← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 66

Sashe 12

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Meye ya ke damun ta?".
Dr Hussain ya tambaye ni.

"Sickler ce". na bashi amsa a taƙaice.

Zaro ido yayi yana kallo na a razane, can kuma sai yace, "shi ne kuma kika É—auke ta zuwa yawo bayan kinsan ciwon su baya son wahala?".

Zunɓuro baki na yi ina hararan shi ƙasa-ƙasa ina ɗan ƙunƙuni na.

Ya na kallo na yace, "zagi na ki ke yi Aisha?".

Ina kallon shi kaman zan yi kuka na ce,
"ni mene zai sa na zage ka? Kawai cewa na yi kaima ai yawo ka je kaida matar ka, kuma kaƙi kula ni da ka ga tana gun, bayan ka tafi ka daɗe baka dawo ba, ko zuwa duba ya ya na ke ba ka yi ba saboda kana wurin matar ka".

na faÉ—a kaman zan zubar da hawaye.

Kallo na ya tsaya yana yi kaman yaga sabon abu, amma abin mamaki ko bin ta magana bai yi ba kawai sai na ji yana tambaya na, "Meye gyenotype É—in ki?".

Turo baki na yi ina duban shi kaman zan zunduma ihun haushi, bansan lokacin dana harare shi ba, na kaÉ—a kaina nace,

"meye problem É—in ka da sanin gyenotype É—i na? Ina ce kasan na koÉ—aÉ—É—iyar matar ka".
Na faÉ—a ina tashi tsaye zan bar wurin.

"Ka da ki yadda ki bar nan wurin, kuma ki shirya yanzu zamu koma gida, don asibitin nan ba a kwana, yana fitowa muka ji ya ya ta ke, zamu ta fi gida".

ya faÉ—a idon shi tsaye a kaina, zuciyar shi kuma yana tuna wani lokaci kusan irin haka, lokacin yana service a central bank branch É—in su da ke bauchi, sun shigo gida da wasu corpers Æ´an'uwan shi, amma har da mata a cikin su, suna tafiya ya ce Aisha ta kawo mishi abinci, amma firr yarinyar nan ta dinga mishi tsiwa kaman ba ita ba,

"Yayan mu to me ya sa ba ka ce wa Æ´an matan ka su kawo maka ba? Ni sai kawai ka dinga zuwa da Æ´an matan ka suna yiwa mutane kallon banza kaman sun ga sa'o'in su, ni wallahi suka sake zuwa sakawa zanyi a É—aura maka aure da figaggiyar ciki, idan yaso ka samu mai kawo maka abinci".

Aisha ya tuna yadda ta mishi ranan, babu ko É—igon tsoron shi a idon ta, gashi yau ma Humaira ta sa ke maimaitawa.

Yana kallo na bai ce uffan ba, ni kuma sai harare-harare na ke yi, can jumawa yayi É—an murmushi yana duba na ya ce,

"Ko ta burge kine matar tawa?".
Ya faÉ—a yana jiran ya ji nata irin amsan ko zai zo É—aya da na Aisha a wancan lokacin.

Juyowa nayi da sauri na kalle shi fuska a É—aure nace,

"kai ka ke ganin kyawun ta tun da ka na son ta, ni dai nasan ko kusa ba za'a haÉ—a ta da ni ba wurin kyau, bari kuma kaga lokacin da nawa masoyin zai iso, za ka ji ya tabbatar maka da samun irin mai kyawuna sai an tona".

na faÉ—a ina girgiza jiki na ina fari da ido na.

Miƙewa yayi tsaye yana duba na da mamaki, domin lokacin da Aisha ta gama mishi wannan mitan duban ta yayi yace, " Sister Aisha ko dai Blessing ta burge kine? Halan kema kyawunta ya burge ki"?

Harara Aisha ta mun a wannan lokacin sannan ta dube ni tace, " kai kaga kyawunta don ka na sonta, amma ni ko ku sa dani a ka kawota wallahi zan dushasheta, kuma ka jira ranan da zan fara samari zaka ji an faÉ—a maka haka".

ta faÉ—a tana wucewa parlon Ummi a lokacin, ni kuma nayi murmushi na wuce side É—in mu da Hassan.

Duban fuska na ya tsaya yana yi, har Dr Abdallah suka fito daga É—akin, wasu nurses biyu mata suna gangaro Amal a gado tana bacci, hannun ta É—auke da ledan jini, zuwa in da suke na yi na tsaya ina kallon ta.

Suna shiga wani É—aki mu ka bi bayan su har da Dr Hussain, bayan an kwantar da ita ne nurses É—in É—aya ta fita É—aya kuma ta nemi wuri ta zauna, Dr Abdallah yana duba na da murmushi É—auke a fuskar shi yace,

"Ƴan mata Alhamdulillahi mun samu jinin da ya yi dai-dai da nata, kinga har ta samu ta yi bacci, yanzu za ki iya komawa gida sai wurin 8:00am za ki iya zuwa ki duba ta".
ya faɗa ya na ƙura mun idon shi.

