal, amma Amaal da wuri tayi bacci, nida Ummi kuwa kwana mukayi muna hira, rabi gaba ɗaya labarin rayuwar Mummy na take ta bani, wani lokacin ta tsaya tayi kuka, wani lokacin ta girgiza kanta tayi murmushi, har sai wurin 4 na dare bacci ya sace mu.

Zuwan Aunty hauwa da Uncle Abdallah wani kukan kuma ya sake tashi, domin ranan na tabbatar Aunty hauwa ba ƙaramin so ta keyiwa iyalan Ummi ba, don daga Uncle Hassan da Drn mu gaba ɗaya haɗa su tayi ta rungume su tana kuka, da ƙyar Bappah ya mata magana ta haƙura tayi shiru, gaba ɗayan su sakata sukayi a tsakiyar su, ita kuma dukka hannayenta suna ɗaure akan su kaman zata maida su cikinta ta keji.

Bayan hira da gaisuwa da akayi a tsakani, Abbu yayi wa kowa bayani dangane da abinda ya faru da mu a saudi, da kuma dalilin daya kawo Drn mu yabada labarin shi, da zuwan Daddy na, gaɓa ɗaya kowa saida ya jinjinawa Dr irin son da yake mun, daga baya Bappan misau yayi mana nasiha mai ratsa jiki da kuma yadda da *ƘADDARA* mai kyau da marar kyau, inda yake cewa da babu wanda bai so auren Aisha da Hussain ba, amma ashe babu rabon auren a tsakanin su, gashi kuma da akayi haƙuri itama tayi biyayyah wa iyayenta gashi abinda ta haifa mafi soyuwa a gareta zata auri abinda itama taso sama da komai a rayuwarta, ya cigaba da duban fuskar kowa har ya kawo kan Aunty hauwa, murmushi yayi yace.

"Hauwa kinga ikon ubangiji ko? Babu abinda kike so sama da kiga kin haÉ—a zuri'a da Æ´ar'uwarki, sai gashi alokacin da kika so Allah kuma bai nufa ba, dama haka iko na ubangiji yake abinda kake ganin shine dai-dai agareka sai kaga wurin Allah kuma ya chanja maka da wani indai har kabar mishi dukkan al'amuranka, gashi yau Hassan ya auri Æ´arki ta cikin ki, ga shi kuma Hussain da rawar kai ya tsallaka ya tafi har kan jikarki, don tsabar basu son wani ya kwashe musu iyalen maman nasu duk suka handame a tsakanin su", Bappah ya faÉ—a yana duban Hassan da Hussain da dariya.

Uncle Hassan ne ya buɗe baki yace, "dik wanda yayi zagin kasuwa yasan da wa yake, don tabbasa kaso Fatima ni kuma na ƙwace maka shiyasa kake gugan zana ɗan tsohu",

Ranƙwashi Abba yayi mishi yana dariya yace, "mai Bappah zaiyi da zabiyar matarka", dukkansu dariya sukayi, sannan muka shiryah mukaje Narabi mukayi ziyaran ƴan'uwa.

Tunda Affan ɗan uncle Auwal ya ƙyalla ido akan Amaal gaba ɗaya ya susuce gashi ba mai yawan magana bane, yadda kasan Uncle Auwal haka yake da shiru, amma duk hankalin shi da idon shi yana kanta, mutsi kaɗan idan za'aje wuri zakaji yace tazo ta shiga motan shi, duk yadda naso na jawota amma fir ya hana, haka dole na haƙura na barsu tare, shi kuma Faisal gaba ɗaya hankalin shi nakan Jedderh autar uncle Baba da yanzu take Ss3, duk wani feleƙe irin nata baya bashi haushi sai bibiyanta kawai yakeyi, ita kuma duk da kyau irin nata amma ganin ɗan balarabe sai wani falli ta keyi, nidai babu ruwana da kowa ta Baby na kawai nakeyi.

Daga Narabi tilde muka wuce family house ɗin su Daddy, inda anan muka haɗu da su Yayah Ahmad shida Yayah Aliyu, ganin su yasa Daddy ya tara musu ƴan'uwan shi akayita musu faɗa domin su daina bin halin uwarsu suyi zumunci da ƴar'uwar su ƙwaya ɗaya, haka suka nemi gafaran Daddy dani gaba ɗaya.

