Sashe 40
Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rayuwar babu wuya, yau Aunty hauwa sun dawo hutun first term, kai tsaye misau ta wuce, domin zata jira sai Baba Umar yazo tukun su wuche lagos, domin yace wannan hutun lagos zata je tayi, domin hutun 3 weeks zatayi, shi kuma yaga ya kamata su fara sabawa da suwaiba.
Tana shiga gidansu tayi karo da Baba wato yayanta Musa, yana ganinta ya fara dariya yana cewa, " jama'an gidan nan ku fito kuga wata afiruwa kazar mayu", yana dariya lokacin da Goggo hussaina ta fara fitowa yana dubanta yace, "Mama don Allah kiga ƴar ki duk ta wani fige babu daɗin kallo, sai wasu ido girkima girkima kaman na hajiya umma ƴar madara", ya ƙarisa faɗi yana dariya domin yasan ya tsukano Mama, wato goggo hussaina, harara ta bishi da shi tana kaɗa kanta tace, "kayi damu iyayenka ba namu iyayen ba, ɗan tselanƙwa mai ƙananun ido kaman ƙaramar tocilan", ta faɗa tana kamu hannun Aunty hauwa da ta fara zuban hawayen tsokanan da Baba yake mata, domin babu hali su zauna inuwa ɗaya da shi zakaji ya tiso ta gaba har sai tayi kuka, amma yayah Auwal ɗinta tattalinta yakeyi kaman wata ƙwai, Mama tana hararanshi tace, "zakaje gidan umman neman ɗumamen safe da kunu ae, namaka alƙawarin yau zan tura ɗan saƙo ya gaya mata irin tonon sililin da kake mata", ta jawo hannun Aunty hauwa suka shige ɗaki, ita dai Addagana tana zaune a ɗakinta tana biya karatun ta, bata wani fito ba sai dariyan drammer su kawai ta keyi daga inda ta ke, amma har cikin zuciyarta tana jin wani iri da akace hauwa ta fige, toh komai ke damun ta? Allah kaɗai ya sani.
Tunda Mama ta lura laulayin ciki Aunty hauwa ta keyi, domin suna shiga É—akin ta dawo da bayan kaman zatayi amai tace, "Mama kaman anci miyar stew a É—akin nan, warin shi na ke ji", mama da sauri ta É—auki kwanon miyan ta fitar zuwa kitchen, sannan tazo ta É—aga labulayen É—akin tana duban Hauwa data faÉ—a kan gado ta kwanta rub da ciki, cikin kallon tausayawa tace, "buÉ—É—o nah mai kike so toh a dafa miki?" juyar da kai kawai Aunty haiwa tayi alaman ba tason komai.
Mama tana duban ta tace, "haka bazai yiwu ba hauwa, kinga yadda kika fita hayyacin ki kuwa? Kodai bakyacin komai ne a makarantan? Kuma kin takura kanki da karatu ko? Don Allah gaya mun me kike so kafin wannan mai neman maganan yayi gaba na rasa É—an aika".
Juyowa Aunty hauwa tayi tana duban mama fuska a murtuƙe tace, "Mama komai naci amai nakeyi, ni bansan me zanci ba, kawai fanta nake iya sha", ta ƙarasa faɗi hawaye yana bin idonta.
Mama na duban ta kaman ta tayata zub da hawayen tace, "toh zakici faten tsaki"? Da sauri Aunty hauwa ta tashi ta zauna tana duban mama tace, "yauwa mama amma na gidan umma nake so, wanda ta ke saka mishi gauta", ta faɗa tana tasowa tayi parlour wurin fridge ta buɗe tana kallon ƙullin zuɓun da mama takeyi na sayarwa, har ƙasa ta zauna tukun ta ɗauki leda ɗaya mai sanyi ta ɓula ta zuƙe shi, mama kuma tayi waje tana ƙwala ƙira wa Baba ƙarami, sannan ta dawo ta neme kujera ta zauna ta ƙurawa Aunty hauwa ido da ta ɗauki leda na biyu ta ɓula tana wani lumshe ido tana sha.
