Sashe 11
Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jingina kanta ta yi a jikin gado tana ɗan shirin komawa bacci, gefen ta na zauna nayi ta lallaɓa ta a kan taci abinci, da ƙyar ta yarda, haka naje na zuba mata abincin a plet na kawo mata har ɗakin, ɗayan hannun kuma ina ɗauke da ƙaramin jug dana zuba taceccen ruwan apple ɗin a ciki.
Duk yadda ta so taƙi cin abincin ban barta ba, sai dana takura ta ta cinye abincin, sannan na miƙo mata magungunan ta tasha, tana gamawa Abbun ta ya kira wayan ta, ni na ɗauki wayan muka gaisa, tambaya na jikin ta ya yi cikin damuwa da nuna kulawan su a kanta da ciwon ta.
"Humaira kina ga zaku iya kwana a gida ko kuma Dr'n ta yazo ya tafi da ita hospital"?.
"Abbu babu komai, zamu iya kwana, yanzu ma ta samu ta yi bacci, bayan ta tashi ne tayi sallah kuma taci abinci, yanzu ma tasha drugs ɗin ta, ina ga babu komai insha'Allahu, don naga kaman ya fara mata sauƙi".
Bayan mun gama wayan ne na wuce parlor domin naci abincin, da ya ke ban yi mai yawa ba, duka na juye a plet É—in sannan na zauna na fara ci, amma gaba É—aya zuciya na ya kaso kashi biyu, É—aya ina tunanin ya ya zamu yi ni da Amal idan ciwon ya tashi cikin dare? ÆŠayan zuciyan kuma ina tunanin Dr Hussain da Dr Khadija dana gan su tare, ko yanzun ma tare suke ita da shi ko kuma ya ya abin yake? Haka dai nayi ta hira da zuciya ta har na gama cin abincin.
Books É—ina na baje su a parlon ina karatu, bayan na duba Amal na ga tayi bacci.
Bani na tashi ba sai around 11:00 pm, ina shiga É—akin na duba ta naga still baccin ta ta keyi, a hankali kada na tashe ta na wuce toilet domin nayi wanka.
Ina fitowa a toilet na É—auki turare na mai sanyin daÉ—i na shafe jiki na da shi, sannan na É—auko wando da riga masu É—an kauri kaÉ—an na saka, domin gaba É—aya yau naji garin kaman da É—an sanyi, hula na saka na É—ale gadon, bayan nayi addu'a na shafa na kashe mana wutan na kwanta.
Kaman a cikin mafarki na ke jin nishin mutum a kusa dani, a firgice na tashi zaune na kunna wutan ɗakin na juya inda Amal ta ke, abin tsoro ita ɗin ce kuwa zaune ta riƙe cikin ta ta na ta nishi, da sauri na matso kusa da ita na rungume ta, ido na cike da hawaye ina tambayan ta,
"Sister ina yake miki ciwo? Ko na kira Dr ne"?.
Ta riƙe ni da ƙarfi duk idon ta sun yi fari ƙal na alaman babu jini, tana nishi hannunta riƙe da cikin ta ta ɗaga mun kanta alaman na ƙira shi.
Da sauri na jawo wayan ta da yake kan bedside na buɗe, inda naga 2 misscall ɗin Abbun ta, amma ban bi takan shi ba na danna ƙiran Dr Abdallah, bai fi ringin biyu ba ya ɗauka bakin shi ɗauke da sallama, jiki na yana rawa na ce.
"Hello Dr Amal ce.." na faɗa kaman wanda aka ƙwaci sunan a baki na, a cikin nutsuwa yace mun, "in da ku ke a kwai abin hawa ne? Ko kuma nazo na ɗauke ta za ki bani address"?
Ta shi na yi tsaye na ce, "ka zo don Allah".
sannan na ba shi address ɗi na, da sauri na shiga toilet ɗin nayi fitsari kuma nayi brush, ina fitowa na buɗe sif ɗina na ɗauko wani after dress na ɗaura akan kayan baccin sannan nayi rolling ɗan gyalen a kaina, jaka na na jawo na jefa carbi na da waya ta, na riƙo Amal muka ta shi tsaye ina kallon ta nace, "sister za ki shiga toilet"?
Ɗaga mun kai tayi alaman zata je, da sauri na kai ta, da ƙyar ta na kuka zuwa lokacin ta yi fitsari, tana ta shi ta yi alwala da ƙyar, na saka hannu na riƙo ta muka fito parlor.
Na lura kullum Amal a cikin alwala ta ke, yau ɗaya na ji ta burgeni wato duk zafin ciwon da ta ke ji bai hana ta yin alwalan da ta saba ba ko? Ya Allah nima ka bani ikon yin shi a rayuwa ta, muna zama bamu daɗe ba naji an buɗe gate ɗin mu, motan Dr ta shigo, kafin na yunƙura sai jin wayar ta ta fara ringing, ban tsaya ɗaukan wayan ba, na kama hannun ta muka yi hanyar fita waje.
Muna fitowa na tsaya rufe ƙofan sai ga Dr Abdallah da sauri ya fito a motan shi ya ƙara so in da mu ke, dai-dai lokacin na ga Dr Hussain ma ya buɗe ƙofan shi yana tsaye yana kallon mu.
