← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 66

Sashe 14

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarasowa jikin motan na yi ina murmushi, ganin su Peter sun wuce gidan su ya saka nima na buɗe gaban motan na zauna, har lokacin murmushi na keyi ina duban Dr don inji mai zaice, amma abin mamaki ko kallo na bai yi ba, jan motan kawai ya yi muka fita a gidan.

Muna tafiya shiru bai ce mun komai ba, a hankali na dube shi nace, "Dr mu baka ce komai ba"?.

Baice mun uffan ba kuma bai kalli in da na ke ba, ganin fuskan shi a É—aure ya saka naja baki na na yi shiru, muna haka babu wanda ya kula kowa sai ni da nake kallon gefen hanya, a haka har muka isa wurin cin abincin.

Tun da nazo garin ban taɓa ganin wurin da ya mun kyau da ban sha'awa irin wannan wurin ba, kallon wurin nayi baki na ɗauke da murmushi nace,

"Dr'n mu wurin nan ya mun kyau sosai, ban taɓa ganin wurin da ya mun kyau irin nan ba tun da na zo garin nan".

Kallo na ya yi baice komai ba ya buɗe ƙofan ya fita, ganin haka ya saka na yi sauri na buɗe motan nabi bayan shi.

Woow gaskiya wurin cin abincin yayi kyau na gaskiyan gaske, da ya ke ba cikin wurin muka shiga ba kai tsaye, wurin swiming full ɗin muka je shi yasa wurin ya yi matuƙar burge ni, in da muka zauna ya yi ɗan gefe da mutane, kuma ma wurin mutanen basu da yawa, sit biyu ne a kan table ɗin, muna zama ya ƙurawa ruwan idon amma har lokacin fuskan shi a ɗaure tam.

Kallon shi nayi jiki na a sanyaye na ce, "Dr mu mai ya same ka naga ranka a ɓace? Ko nayi maka laifi ne?".
na faÉ—a ina kallon shi kaman zan yi kuka.

Ɗago idon shi ya yi ya ƙura mun ido, baice mun uffan ba sai kallon da yake mun, wanda har na fara jin wani iri a jiki na, can na hango wata ƴar budurwa da fararen kaya ta nufu in da muke, daga ganin irin ma'aikatan wurin ne, ganin ta ƙaraso in da muke da wani ɗangalallen skirt ɗin ta duk sai na ji haushin ta ya kama ni, na dube ta a ya tsine ganin gaba ɗaya ita hankalin ta akan Dr ya ke ba a kaina ba, sai wani rausaya ta ke yi kaman wata ganyen bishiya, miƙa mishi menu ta yi ya zaɓi abincin da ya ke so, hararan ta nayi bansan lokacin da naja tsaki ba, bayan yayi ticking abinda ya ke so ya miƙo mun, ni dai kawar da kaina gefe nayi ban ƙara kallon shi ba.

Shiru ya yi yana kallo na yana jiran yaga me zan ɗauka, ni dai ƙara juyar da kaina na yi na dubi cinyar yarinyar wasu sirara da su farare, na sake ɗaure fuskana na dubi Dr daya ƙura mun dukkan idon shi a kaina, alaman zan mishi kuka nayi.

"Ranka ya daɗe to ka zaɓa mata abin da kasan ta fi so mana? Don naga daga dukkan alama wannan amaryar ta ka yau shagwaɓa ta ke ji da shi, kai ta ke jira kamata komai".
yarinyar ta faÉ—a cikin harshen turanci tana duba na da murmushi.

Kallon ta ya yi yace, "ita haka ta ke wai duk abunda na ke so shi ta ke son ci itama, saboda haka ki kawo mana komai iri É—aya kada yau ta hanani sukuni da fitinar ta".

ya faÉ—a yana duban yarinyar, wanda ta juya tana ta murmushi tana cewa, "haka halin amare ya ke ai, sai ta haihu kuma kaga ta koma son abinda É—an ta ke so".

Harara na bita da shi daga baya naja tsaki baki na a zunɓure na juyo da fuska na kan na Dr, gaba na ne naji ya faɗi da ƙarfi domin ganin idon Dr Hussain sauƙe a kaina yana bina kuma da murmushi.

"Yarinyar tana da kyau sosai gashi ta iya karrama baƙo".
na ji muryan Dr Hussain yana faÉ—a mun a hankali cikin nutsuwa.

Da sauri na ɗago na dube shi, har lokacin idon shi yana zube a kaina, da sauri na sa kai na duba in da yarinyar ta bi amma ban ganta ba har ta wuce, zunɓura baki na yi ina kallon shi kaman zanyi kuka na ce,

"Dr bata fini kyau ba fa, kaga ƙafanta fa kaman bulugari".
na faÉ—a ina turo baki na gaba, kallo na ya yi yana É—aga kafaÉ—an sama, sannan yace, "ni dai a ido na ta mun kyau sosai".

"Dr to ni fa bana maka kyau ne? Kullum sai kai ta faɗin kyawun wasu amma ni ko sau ɗaya baka taɓa cewa ina maka kyau ba".
na faÉ—a ina kifa kaina akan table É—in zan mishi kuka.

"Kina mun kuka idan ta dawo zan faÉ—a mata a gaban ta duk duniya babu mai irin kyawun ta, saboda haka gara ma ki É—aga kan ki don gata can dawowa".

