← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 66

Sashe 23

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bansan me yasa na ke yawan jin kunyar shi ba idan ya kalle ni, murmushi na yi na sunkuyar da kaina ina kallon yatsuna ina wasa da su.

"Faisal matashin yaro ne fari kyakkyawa mai nutsuwa da ilimi, Faisal farin balarabe ne ɗan gata a wurin Ummi da Abbu, Faisal shine ɗa na farko a wurin iyayen shi, yana karatun medicine a oxford university, yana shekaran shi ta ƙarshe, Dr naj ina matuƙar ƙaunar Faisal, saboda irin so da kulawan da yake nuna mun, faisal ba ya haɗa soyayya ta da ko wacce mace a duniya, ko dan ba bu wanda ya taɓa so nane sama da na shi? Oho ina ga don duk duniya babu mai mun irin soyayyan shi shiya sa nake ganin hakan".

"ƙarya ya keyi bashi kaɗai bane yake sonki, ƙarya ne shiɗin ba son ki ya keyi ba yaudara ne, ina ma yasan kanshi ballan ta na ya soki".
Cikin tsawa yake maganan bayan ya miƙe ya tsaya a kaina.

"Kada ki sake barin zuciyar ki ta yarda wani yana miki so sama".......

sai kuma ya yi shiru yana kallon Amal da ta taso ta miƙo mun waya tana,
"ga bros yana kira".
tana miƙa mun ta ɗauki kwanukan tayi hanyar fita a parlon, ni kuma ɗauka nayi fuskana cike da murmushi, amma ƙasan zuciya ta kaman na ranta da gudu.

"Hello honey nah".
Banji amsan da Faisal ya bani ba kawai naga waya ta a hannun Dr, kashe wayan ya yi sannan ya nuna ni da yatsan shi.

"Duk abinda ya ke rawa a kan ki Aishatu zan ɗaure miki shi, baki da hankaline a gaba na zaki tsaya kina waya har kina ƙiran wani ƙaton banza wai Honey? Baki da tunani ne? To daga yau ki bashi haƙuri kigaya mishi gaskiya karatu za kiyi ba soyayya ba, nawa ma ki ke da zaki damu kan ki da soyayya. Ko dama abunda Daddy ya turo ki yi kenan?".

Juyi na farayi a gabanshi ina magana cikin shagwaɓa,
"Dr'n mu dubi fa wallahi na girma, kuma ni son shi ya mun yawa kaman bazan iya karatun ba ma gara a mana aure kawai".
na faɗa ina ɗaura hannu na a gefen heart ɗina ina wani lanƙwashewa kaman tarwaɗa.

ya daÉ—e yana kallo na, sannan murya a hankali ya nuna mun hanyar waje yace,

"fita don Allah kije ki ƙarashi fitinan ki wa Amal, amma nikan nawa ya isa haka, wuce kifita".
ya faɗa kaman idan ya buɗe baki ya yi magana da ƙarfi zuciyar shi zata faɗo.

Buga ƙafa na fara a wurin ina nikan bazan tafi ba sai kaba ni waya na, kasan fa zai kira ni anjima, kuma ni sai ka rakani Dr nah".
na faɗa ina kan dire ƙafan a ƙasa.

Riƙo hannuna ya yi muka nemi wuri muka zauna, yana duba na a nutse yace,

"Don Allah ki taimake ni ki rabu da yaron nan, bana so naga kina son kowa Humairah, ban shirya samun damuwa ba a tsakanin mu yanzu, don Allah ki barshi bana so, ko baki so na samu kwanciyar hankali ne?".

"ina so mana Dr'n mu".

"tunda kina so to bana so naga kina son kowa idan kin tashi aure ni zan zaɓa miki miji, amma yanzu karatu na fi so kiyi kin ji Baby nah".

Turo baki na nayi gaba ina kallon shi kaman zan yi kuka nace,
"Dr ni fa auren shi zanyi, ina son shi fa sosai, da ƙyar fa nake iya bacci this days, daga na kwanta sai na fara mafarkin munyi aure ya kaini mall, wataran har yara masu na ke ganin mun haifa kaman yaran Larabawa".

"Ya rabbi! Don Allah ki daina kwantan ta kan ki da wani namiji Baby, har kina tuna wai za ku haihu tare? Zaki kashe ni ne kawai kwanana bai ƙare ba".

ya faɗa yana matse yatsun hannu na da ƙarfi, wanda har sai da nayi ƙara da ƙarfi tukun ya sa ke su.

"Baby kaima fa kana da mata, to ni me zai sa ba zanyi aure ba?".

"ni bani da wata mata".
ya faɗa da ɗan ƙarfi yana ƙura mun ido, nima ƙura mishi idon nayi cike da mamaki, baki na a buɗe nace, "Dr Khadijah fa?"

"Ni ba mata ta bace, ita ta ke shirmen ta, ke kuma ki ka dame ni wai mata ta ce, ni tun da nazo ƙasan nan ban taɓa son kowa ba sai mace ɗaya, ni kuma ban taɓa aure ba har yanzu".

Gaba na yana faɗuwa ina duban shi nace, "wacece ka taɓa so a ƙasan nan? To me yasa na gan ka da Dr Khadijah ranan a wuri ɗaya? Idan ba son ta ka ke yi ba mai ya haɗa ka da ita?".
Na faÉ—a kaman wata mai tuhuman É—an ta.

