← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 66

Sashe 27

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dr Abdallah tun ranan da muka zo registration Abbu ya haɗa ni da shi a matsayin Dr na, kuma tun lokacin na fahimci ya faɗa cikin soyayya ta, amma ban ƙarasa fahimta ba, sai da nayi ciwo na tafi gida, ya kasa zama ya bini har ƙasan mu, duk da shima ɗan can ne kuma cikin gari ɗaya muke, amma nasan ya yi haka ne don ni, soyayya ce kawai zai kawo haka, sannan wannan kwanciya ta ɗin ya nuna mun babu wata mace da ya ke so da tausayi iri na, ranan farko yace mun, ya kamata na auri likita domin na dinga samun kula, sannan ya dawo yace shi zai sama mun wanda zai kula dani, washe gari yace duk duniya shi zai fi bani kula saboda haka ya zaɓa mun kanshi don ya kula dani, ai dai baki ji yace so na yake yi ba, amma kuma yanzu ni da shi mun san soyayya muke yi, ke kuma abunda kika kasa fahimta da Dr Hussain kenan, yana miki son da ko a gaban waye sai ya nuna, amma ke duk bai ishe kiba kinfi son yace yana son ki kije kiyi tunani bayan 2 days ko? Irin yadda su Ummi suka yi da ko?".
Ta faÉ—a tana harara na.

Bansan lokacin dana kwashe da dariya ba, duk wannan ɓacin ran lokaci ɗaya naji ya gudu, duk dariya muke yi ni da Amaal, sai naji waya ta ta fara ringing, da sauri na jawota ina dubawa, ganin sunan Dr Hussain ya saka ni zaro ido na duban Amaal.

Harara ta mun taja duvet ta shige ta bar ni, haka na É—auki wayan yana dab da tsinkewa,
"hello babyn Baby ba kiyi bacci ne bane?".
Naji yana tambaya na da wani irin murya wanda baza ka taɓa cewa muryan shi bane.

Lumshe ido nayi a hankali na furta,
"na kasa bacci saboda bansan ko Baby ya yi bacci ba".
na faɗa ina jin yadda zuciya ta ta ke bugawa da sauri da sauri, saboda ban taɓa tunanin baki na zai iya furta haka ba.

Daga in da Dr yake ya tashi ya zauna, murya ƙasa-ƙasa yace, "da gaske?".

"iya kacin gaskiyan da yake zuciyata kenan my Dr".
na sa ke tabbatar mishi.

Ajiyan zuciya ya yi yace, "Baby ina son ganin ki wallahi yanzu a gaba na, Baby bugawan zuciyata yana ƙaruwa, Baby ki leƙo na gan ki don Allah".

Runtse ido na nayi saboda yadda na kejin muryan shi yana rawa, a hankali nace,
"Baby ni sai dai kazo ka É—auke ni wallah tsoron fitowa nake yi ni É—aya, kuma ni sai nagan ka kafin nayi bacci".
na faɗa ina mishi sheshsheƙan kukan ƙarya.

"Ba,,byy,yy!" Yaja sunan da É—an sauti sannan yace, "bana gajjiya da ganin ki, bana gajjiya da jin muryan ki, ki fito na ganki kin ji".

Tashi nayi wayan na riƙe a kunne na ina ta sauƙe mishi buhun shagwaɓa har nazo jikin ƙofan parlon na tsaya, ina jin shi ya buɗe na shi ƙofan ya ƙaraso, sai na kasa buɗe ƙofan, shi kuma sai magiya yake ta mun, ganin nayi da shi ya koma ya ƙi kawai sai na saka hannu na buɗe ƙofan, kallon shi nayi sanye da wasu kayan bacci cotton masu masifan kyau, three quater da riga mai kyau, ƙafan shi sanye da wani silifas fari, ido ya ƙura mun wayan shi yana kare a kunnen shi, har lokacin bai yanke ba, nima ina kallon idon shi ban yanke wayan ba, naji yace,

"Baby'n baby!" ta cikin wayan, ina kallon shi nace, "baby nerh!". runtse ido yayi.

_*MUM SAYYEED GA KYAUTAR WANNAN SHAFIN,BAWAI DON YA ISA YA NUNA MIKI IRIN ƘAUNAR KI DA MUKE YI NIDA BESTY BA, KO ƊAYA KINFI KYAUTAN LITTAFI GUDA MA A WURIN MU, KINA NAN CIKIN RAN MU, MUNA MIKI SON SO.*_

*Plsss keep following, commenting, voting and sharing.*
*Love you all my fans❤️😘.*

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

_Wannan shafin nakine MUM SAYYEED Allah ya bar zumunci_

*SHAFI NA 21📑*

*__________📖* Murmushi nayi ganin ya buɗe idon yana mun alaman da yara sukewa iyayen su idan suna son abu a hana su, ganin ina murmushi shima ya maida mun martanin murmushin, "Baby kaman yau bazan iya bacci ba idan bamu tare, yayah za'ayi ne wai? Babyn ki fa abin tausayine fah", ya faɗa yana ƙara matsuwa kusa da inda nake.

Murmushi nayi na ɗan matsa baya kaɗan, don yazo dab da ni har ina jin numfashin shi a kusa da ni, "Baby toh kasan babu yadda zan maka, domin Allah bai halattah kwanan mu wuri ɗaya ba, saboda haka kayi haƙuri ka koma ka kwanta, da safe zamuyi magana, yanzu kam ae ka ganni", na faɗa ina ƙara sauƙe mishi murmushi.