Kallon shi na yi a marairaice nace, "Plz Dr kabar ni na kwana ina ganin ta mana, kaga asuba ma ya kusa".
Na faɗa ido na yana cikowa da ƙwalla.

Hannun Dr Hissain na ji ya kamo nawa a hankali na ji yana cewa,

"kibar su suyi aikin su mana Aisha, Kizo mu koma da safe zan dawo da ke insha'Allahu".

na buÉ—e ba ki zan yi mishi musu, sai na ga ya lumshe ido ya buÉ—e yana juya mun kanshi alaman baya son musu.

Bance komai ba na bishi yadda yake jana muka fita a É—akin, ni kuma ina ta waiwayen Amal da ke bacci kaman zanyi kuka, amma haka Dr Hussain ya jani mika fita, shi kuma Dr Abdallah sai bin mu yake da murmushi.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 10📑*

*__________📖* "Kinsan duk wanda ya gan mu zai yi tunanin mu miji da mata ne, so idan nace mata ba haka bane ba zata yadda ba, zata tsaya ta yi ta damun mu da tambaya, kuma ma na lura so na ta keyi, tun ranan da na fara zuwa cin abinci nan wurin".

ya ƙara sa maganan yana kallo na.

Tsakin da ban shirya ba na yi, ina duban shi kaman zan fashe a wurin na ce,
"tun da ka lura tana son ka ba sai ka daina zuwa cin abinci wurin ba, in banda kai ma, kana da mata ya ya zaka dinga sayen abinci a waje? Kawai ka daina zuwa don Allah Dr'mu".

"Saidai idan zaki na dafa mun to sai na daina zuwa wurin, amma mata na ita bata iya girki ba, saya itama ta keyi kullum, ko kuma ni na dafa mana".
cewar Dr Hussain.

Baki na buÉ—e ina kallon shi cike da mamaki,
"amma dai wallahi ta yi kyawun banza, ace mace ba zata yi girki wa mijin ta ba kam ai da sauran ta kuwa, kyawunta bai amfane ta komai ba, kace ashe dole su kazan mayu su dinga tsintar ka a wurare da yawa a ƙasan nan".

"Hmmm wata rana naje wani wurin cin abinci ma haka su kayi ta bina, ɗayar bakiga kyawun ta ba, ina ga duk duniya ban taɓa ganin mai kyawun ta ba, gata ƴar duma-duma da ita, ranan kwana nayi banyi bacci ba, ina rufe ido na sai na ganta a ido na".
ya faÉ—a yana jinjina irin kyawun da ya gani.

Kallon shi na ke yi baki da ido na a buÉ—e, "amma dai kam aljana ce ba mutum ba, don duk wacce ta fini kyau kam ai ta zama aljana, wallahi kadai na yawon sayen abinci, gara ma na dinga da fa maka kada wata rana Æ´an gidan ku su samu labarin ka shiga jeji".
na faÉ—a ina jin zuciya ta kaman zai fito waje.

ÆŠaga kafaÉ—an shi yayi alaman duk yadda na gani haka za'ayi.

"Hmmm".
kawai nace domin raina yayi matuƙar ɓaci da jin yadda ake son shi.

"Kinyi shiru baki ce komai ba".
ya jefo mun tambaya yana tsaya a gate É—in gidan mu domin jiran a buÉ—e mishi.

"To ni Humaira me zance? Kawai sakarar matar ka ta kasa kula da kai, common girki ba zata zauna ta maka ba, har sai kajin mayu sun haɗu sun lashe ka tukun tazo tana kukan wai ita ma tana son ka ko? Da ƙafanɓta a sandare kaman taɓarya, ni shiyasa ban cika son naga mace mai kyau da yawa ba, don wahalar da miji su keyi irin su, ballanta na kai da baka ganin kyawun kowa sai nata, to ko me zance? Sai dai na yi ta addu'an Allah ya kare ka daga sharrin su, ni daba ka ganin kyawuna ni yazama mun dole na Kula da kai ai".
Na faɗa raina a ɓace.

Haka muka yi parking na fita a motan ina duban shi nace, "to what time zamu koma asibiti wurin Amal? Kasan yau su Abbun ta zasu iso da dare".

"Ki bari sai 6:00pm sai muje, idan yaso 9:00pm sai mu dawo"

KaÉ—a kaina nayi alaman ya mun, sannan na wuce na yi side É—ina, ina shiga kwanciya nayi a parlor ina ta tunanin labarin da Dr ya bani wai yaga kyawun wata, ikon Allah ko me yasa ni baya ganin kyau na? Hmmm shi ya sani na faÉ—a a zuciya ta.

Muna shiga hospital É—in muka ci karo da Dr Abdallah ya fito shi da wasu nurses guda biyu daga É—akin, amma sakarai har ya manta abinda ya faru jiya, yana ganin mu ya fara mana murmushi kaman yaga wasu Æ´an'uwan shi.

Da sauri Dr Hussain na ji ya saka hannun shi ya riƙo nawa hannun, fuskar shin nan kaman bai taɓa dariya ba, yadda kuka san ya shigo class yana lectures haka ya yi da fuskan, koma nace yama fi hakan.
Chapter 12 · 0% Book details