Baba ƙarami ya ɗaga labulen ɗakin bayan yayi sallama mama ta amsa, idon shi ya sauƙa akan Aunty hauwa da take shirin ɗaukan leda na uku tasha, da karfi yace, "kutt hauwa inace dai kin bada kuɗin tukun kike sha bawai kinga na bati ba ko"? Ya faɗa yana ƙara sowa cikin ɗakin baki a buɗe yana kallon mama akan tayi magana.
Bappah ne ya shigo gidan da sallama, yana dariyan halin Baba ƙarami ya ƙaraso ƙofan mama yana cewa, "kaidai baba ina ruwanka da tambaya, kasan ko duk zuɓun fridge ɗin ma ita aka yi"? "caɓɗi jam, amma ko nima dole nasha ɗaya don ita har uku fa take sha Bappah", Baba ƙarami ya faɗa yana kallon idon mama da take binshi da harara.
Yana dariya ya karkata kanshi wurin mama yace, "mama gani ina zanje miki"?
"kaje gidan umma kace ina son faten tsaki mai gauta wa Hauwa, yanzu ta dawo daga makaranta ta kasa cin abincin mu, gwaten kawai ta ke son cin kaji".
Juyowa hauwa tayi ta gaida Bappah daya nemi wuri gefen mama ya zauna yana dubanta da tausayawa yace, "bakiji daɗin jikin bane baɗɗo nah? Duk kin rame kin wani ɗashe gaba ɗaya kaman bakida jini? Me kike son ci nasaya miki"? Bappah ya ƙarasa faɗi shima yana duban ta da tausayawa.
"Bappah ferfesun kayan ciki nake so", ta faɗa tana kwanciya akan ledan tsakar parlourn Maman, "kutt amma hauwa kin tunkuɗu rikici wallahi, ke kaɗanki kin shanye zuɓu leda uku, gashi yanzu kinsa za a haɗa tsuhuwa da aikin yin gwate, a haka ma mai gauta wanda da ƙyar idan umma bata sake cillani kasuwa ba, yanzu kuma kin matsawa bappan mu ya sayo mana kayan ciki a dafa mana, haba hauwa cikin mu ae baxai ɗauki abinci dayawa ba", ya faɗa yana fita da sauri a ɗakin yana dariya, domin irin kallon da mama ta ke mishi kaman zata mare shi, yana tsayawa a tsakar gidan ya kwaɗawa Addagana ƙira yace, "fito kiga halin wariyar da mama da Bappah suke mun, don Allah Addagana nima ki saya mun kazar alka mana na huce", fitowa tayi tana kallon shi tace, "nikan ba aikanka akayi bane Baba"? Addagana ta tambayeshi.
Haka ya fita yana cewa daga nan zan leƙa gidan yayah Auwal nace mishi zizar ƴaƴa fa tazo, gida ya kache me da girke girke, shima ya saka ƴar lukutan matar shin nan ta dafa nata ta kawo", yana dariya ya fita a gidan.
Da yake anyi auren hauwa december, febuary akayi na yayah auwal, da matar shi da takasance Æ´ar bappan su ce, Ummi kyakkyawar bafulatana da suke yanayin kama da Yayah Auwal.
*©AUNTY NICE CE*âœðŸ»âœðŸ»âœðŸ»
[8/14, 11:45] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
   *1441H/2020M.*
 Â
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATIONâœ*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
    ```ðŸŽG•W•AðŸŽ```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*ðŸ‡ðŸ¼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICEâœðŸ¼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 34📑*
*__________📖* Murmushi Bappah yayi yana duban mama yace, "kinji abinda ɗanki yake faɗa ko"? Tana dariya ta dubi Aunty Hauwa tace, "kije ki gaida Adda ko", tashi Aunty hauwa tayi ta nufi ƙofar ɗakin Adda, wanda ta shimfiɗa taburma tana ƙulla ayanta mai sugar.