Ɗago kaina na yi na dubi hanyar da ta ke tahowa na ƙura mata ido, can na juyo da ido na kanshi na ce,

"amma baka gani da kyau Dr, don Allah dube ta yadda kasan kazar mayu haka ta ke, amma har ka iya ganin kyawun ta ba ka ga nawa ba, ni da na ke Æ´ar duma-duma mai kyawun asali".
na faÉ—a ina juya ido na ina kuma hararan in da ta ke tahowan.

Dariya Dr Hussain ya yi wanda abin mamaki har sai da sautin ya fito sosai, ƙura mishi ido nayi baki na a buɗe ina kallon shi da mamakin dariyan da ya keyi, dai-dai lokacin kazar mayun ta ƙaraso.

Fuskar ta É—auke da fara'a tana duban shi tace,

"oga lallai yau kana cikin jin daÉ—in amarci, ya kama ta ayiwa amarya kyauta don ta na ra saka ka farin ciki, amma ita kuma naga kaman baka sa ka ta farin cikin, don sai shan magani ta keyi".

ta faÉ—a tana jera mana komai akan table É—in, gefe É—aya kuma wani abokin aikin ta ne yake ajiye mana drinks É—in.

Hararan ta na yi nace,
"ke wai baki da abin faɗi ne sai akan Dr na! Gaba ɗaya daga kinaraso sai ki maida hankalin ki kanshi jiki yana rawa, to Dr matar shi ta ishe shi, don tafi kyau da siraran ƙafan ki a wurin".

na faÉ—a ina murguÉ—a baki na gefe, shi dai Dr sai dariya ya ke tayi, duk jikin yarinyar a sanyaye ta bar wurin cikin sauri.

Harara na bita da shi nace,
"ga É—uwawun ta kaman an maka mata mara, ni banga wani abin burgewa ba anan wurin in banda abin nimiji".
na faÉ—a ina kallon shi fuska na a murtuke, saboda irin dariyan da ya ke ta yi.

Kallon shi na ke yi baki a buɗe, don na fara ƙuluwa da dariyan da yake ta yi, ganin bazai daina ba kawai na miƙe tsaye zan bar wurin, sai ji nayi an cafko ni da sauri har sai danayi kaman zan faɗo kanshi, har lokacin idon shi yana kaina fuskan shi ɗauke da murmushin, sannan ya ƙura mun ido ta cikin glass ɗin shi.

Kallon in da yarinyar ta bi nayi, sannan na dawo da ido kanshi, shima har lokacin kallo na ya ke yi, sai can yace, "idan kin tafi wa zai ci abincin da ki ka saka nayi order'n shi"?

"Sai na kira maka ƙazar mayun ta taya ka ci ai, tun da na ga hankalin ka baki ɗaya ya tattara gare ta".

Ƙunshe bakin shi ya yi kaman yana son maida dariyan shi, yana kallo na yace,

"to ai kince É—uwawun ta kaman an maka mara, to me zan kalla a jikin ta har naji daÉ—in cin abincin? Kawai ke Æ´ar duma-duman nake son ki zauna ina kallon fuskar da Peter yace mai kyau ne, ki sakani na yi ta cin abincin, ina tunanin wani irin miji zan nema miki wanda zaku haÉ—u ku haifi yara masu kyau".

Zama nayi ina duban shi da murmushi sannan nace, " yanzu kaima kaga bata da kyau ko?".

ÆŠaga mun giran shi yayi alaman "ehh" Sai na ji daÉ—i ya rufe ni, ina kallon shi da jin daÉ—i É—auke a fuska na nace, "to ni fah ina maka kyau?".

Girgiza kai ya yi alamar "a'a".
turo baki na na yi kaman zan yi kuka nace, "to ni yaushe za ka ce ina da kyau ne kam Dr? Bayan kai kullum kyawun ka na ke gani, amma ni sai dai kaga na wasu amma baka ganin nawa?".

Murmushi ya yi ya ce, "sai ranan da wasu suka daina ganin kyawun ki, to ranan zan gaya miki abinda ki ka daÉ—e kina so kiji daga gare ni".

yana gama faÉ—in hakan ya turo mun pilet É—i na gaba na, ganin haka yasa na harari abincin na juyar da kaina gefe.

"me yasa ta ce ni amaryar kace amma baka ce mata ni sister ka bane? Yanzu idan wani yana so yace yana sona ai fasawa zai yi idan tace ni matar aure ne, bayan kuma kasan kai É—in kana da mata Æ´ar wada".
na faÉ—a ina kallon zoben hannu na.

Murmushi ya yi sannan a hankali yace,
"don Allah kici abincin ba na so kuma ki ɓata yammacin da kika ƙawata mun shi yanzu-yanzun nan, kada ki bari ɓacin rai ya ziyar ce ni Aisha, idan mun ci abincin zan gaya miki dalili na na gaya mata hakan kinji ƴar rigamar Dr'n ta".
ya faÉ—a har lokacin ya na murmushin.

Muna gama cin abincin ya ƙurawa ruwan ido, ganin ba zai ce komai ba yasa nace, "mun gama ci baka gaya mun dalilin ba".

Lumshe idon shi ya yi bai ce komai ba, sai murmushin da yake ƙawata fuskar shi kawai ya ke yi, ina kallon shi a zuciya ta nace,

_anya a kwai mai irin kyawun Dr Hussain kuwa? Allah yasa idan na ta shi aure na samu mai irin kamanin shi, don gaskiya Dr Hussain mai kyau ne, kuma mai aji ne na ƙarshe._

"Dr idan na girma zanyi aure zan samu mai irin kyawun ka kuwa".
Na faÉ—a hankali na kwance ina duban shi.
Chapter 14 · 0% Book details