← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 66

Sashe 39

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka muka fara tsalle da murna, domin gaskiya Aunty Hauwa ba dai nuna mana so ba duk masifanta amma akwai ta da alheri, gashi ko cin abu zatayi taga idon mutum toh babu yadda zatayi sai ta baka, ita dai abunta bai rufe mata ido ba, kaman ƴan garin su mamanta idan sunzo, duk da tasan irin muguntar da sukayi wa mamanta amma haka zata tattaro kayanta ta basu tace suje su raba, gaskiya halinta babu abinda ta bar na Goggo Hussaina, kaman tasha ne a nononta, saidai faɗa kam sai a hankali, wasu sukance ta ɗauko wani yayan Baban sune amma ya daɗe da rasuwa, domin wuni yakeyi akan kujeran katako a ƙofar gidan shi, duk wanda ya wuce sai yayi masifa, shi ne ƙiran mai gyaɗa, shi ne mai gujjiya, mai rogo bata tsira ba, kuma yana saya yana masifa, toh haka Aunty Haiwa ta ke, domin gidan su family house ne, duk yaron da ya shigo sai ta hantare shi, amma kuma kullum jakanta da sweet tana raba musu, Allah sarki Aunty Hauwa nah", Dr Hussain ya ƙarasa faɗa yana sha re hawayen shi, kuma lokaci ɗaya ya sunkuyar da idon shi a ƙasa yana ta share hawaye, gaba ɗaya parlourn kowa sai jikin shi yayi sanyi, babu wanda yace uffan, sai Faisal ne ya tashi ya ɗauko goran ruwan sanyi ya miƙa mishi, karɓa yayi ya sha kusan rabin roban, sannan ya ɗago idon shi ya dube ni, ganin ina share hawaye na sai yayi murmushi ya maida idon shi ƙasa.

"Ummin mu da fara'a ɗauke a fuskarta ta miƙa hannu ta rungume ƴar uwarta, itama Aunty Hauwan tana murmushi ta rungume Ummi, bakinta bai rufu ba tace, "Adda Fati kiji mijinki wai kinfini kyau? Nidai da mutanen gida duk mun san muna kama da ke amma maganan gaskiya nafi kyau, ni banma taɓa jin wanda ya taɓa cewa kinfini kyau ba, haba dubi ido na kaman ni na ɗusana abuna, kowa ya ganni sai ya sume da kyaun idona", ta ƙarisa faɗi tana murguɗa baki tana juya idon nata.

Dariya gaba É—aya parlourn sukayi, Abba yana hararanta da wasa yace, "amma Hauwa bakida wayo, waya ce miki kinfi Fatima kyaun ido? Ke baki san ana zolayanki bane ake cewa kuna kama? ae kinfi kama da Auwal da musa, domin Fatima ae ta muku zarrah a kyau, don ke macece shiyasa ake kwatanta kamanin ku, kuma kunfi su Auwal fari".

Kuka Aunty Hauwa ta fara tana duban Ummin mu tace, "don Allah Adda Fati ki gaya mishi gaskiya saboda Allah, wallahi yayah Auwal da Yayah Baba ƙananan ido suke da shi, sufa irin idon su Bappanmu suke da shi ƴan ƙanana, kuma hancinsu bai kai namu ta shi ba, Adda kimishi bayani ya lura, wallahi ni ina da kyau mai ɗaukan hankali, ranan fa zan wuce wani DPO yazo wucewa kasa tafiya yayi yace sai yaga gidan su wanann mai kyaun, wallahi yanzu a school Hauwa beauty ake cemun, ko Hauwa golden girl", ta ƙara sa maganan tana share hawayenta, wato Aunty Hauwa komai zakayi kada kace bara da kyau domin ita ta yadda ita mai kyau ce, saboda haka kullum Ummin mu idan zata saka ta aiki ta mata babu ɓacin rai, zakaji tace zizar gidan mu, autar Adda da yayah da bappanmu, maza tashi kimun aiki, toh babu musu zata tashi tayi yadda ya dace, shiyasa Aishan mu ta gaji halin Aunty Hauwa, gashi kuma kullum ɗabi'un da Humairah ta keyi kenan, wanda shi yaja hankalina gareta, don ni tun ina yaro abinda Aunty hauwa ta keyi burgeni yakeyi, ban fahimtan komai amma idan tana rikicin tafi kowa kyau, abin daɗi yake mun.

Domin wataran sai ta jamu cikin ɗaki nida Hassan ta tsaya gaban mirrow tayita kallon kanta, ta juya ta gyara tsayunta, ta lanƙwashe nan ra juya na, ta baza gashinta mai azaban kyau tana duban mu zata ce, "yarana amma dai duk ƙasan nan kafin a samu mai kyauna za a sha wahala ko? Kunga irin kyaun ido na kuwa"? Hassan idan ya kalleta zaice amma baki kai Ummin mu ba fah, toh hannu ta ke sawa ta kai mishi ran ƙwashi ta fatattake shi a ɗakin tana cewa, wannan kam kuskure akayi aka saka maka sunan mahaifinmu, ɗan banzan yaro mai goshin tsiya dama isubu aka saka maka, sunan wani ɗan ajinmu a lungun fada, ko kuma a saka maka gedau ko kantara, shashan yaro kawai," sannan ta dawo da kallonta kaina, "kaifa me kace"? Murmushi nakeyi ina da shekara huɗu amman nasan wayon ince mata, "kinfi Abba da Ummi kyau, kinyi irin india", tsalle ta keyi ta ɗaga ni sama tace wani abunma sai naje turai na ɓaro kyau tukun yaro na mai kama da larabawa, nima daɗin abinda ta ke faɗi nakeji.