Gefen tabarmar Aunty hauwa ta zauna, idon ta na kan ayan, ta gaishe da Adda, bayan sun gaisa ne Aunty hauwa ta saka hannu ta ɗebi ayan ta kai bakin ta, lokaci ɗaya ta rufe idon ta don tsabar daɗin da ya ziyarci ƙwaƙwalwarta, ganin haka Adda ta ɗago wani ledan ta ƙullu mata mai yawan gaske ta miƙa mata, gyara zamanta tayi a gefen Adda ta maida hankalinta kan cin ayan.
Adda tana gama ƙullawa ta dubeta tace "ko zakici rogo"? Ido Aunty hauwa ta ɗago tana kallon Addan cikin nutsuwa tace, "dama ki soya mun shi ya koma ƙosan rogo".
Tashi Adda tayi ta ɗauko rogon ta saka attaru da ajino da albasa ta kirɓaci yayi laushi, sannan ta haɗa murhunta ta ɗaura mangyaɗa, ta fara soya mata, lokacin kuma Mama ta fito tsakar gidan domin Bappah ya koma ƙofar gida domin fara ƙiran sallan azahar da akeyi.
Dukkan su alwala sukayi, bayan sun idar da sallah ne Adda ta zuba mata ƙosan rogon a pilet, tace ta karɓo yaji a wurin Mama, da sauri ta tafi parlourn mama ta karɓo yajin, a tare suka fito ita da maman, kafin kace me ta cinye rogon nan, mama ta miƙo mata zuɓu guda 2, a wurin ta zuƙe su, sannan ta yi hamdala ta wuce ɗakin mama ta kwanta akan three sitter maman, lokaci ɗaya bacci ya ɗauke ta.
Ana ƙiran sallan la'asar ta buɗe idonta da ƙaran wayanta ya tasheta, amma bata iya ta tashi ba ta jawo wayan ta kai kunnen ta, muryan Baba Umar taji yana mata sallama, hira sukayi na zuwa wani lokacin yana kuma tambayanta yanayin jikintan, haka dai suka ɗan ɓata lokaci kaɗan, sannan ta tashi ta fito domin yin alwala.
Tana idar da sallan mama ta shigo ido ta ƙura mata ganin ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jan charbi, a hankali ta ɗago suka haɗa ido da mama.
"Hauwa ga gwaten tsakin an kawo miki, amma ina ga bayanzu zakici bako?" murmushi Aunty hauwa tayi tace, "yanzu kai mama, kinji wani irin yunwa dana ta shi inaji kuwa"?
Mama ko da sauri ta jawo kulan ta ɗauko pilet ta miƙa mata, wani murmushin daɗi Aunty hauwa tayi, ta ɗauko ta zuba cikin pilet ɗin, sai wani ƙamshin gyaɗa yakeyi, ga tantaƙwashi rututu a ciki, Aunty hauwa dariya tayi tace, "Allah sarki hajiya umma, irin wannan daɗin yau ina zan kaishi"? Sannan ta dubi mama tace, "mama kada abawa kowa duk zan cinye zuwa anjima, don nasan Baba ƙarami yana zuwa ya gani toh sai wani ikon Allahn, don sai yaci", ta faɗa tana ɓoye coolern a bayanta.
Dariya mama tayi tace, "muma umma ta mana coolern mu daban, kuma Baba kam ae shi ya kawo, babu yadda banyi da shi bama ya tsaya yaci, amma yaƙi yace pepesoup ɗin kayan cikin kawai yake jira, amma wannan kam ya bar miki".
"Chabb É—i jam, mama kada ma kibashi, ni nafi son saifa da hanji ma kawai, idan akwai yaÉ—i a ciki ki bashi mama", ta faÉ—a tana kai loman gwaten, kallon mama tayi tana murmushi tace gaskiya umma badai iya kwamacalan girki ba kam, zwaii kenan", ta faÉ—a tana maida dariyanta.
Hararanta mama tayi, "da yake ta rufa miki asiri ta farfaÉ—o da ke ae dole ki faÉ—i haka, amma akwai gobe zan ce kada ta dafa miki komai ta barki da halinki", dariya dukkan su sukayi.