Duk yadda Daddy yaso zama dani Ummi taƙi mishi, domin shirin auren mu da Dr akeyi cikin satin nan, domin zamu koma school, kuma su Abba sun tabbatar mishi muna gama karatun mu ya tattaro ya dawo gida ya zauna, inda Umma tace idan bai dawo ba kuwa ita zata zo ta ɗauke ni mu dawo, haka yayita murmushi bai ce musu komai ba.

Shiri na musamman Ummi na ta ke mun, don watarana inaji Aunty hauwa tana mitan wai Ummi me take so tayiwa É—anta ne kam? Mallake mata É—a ne za'ayi irin wannan shiryani da ake tayi"?

Dariya Ummi tayi tace, "ɗan nakine dole sai mun kammale kanshi wuri ɗaya, din kada mu mishi laifi ya tattara kayan shi mu rasa kuma wa zai sake dawo mana da shi gida", da sauri na buɗe bakina bayan na ajiye goran tsumin Hajiya Aisha Aliyu Garkuwa mai haɗin gaske da nake sha nace, "Ummi ae duk inda Baby ya gudu zan bishi na tarkato abuna, ina zan bari wasu masu jan kunne su ƙwace mun shi? Kinsan faman danayi da shi akan wata ƴar india mai jan kunne kuwa? Sai da na zama ƴar bariki tukun na kwace abuna, na barta da sakakken baki, ga wasu masu halittan kajin mayu a hotel da in sun ganshi suke lanƙwasa kaman macizai, da kyat na fige mishi zuwa cin abinci inda suke na dage da bashi abinci, hmmm ta ina zanyi saken wannan haɗaɗɗen babyna ɗin ya kuɓuce wani wurin kuma"? Ina rufe bakina Aunty hauwa ta kaimun dundu a bayana, baki a buɗe tace.

"anya humaira kinsan ku.ya kuwa? Mufa iyayen shine kika zaƙalƙalewa a gaban mu irin haka? Tou na sake ji kince babyn nan a gabana kiga yadda zan fasa miki baki, ɗan nawa da girman shi zaki na gaya mishi baby sai kace wani Affan".

Muryar Baby naji shi da Aunty Fatima da Uncle Hasan suna dariya bayan sun shigo ɗakin Baby ya dawo kusa dani ya zauna yana duban Aunty hauwa yace, "haba Aunty nawa ma nake da baza ace mun baby ba? Gaskiya ni Aunty hauwa babu ruwanki, kawai kibarni a ce mun baby kafin na tsufah, yanzu Hassan ya isa a ƙira shi da baby ne bayan ya zama wani dattijo, har zai aurar da ƴa, nikan kubar mun sweet baby na ta faɗi abinda ta keso, ku toshe kunnen ku".

Nidai zunɓura baki nayi ina kallon Aunty hauwa da wutsiyar ido, azuciyata ina Allah-Allah Ummi tace ta tashi ta tafi ta barmu, Amaal kuma sai dariya ta ke tayi ita da Ummi, uncle Hassan ne yace.

"Aunty hauwa nima fah ana ce mun babyn nan fa idan babu idon ko" ya faɗa yana duban Aunty fati data buɗe baki tana kallon shi, dariya yayi yace, "ƙarya nayi ne baby luv"?

Gaba ɗaya ɗakin dariya aka fara har da Auntyn hauwa, don Aunty Fatima tuɓurewa tayi tana ta rantsuwa tana duban Ummi tana cewa, "wallahi Ummi faɗi yakeyi, bana wani ce mishi Baby, nikan kuce ya bari Hummy fah ƴata ce yayah yake faɗa a gabanta".

Dariyanta akayi tayi don gaba ɗaya Aunty Fati bata daina shagwaɓa har yanzu.

Ranan friday aka ɗaura auren mu da Dr nah agarin Tilde, inda Baban mu dama ya yi ginin shi mai kyaun gaske a gefen gidan su, zuwa yamma a ka ɗaukoni zuwa garin bauchi, ranan Daddy na ba ƙaramin kuka yayi ba, wanda dayawa sai da suka taya shi kukan, ni kuma nayi kuka domin a ranan na ƙara tausayawa Daddy na rashin mummy na da yayi.
Chapter 65 · 0% Book details