Sa ke riƙo hannu na ya yi cikin ƙasa da murya yace,
"ni dai bana son Khadijah, kuma ban taɓa son ta ba ballanta na na aure ta, amma na miki alƙawari idan kin rabu da yaron nan zan baki labarin komai game da Khadija".

"har wanda ka taɓa so zaka bani labarin ta?".
Yana murmushi yana duban ido na yace, "har su Hassan ɗi na, Ummi nah da Abba nah duk zan baki labarin su, amma sai kin mun alƙawari ba zaki sa ke kula kowani namiji ba, kuma ba zaki so ko wani namiji ba sai wanda na zaɓa miki".

Shiru na yi na zuba mishi ido, ganin yadda shima ya ƙura mun ido nace,
"to nima kamun alƙawarin ba zaka so ko wacce mace ba, idan ka so wata nima zan so faisal, don yana da kyau kuma fari ne".

"Baby ya kai ni kyau?".

Kallon Dr na yi baki na a buɗe nace, "ni fa ban taɓa ganin mai irin kyawun ka ba, kai fa kyawun ka mai kyau ne".

Runtse ido ya yi zuwa can ya buÉ—e su a kaina, "ta shi muje na raka ki dare ya yi, kuma Amal za ta gajji da jiran ki".
ya faÉ—a bayan duk mun tashi mun tsaya muna kallon juna.

"Baby kina da".... Sai kuma ya yi shiru yana murmushin da ya ke cije leɓen shi, turo baki nayi nace, "baka ƙarasa ba".

Dariya ya yi ya jawoni muka yi hanyan waje, a waje muka ga David da Peter suna shigowa gidan, zuwa su kayi suka gaida Dr, sannan Peter ya dube ni yace,

"preety yau kin yi kyau sosai, kaman wata star".
Ya faÉ—a suna wuce gidan su suna dariya.

Nima dariyan nayi na matso kusa da Dr nace, "kai kaɗai ne baka taɓa ce mun ina da kyau ba, kowa sai yace kyawuna ya yi yawa ma, amma kai ko kaɗan baka taɓa cewa ba".
na faÉ—a ina hararan shi.

Yana rako ni ya tsaya yana mun wani duban da har sai da naji tsikar jiki na yana tashi yace, "bana son kibar su Peter suna cewa kina musu kyau ba, bana jin daÉ—i, sufa students É—ina ne, bana jin daÉ—i gara ki hana su".

"zan gaya musu su daina, amma da gaske goben komai zaka gaya mun"?

"idan kin daina son Faisal ba".
ya faÉ—a yana komawa gidan shi, bayan ya sa ke mun hannu na.

Ina shiga Amal ta taso tana tambaya na yadda a kayi? Labarin abinda ya faru na bata, haka muka yi ta dariyan shi, duk da Amal ta mun masifan me yasa nace yana da kyau, me yasa kuma nace, shi bai ganin kyawu na?.

Hararan ta nayi nace, "ce miki a kayi ina sani ne na ke gaya mishi? Kawai idan ina ta re da shi manta kowane shawara ku ka bani nake yi, sai É—aÉ—É—aya, ke dai Allah ya kaimu goben muji labarin komai.

_NIMA AUNTY NICE NA CE ALLAH YA KAIMU GOBEN DA RAI DA LPY, IDAN KUNA BIYE DA ALƘALAMI NA ZA MUJI ME ZAI KASANCE A TSAKANIN SU._

VOTE
COMMENT
SHARE

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 16📑*

*____________* 📖 Muna cikin haɗa girkin Amal ta ƙira brother ta Faisal, suka shiga tsara yadda zasu dinga ɗaga hankalin Dr Hussain, nidai sai dariya da sha'awan su kawai nakeyi, domin a handsfree ta bar wayan, burgeni sukeyi kaman wasu friends.

Ina sauraren su ina ɗan dariya ƙasa kasa, chan naji muryan Faisal yana cewa, "ina ƴan mata na ɗin? Bani ita naji muryanta", dukkan mu dariya mukayi tukun ta miƙo mun wayan na kara a kunne na.

"Hello sweety" ina dariya nima nace, "hello honey" dukkan mu dariya mukayi, sannan ya dinga tsara mun yadda zan dinga amsan wayan shi a gaban Dr, haka mukayi ta hira har muka gama girkin mu, ƙamshi kam nasan ba gidan Dr ba, yau inaga hatta gidan su Peter ma sai sunji.

8:30pm dukkan mu munyi wanka, dogon riga muka saka kowa ta yafa É—an gyalen kayan, É—iban abincin mukayi dukkan mu muka fita zuwa gidan Dr.

Bamu daɗe muna knocking ba yazo ya buɗe mana, har zuwa lokacin fuskar shi a ɗaure, haka ya bamu hanya muka kai abincin har kan dinning ɗinshi, wucewa yayi parlor ya chigaba da kallon shi batare da ya kalli inda muke ba, ganin haka Amal ta mun signa, dariya nayi na wuce inda yake na zauna a hannun kujeran ina leƙa fuskan shi ina murmushi.

"Babyn baby yau na maka girki mai daɗi, taso muje na zuba maka kaji daɗin shi," harara na yayi sannan ya juya ya kalli inda Amal ta ke zaune, ganin hankalinta yana kan wayanta sai ya dube ni yace, "bazan ci ba ni naƙoshi".

"Haba babyn baby! Ko kafiso yau na kwana banci komai ba? Kuma na kwana ina kuka"? Na faÉ—a kaman zan fara mishi kukan a lokacin.
Chapter 23 · 0% Book details