← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 66

Sashe 32

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki shiryah da yammah na kaiki yawo kiga wurare, yanzu zanje naci abinci na kwanta na huta ko Æ´anmata na", ya faÉ—a yana fita a É—akin.

Buga ƙofan da ƙarfi ya saka ni ɗago idona da sauri, Amaal ce kaman a wani jehota ta faɗo ɗakin, sai harara ta ke sauƙe mun, tayi kaman zata yi magana kuma sai ta fasa ta juya ta fita ta bar mun ɗakin, ajiyan zuciya na sauƙe ina taɓe baki na ɗaga kafaɗa ta alaman ko a jikina, kallon wayata nakeyi cike da tsoro, ganin number Dr nah da yake yawo a saman screen ɗin, har ya yanke ban iya na ɗaga ba, a karo na biyu wani ƙiran ya sake shigowa, bansan lokacin da naji zufa a jikina ba, chan cikin zuciyata ina raya kodai Amaal ta gaya mishi wani abu ne? har zai yanke shima da ƙyar na ɗaga.

"Hello" na iya faɗi ba tare da wani kuzari a jikina ba, daga ɗaya ɓangaren naji shi yana cewa, "yes hello baby, yayah naji voice ɗinki kaman kina bacci na tashe ki"? Da sauri na gyara zama na da muryah na nace, "bansan na fara baccin ba yanzu fah na ɗan kwanta", na faɗa ina jin bugun ƙirjina yana ƙaruwa.

"toh ina Amaal ta tafi ta bar mun ke? Nifa idan bazata baki kulawa ba zan taho na É—auke abuna kawai muje Daddy ya mana aure, don nafi so ni da kaina na dinga baki kula baby, ki gaya mun bata baki kulawa ko"?

lokaci É—aya naji tausayin Dr nah cikin zuciyata, runtse idona nayi sannan nace "lahh Dr na muna tare da uta fa, sai da taga na rufe ido ne inaga ta bar É—akin, amma Amaal tana bani dukkkan kulan daya kamata har ma ina jin nauyi da kunyan yadda suke mun, ka kwantar da hankalinka babyn baby", na faÉ—a ina É—an fitar da muryana don hankalin shi ya kwanta.

Ajiyan zuciya ya sauƙe da ɗan ƙarfi, sannan yayi ƙasa da muryah yace, "baby komai na duniyan nan yayi mun zafi, ashe bansani ba mun shaƙu haka? Gaskiya baby na gajji da kaɗaici, next week insha Allahu zan zo na dubaki, idan yaso ko 1week sai nayi mu juya tare, don na gajji wallahi baby, ko ina baya mun daɗi", ya faɗa kaman zaimun kuka.

Dariya nayi a hankali nima cikin kewan shi nace, "baby toh ae da sauran hutun mu, kuma inajin daÉ—in wurin wallahi, kawai kaima kazo mu zauna har sai mun gama hutun tukun mu tafi gaba É—aya", na faÉ—a ina dariya.

Shima dariyan yayi, "haba baby bakijin kunya dukkanmu muje mu taru musu a gida? ae suma zasu kuremu, nidai zanzo nayi 1week, kuma a hotel zan sauƙa ba a gidan ba".

"Baby meyasa bazamu zauna wuri É—aya ba? Nikan da kai nake son zama baby", na faÉ—a ina masa kukan sakalci.

"idan kina son mu zauna wuri É—aya ae babu matsalah baby, kawai zanje na gayawa Daddy mun amince aure muke so, sai kawai a É—aura mana mu zauna a gida É—aya tunda kema yanzu kina son hakan", ya faÉ—a yana dariya.

Da sauri nace "nifa bance aure zamuyi yanzu ba baby, kawai nafi so mu zauna wuri ɗaya ne dakai", na faɗa ina zaro idona don ganin Faisal daya buɗe ƙofan ɗakin ya shigo.

Kai tsaye inda nake zaune ya taho fuskan shi a ɗaure, ni dai zuba mishi ido kawai nayi ina ganin ikon Allah, daga cikin wayan kuma inajin dariyan da Dr nah yake ɓaɓɓakawa, abin tsoro da mamaki kawai jin Faisal nayi ya hau kan gadon ya ɗaura kanshi akan lap ɗina, sannan ya ɗauki ɗayan hannu na ya ɗaura akan shi yana shafa kan nashi da hannuna, kuma ya wani runtse ido kaman maijin bacci, ga wani ɗan ubansun ƙamshin da yake tashi a jikin shi, wanda lokaci ɗaya naji yana sanyaya zuciyata daga bugawan da tafara daga farko.

"Baby tunda kina son mu zauna wuri ɗaya ae kawai aure ne ya kamace mu, domin gudun kada Baby yayiwa babyn shi ɓarna, azo ana cewa ba haka aka soba, kinga zance ya lalace *_ƘADDARA TA RIGA FATA_* kenan, wanda ba hakan za a so ba, so kawai muyi haƙuri na zauna a hotel ɗin ko baby nah".

kasa bashi amsa nayi saboda yadda Faisal ya saka hannun shi yana ta matsa mun cinyoyina kuma yana mun wani tafiyan tsutsa, runtse ido na nayi bansan lokacin da na sauƙe ajiyan zuciya mai ƙarfi ba, wanda saida Faisal ya buɗe idon shi ya ɗaura su akaina, shi kuma baby daga ɗayan gefen shima ajiyan zuciyan yayi, murya ƙasa-ƙasa yake cewa, "baby ko dai na zo ne kina da buƙatan ganin babyn ki kusa da ke"?

kasa bashi amsa nayi saboda maida hankali da nayi kan Faisal domin na ture hannun shi da yake mun yawo da shi akan cinyana, wanda yanzu yake shirin kaiwa kan gwiwa na, kuma lokaci É—aya naji numfashina yana shirin É—aukewa, bansan lokacin dana furta, "wayyo don Allah kabari inajin wani iri".