Amal ta kasa ɗaga ƙafan ta ta yi tafiya sai kuka ta ke yi, ganin haka na yi sauri zan riƙe ta, amma sai Dr yace a'a ki riƙe bag ɗin ki bari na taimaka miki, kallon shi na yi kaɗan na juya kaina gefe a zuciya ta ina cewa _ashe ma Balarabe ne shima Dr._
Ban san lokacin dana juya na kalli Dr Hussain ba, wanda har lokacin yana tsaye yana kallon mu, jikin shi ɗauke da wasu kayan bacci masu masifar kyau green colour, alaman bazai ce mun uffan ba, sai nima na daure na bi bayan su Amal, a lokacin David da Peter suka fito, ganin mune zama fita naga sun ƙara so in da muke da sauri.
"Preety bata da lafiya ne?".
Peter da ke ƙarasowa kusa da ni ya tambaye ni, cikin damuwa na ke gaya mishi ita sickeler ce kuma ta samu crises tun jiya da yamma, yana bin mu da kallon tausayi, sai David ya jeho mun tambayan.
"Preety why baki kira mu mun taimaka muku zuwa hospital ba? Naga kin nemo wani da ga wani wuri bayan muna tare kin kuma san akwai abin hawa?".
Ya faÉ—a yana duban Dr Abdallah daya buÉ—e bayan motan ya kwantar da Amal.
Kafin nace komai, sai Dr Abdallah ya ɗa go kan shi da murmushi yana miƙawa David hannu kuma yana gaya mishi yayi haƙuri bawai mun nemo shi daga wani wuri ba ne, dama shi Dr'n Amal ne.
Bayan sun tambaye shi asibitin da zamu je ya gaya musu, ni kuma na buÉ—e gaban motan na shiga, ko tayar da motan ba'ayi ba kawai naji an buÉ—e in da na ke zaune, sai jin muryan shi ya na cewa.
"koma back seet in da ta ke ki zauna".
ban iya mishi musu ba jiki na yana rawa na fita na koma bayan, sannan shi kuma ina ganin shi ya shige ya zauna, idon shi a kan Dr Abdallah sannan ya ce mishi.
"Aisha Sister na ne".
Dr Abdallah bai ce komai ba sai smilling da ya yi ya ja motan da sauri muka tafi.
Tun da mu ka shiga motan babu abinda ka ke ji sai sautin kukan Amal, ga wani miƙewa da ta ke ta yi, muna isa Dr Abdallah ya fito da sauri ya buɗe motan, lokacin kuma wasu nurses sun turo ɗan gadon su na ɗaukan marasa lafiya suka ɗauke ta, cikin gudu-gudu muka bi su ni da Dr Hussain, emargency room Dr ya wuce da ita, bamu daɗe ba wasu Drs guda uku suka bi bayan shi ɗaya namiji biyu kuma mata.
A reception ɗin asibitin muka zauna ni da Dr Hussain, babu wanda ya kula wani a cikin mu, har tsawon wasu mintu na, sai ga Dr Abdallah ya fito hannun shi riƙe da waya, da ga dukkan alamu shi da Abbun Amal suke wayan, har in da muke zaune ya zo ya tsaya ya kuma cigaba da wayen shi haka zalika idon shi a sauke a kaina ya ƙura mun ido yana amsa wayan.
Suna gama wayan ya dube ni da murmushin dana lura kaman baya barin fuskan shi, murya a nutse da ya nuna yanayin maganan shi ke nan ya dube ni yace,
"ƙawar ki mun samu tayi bacci, pain ɗin ya ɗan mata sauƙi, amma kuma tana buƙatan ƙarin jini, shi ne muke magana da Abbun ta".
ya faÉ—a har lokacin fuskan shi É—auke da murmushi yana duba na.
"Da ka ke mata bayanin abinda zaka yi to ita mai ta sani a game da aikin ka? Ina ce kun gama magana da mahaifin yarinya? Ina ga kaman ba lallai bane sai kazo ka mata bayani kawai ka aiwatar da abinda ya ke aikin kane".
Dr Hussain ya faɗa fuskan shi a matuƙar ɗaure, wanda sai da naji kunyar abinda ya faɗa, amma abin mamaki Dr Abdallah juyawa yayi yana duban shi fuskan shi har lokacin ɗauke da murmushi.
Shi kuma Dr Hussain kawar da kai yayi gefe kaman bai lura da kallon shi Dr Abdallah ya ke yi ba, "Yayan mu kada ka samu damuwa da magana na, kasancewar ta re su ke ciwon ya tashi, kuma naga ita Æ´ar'uwarka irin damuwan da ta shiga shiya sa na mata baya ni don hankalin ta ya kwanta, don É—azu da muka yi waya na jita cikin yanayin damuwa".
ya faÉ—a ya na duba na kaman wanda ya ke son fahimtan wani abu a tattare dani.
Bai jira mai Dr Hussain zai ce ba ya juya ya koma in da ya fito, muna zaune shiru babu mai cewa uffan sai wucewar mutane kawai ta gaban mu kaman safiya da ce ta yi, daga dukkan alamu asibitin na manya mutane ne, kuma babban asibiti ne.
"Wa to ke har wani kiran wayan shi ki ke yi ko? To kiyi deleting number'n tun da dai an kawo ta asibitin".
Dr Hissain ya faÉ—a yana bina da harara.
Fuska na a tsuke na dube shi sannan nace, "ni fa babu number'n shi a waya na, dama ta wayan Amal Abbun ta yace na kira shi idan jikin ya ƙi.....".
Ban ƙarasa ba faɗar abunda ke baki na ba, na ji yayi tsaki ƙasa-ƙasa, sannan ya ɗan dube ni ya ɗa ga kafaɗa alaman babu abinda ya dame shi, ganin hakan da ya yi sai na ji raina ya ɓaci, tashi nayi zan bar wurin, kawai sai na ji yace,