"Dr na toh ina ita Auntyn Hauwan yanxu ta ke? Nima naji ina sonta, don nima ina son ace ina da kyau, duk da nasan ina da kyau amma ina son ace nafi kowa wallahi", na faÉ—a ina duban dr da yake kallona idon shi na zubar da hawaye bakinshi kuma da guntun murmushi.

"Toh ae ke baki mun kama da Æ´an india, asali ma ni banga kyaunki ba, kaman Aishan mu da Aunty Hauwa sunfi kyau", Dr ya faÉ—a yana fito da sautin murmushinshi, kuma hawaye yana kanbin fuskan shi, gaba É—aya parlourn dariya aka fara mun, yadda na turo bakina gaba kaman zan falla ihu.

Amaal mai ta samu banda dariya, tana duban Dr tace, "ga goshin ta kaman na gedau da kantara", gaba ɗaya parlourn dariya akeyi, Dr yana dariya yace, "Amaaƙ sunan kakanunae fah na wurin uwa, ƙannen maman umman mu ne fah, in kinyi wasa sai na haɗa ki da gedau babu ruwa na".

Daddy ƙurawa Dr ido yayi duk yana cikin ruɗani, duk dariyan da akeyi shi bayayi, idan ya dubi Dr ɓa wani lokaci sai kuma ya dawo da idon shi kaina, nidai ina satan kallonshi kaman wani mai nazari, chan kuma sai naga yana share hawayen da bansan me yasa suka zubu mishi ba, gaba ɗaya hankalina sai ya tashi, kawai sai na fashe da kuka na riƙe shi ina tambayan shi, "Daddy me yafaru kake kuka"? Murmushi yayi ya riƙo hannuna muryah a hankali yace "babu komai na tuna da mahaifiyar kice", ya faɗa yana sha re hawayen shi.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/13, 11:38] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 33📑*

*__________📖* Ana haka magana ya fara ƙarfi tsakanin Aunty Hauwa da Baba Umar, domin wani so sukeyiwa junan su kaman me, amma Ummi nah ita bata so hakan ba, domin tanaga kaman Suwaiba zata ce ita ta haɗa ƙanwarta da mijinta, amma koda Abba yace mata babu ruwanta, kada ta damu da maganan mutane sai kawai ta yi shiru ta bisu da addu'a.

Ranan da Aunty Hauwa ta gama huta, Baba Umar ya matsawa Abba akan shifa dole su tafi tare da ita, domin aje anema mishi aurenta, don bada wasa yakeyi ba, kada yana chan lagos wani yazo ya ƙwache mishi ita, babu yadda Abba ya iya dole suka biyota.

Tadawo da washe gari mutanen jos sukazo har misau neman aure, babu wani wasa da hankali akayi komai cikin mutunci da dattaku, a ranan iyayen Aunty Hauwa suka bawa Baba Umar auren ta, shi kuma Baban Narabi ya sake neman a saka musu auren bada daɗewa ba, da ƙyar dai aka yadda akan idan tagama wannan year ɗin sai ayi, domin da iyayenta sun fi son sai ta gama karatun haba ɗaya, amma haka aka tsayar da magana nan da 5month.

Ko wani ƙarshen wata sai Baba Umar yazo mata hira har bauchi, toh ganin irin rawan kan da yakeyi ne ya tunzura matar shi ta fara buri, wanda har gidan mu taje tayiwa Ummi kacha-kacha, Ummi ko kaɗan Ummi bata mayar mata magana marar daɗi ba, sai haƙuri kawai da take bata.

December Ummi suka tafi misau domin saura 1week bikin su Aunty Hauwa, daÉ—i nida Hassan mukeji, domin zamuje misau muci masan gidan sarkin dabji, sai murna mukeyi.

Ranan thursday Aunty Hauwa tayi walima a cikin fadan sarkin misau, a cikin wani hall mai suna *GWANI MUKHTAR* waliman yayi matuƙar armashi inda malamai mata kusan kala uku sukayi wa'azi, ranan friday 2:300pm aka ɗaura auren Aunty Hauwa da Baba Umar, kuma a ranan akayi wuni, ranan saturday aka wuce da ita kai tsaye chan Narabi, inda dama Baba Umar yayi gidan shi mai kyau, wanda idan sunzo suke sauƙa a wurin, gida ne mai 4bedroom, saboda haka sai aka bawa Aunty 2bedroom inda kowani ɗaki ɗaya yana kallon ɗaki ɗaya, da toilet a tsakiyan su, ɗaya aka maida mata parlour ɗaya kuma bedroom, ita ma Suwaiba haka aka mata, shi kuma Baba Umar aka bar mishi main parlour da toilet ɗin ciki don baƙi, amma ya yanke shawaran yanzu zaina bin ɗakunan su, amma idan ya samu sarari zai zo yayi ɗaki a cikin parlourn.

Baba Umar Allah bai taɓa basu haihuwa ba, domin sau biyu suwaiba tana ɓari, amma daga baya abun sai yayi shiru.

Ranan Baba Umar ya nuna murnan shi da yaga Aunty Hauwa a gidan shi, kuma matsayin matar shi, daɗin abinma suwaiba ba tazo bikin ba, saboda haka ya samu ya mori amarchin shi da Aunty har na tsawon 2weeks da aka bashi hutu, daga nan ya mata sallama ya wuce lagos, inda ita kuma sauran 3weeks suka ma ajin da shekaran zasu gama, wato sauran mata 1yr ta gama, kuma ya mata alƙawarin duk bayan 2weeks zai dinga zuwan mata, haka suka rabo suna ta begen junan su.
Chapter 39 · 0% Book details