Faisal murmushi ya farayi batare da ya daina ba saima ƙoƙarin kai hannun shi kan gwiwa na yakeyi, daga ɗayan ɓangaren kuma cikin wani irin murya mai cike da shauƙi naji Dr yana cewa, "wayyo baby nima abinda nakeji kenan ki daure na samu Daddy ko auren muyi daga baya sai muyi bikin auren yadda kike so", ya faɗa yana sauƙe ajiyan zuciya mai ɗan ƙarfi.

Runtse ido na nayi da ƙarfin don abinda Faisal ya keyi yafara shiga jikina, amma da Allah ya taimakeni kawai sai naji muryan Amaal da ihu tana cewa, "meye haka bros"?

Da sauri ya tashi ya zauna ni kuma nayi saurin kashe wayan na ƙura mata ido bayan na miƙe tsaye.

_Kallona besty nah miss xerks tayi, cike da damuwa tace, "besty dama ma'anan sunan book É—in naki kenan yau nake gani a tare da Faisal da Hummy"? Ba tare dana ce mata komai ba na runtse ido na cikin damuwa na cije lips É—ina_

Don Allah ku yi subscribing channal namu da ke dandalin youtube, ku latsa wannan link ɗin. Kar ku manta ku taya mu yaɗawa ga ƴan'uwa da abokan arziƙi.
Mun gode.

https://www.youtube.com/channel/UCeThSFXe9yNlA2iJA_IAqqA

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻

[7/23, 11:52] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 26📑*

*__________📖* "Amaal me kike nufi da wannan irin ihun da kikayi? sai kace wani mummunan abu kika samu munayi"? Faisal ya faɗa kaman mai shirin kai mata duka, hankali a tashe Amaal ta dube shi tace, "abu mara kyau kake aikatawa mana bros, saboda Allah Hummy fah amanace a wurin mu, amma duk kabi kana son chanja mata rayuwa, haba bros ka daina abinda kakeyi mana, ba halinka bane fah", ta faɗa idon ta ya ciko da ƙwallah.

Jan ƙafana nayi a hankali na ƙara gabanta, duk hankalina a tashe domin tunda na kashe waya Dr yake ta ƙirana amma tsoro ya hanani ɗauka, hannu na saka na riƙo na Amaal murya a hankali nace.

"Amaal ba laifin shi bane, laifi nane dana bashi yake zuwa inda nake, kuma bana son na ɓata mishi raine saboda danganta kar ku da shi, amma ki sani bazan taɓa juyawa Dr baya ba, ae soyayyan Dr bata da abokin haɗi a wurina, don Allah kiyi haƙuri kuma bana son maganan nan yaje wurin su Ummi, ya tsaya a tsakanin mu insha Allahu zamu magance komai haka bazai sake faruwa ba",na faɗa nima hawaye yana zuba mun don ganin yadda hankalin Amaal ya tashi.

"Hummy na yadda akwai laifinki, amma gaba ɗaya laifin nawa ne dana taho da ke ƙasan mu, yanzu idan wani abu ya faru ne zamu ce da Daddyn ki saboda Allah? don Allah Hummy ki kiyaye bana son wani abu ya faru da rayuwar ki ko kaɗan".

Rungumeta nayi inajin wani irin rashin jin daÉ—i a zuciyata, domin ko babu komai nasan Amaal ta damu da rayuwata, kuma bata son wani mummunan abu ya faru da ni.

Mtsss.... Faisal yaja tsaki yabi ta gefen mu ya fita a ɗakin, ɗagu da kaina nayi na dubi hanyar da fita, sannan na dawo da kaina kan Amaal, fuskana cike da damuwa nace, "Amaal bana so ta dalili na ku samu saɓani da ɗan'uwanki, domin nasan irin son da kuke yiwa junan ku, bana so ta dalili na kuka sa samun fahimta, ni kawai naji ma zan koma school", na faɗa ina juyawa zuwa kan bed ɗin.

Takowa Amaal tayi tazo ta zauna a kusa dani tana dubana da damuwa ɗauke a fuskanta, "Hummy don Allah kada ki bari faisal ya ɓata mana jin daɗin hutun mu, don wallahi kikace zaki tafi toh nima binki zanyi mu tafi tare, ni in banda neman fitina ma, sainan da 5dys fa ya dawo, amma narasa wani fitinan ne ya dawo dashi daga kammala exams ɗin shi, yawanci yana ƙara wasu kwanaki kafin ya dawo, amma ji don ya zo ya ɓata mana hutun mu sai ya dawo, ni banji daɗi ba, kema hummy ki daina sake mishi fuska, kuma gashi Dr yana ta ƙiranki bakiyi picking call ɗin ba, har ya fara ƙiran nawa, toh yanzu me zamuce mishi bayan yaji ihuna hala".

Cikin damuwa nace, "Amaal toh kisan dabaran da zakiyi kada ya fahimci wani abu don Allah", na faÉ—a ina zaro ido tsabar fargaba.

Ɗaukan wayan Amaal tayi, bayan ta amsa mishi sallaman shi naji tana ce mishi, "wallahi na buɗe ƙofa zan shigo kawai na tafi zan faɗi ban sani ba, shiyasa na yi ihu, ina ga anyi mopping wurin bai gogu da kyau ba, kaman da sauran santsin ruwa a wurin, ita kuma hummy sai ta razana ita da Bros Faisal da yake bina a baya, amma ba komai banji ciwo ba kawai naji tsorone", ta faɗa tana maida abun dariya.
Chapter 32 · 0% Book details