"Babyn baby toh ae yakamata nayi wa Daddy magana domin ayi auren akan lokacin, don gaskiya ni nafara nema na rasa nutsuwa na akan ki, kuma ni irin su Faisal É—in nan ba zasu barni na samu kwanciyar hankali ba", ya faÉ—a yana harara na da wasa.

Dariya nayi mai ɗan sauti, "Baby aure kuma tun ban girma ba? Gaskiya ni sai nayi masters ma tukun nayi aure, nidai gaskiya naƙi ba yanzu ba", na faɗa ina dariyan yadda ya buɗe ido da bakin shi yana kallo na cike da mamaki.

"Gaskiya bazai yiwu ba baby, ni bana son kodawo wani semester ma ba muyi aure ba, idan ba haka ba zan taro gidan nan da zama, da kike cewa baki girma ba, bazaki iya ɗaukan Babyn ki bane?" ... Faɗin haka da yayi nayi sauri na rufe ƙofan da ƙarfi, na juya da gudu nayi cikin ɗakin mu ina dariya, da yake duk abun da mukeyi wayan mu yana kunnen mu bamu wanda ya kashe, inajin dariyan shi ta cikin wayan yana cewa, "ƙarya na miki? Kuji mun ƴan matan nan da wayo, kina birkita ni da salon soyayyah ki kuma kina cewa baza muyi aure yanzu ba"? Ina jin shi nayi sauri na katse wayan nima ina dariya, kan bed ɗin na faɗa ina dariya ni kaɗai na.

"Don Allah ki koma parlor ki kwanta, sai kiyi ta sakarcin dariyan ki achan, yarinya anje an kunche miki kai da soyayyah zaki dawo ki sauƙe mun buhuhhunan haukan anan ko? Toh baki isa ba, koma kije chan ko kwana kuna gigita junan ku", Amaal ta faɗa tana turo ni daga kan gadon.

Dariya nayi ina faɗin, "baza ki gane bane Amaaƙ ɗita, bansan me nakeji ba acikin zuciyata ga me da Dr, ina mishi wani fitinannen so, wanda yana nema ya fi ƙarfin xuciyata", na faɗa ina dafa zuciyar bayan na runtse idona.

Kallon mamaki Amaal ta ke mun, "kice bazamu gama school ba za a muku aure"?

Hararan ta nayi, "kaji mun Amaal, bamu gama school ba kuma a mun aure? ae ban girma ba tukun, gara dai sai nagama masters sai amana, lokacin na ƙara girma".

"Chabb ae ko ba son shi kikeyi ba, tun da har son ya fara fin ƙarfin zuciyar ki ae sai a tattara mishi ke a haɗa ku gida ɗaya, ku cinye kanku da soyayyah, amma ni bazan yadda kije ya birkita ki kizo kina hana ni bacci ba, ehen gara ma ki gane", Amaal ta faɗa tana komawa tana kwanciya.

Rayuwar yana ta tafiya, a yau muka fara exams É—in wannan semester, gaba É—aya mun koma wasu iri, domin dukkan mu muna so mu fito da sakamako mai kyau, duk da irin zafin da muke bawa kanmu, bamu rage komai ba ga me da soyayyah mu, duk abinda muke yi dole sai mun bada lokaci na musamman wa junan mu,una yiwa junan mu so na fitar hankali, gashi bamu iya É—aukan lokacin bamu neme junan ba, haka wurin Amaal da Dr Abdallah, kullum suna tare da juna, duk yadda kake tunanin sun wuce wurin, domin wani irin kula Dr yake bawa Amaal, kaman ya maida ta ciki.

Daddy hankalin shi ya kwanta sosai, gashi Abbun Amaal yace mishi idan munyi hutu zai haÉ—a ni da Amaal muje muyi hutu tare a wurin su, domin shi Daddy yace baya son nazo hutu har sai na gama karatu na gaba É—aya, saboda shi baiga me zai saka na taho hutun ba, gara shi idan anyi hutun ya zo mun, amma jin cewa Abbu yace zamuje wurin shi sai Daddy ya samu nutsuwa, domin dama tunanin shi ko naje gida bawani daÉ—in zama zamuyi da su Mama ba, gashi anyi auren Adda hafsat Adda Halima ce a gida, shima Yayah Ahmed dama na taho ana shirin auren shi, ganin basu damu dani da rayuwa ta ba, Daddy bai ko gaya mun anyi auren Yayah Ahmed ba.

Ranan da mukayi final exam ɗin mu, rana ce da bazan taɓa mantawa ba, domin a wannan ranan zuciyata ta aminta da irin son da Dr nah yake mun, sannan a wannan ranan na barwa zuciyata ko bai taɓa furta mun kalmar I Luv U ba, toh zan iya ƙarasa rayuwata da shi, domin ya nunawa duniya babu wata mace a zuciyar shi sama dani.

Bayan mun gama paper muna ta sallama da ƴan class ɗinmu, shi kuma yazo ɗaukan mu domin mu wuce gida, Amaal ta gajji da jirana saboda complain da ta keyi na ƙafan ta da yake ɗan mata ciwo, sai ta wuce cikin motan ta zauna, shi kuma Dr nah ya buɗe mun gaban motan yana jira nah, duk i da nayi idon shi yana kai na, chan na gama abunda na keyi na taho zan shiga gaban motan inda yayi sauri ya buɗe mun daga inda ya ke zaune.
Chapter 27 · 0% Book details