Sashe 51
Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba tashi yayi ya zauna yan bin ƴaƴan shi da kallon so da ƙauna yace, "Adda na Fatima ta nuna mun ƙauna, lokacin da take makaranta duk kuɗin tara idan an bata bazata sayi komai taci ba sai tayi ta asusu, idan kuɗin ya taru zata ɗauke ni ta tafi dani kasuwa duk kayan dana ke so zata saya mun, lokacin aurenta kukan ta na rabuwa dani ne bawai na tafiya tabar iyayenta ba, ranan da za'a kaita gidanta da yake garin toro sukayi hatsari ita da wata goggon mu Allah ya karɓi ransu a wannan lokacin, mutuwar ta taɓa mana zuciya ba kaɗan ba, wanda ni har gobe na tuna sai nace zafin danaji yafi na mutuwan iyayena ma, naso tun haihuwar Amina na saka sunanta, amma sai mahaifin mu ya umarce ni da saka sunan jatumar shi, Hadiza kuma ya umarceni da saka sunan kakarku ta wurin uwa, umaima kuna na saka sunan tawa mahaifiyar, haihuwar indo kuma yazo da rashin mahaifiyar ku wanda dole sunan ta ya chanchanta na saka, da na haifi Asma'u kuma na saka sunan goggona wanda suka rasu tare da Adda fatima, Nana khadija kuma nayi karawa Maman ku kaltume na saka sunan nata mahaifiyar, kinga autata taci soyayyah uku, na farko sunan Adda na, na biyu sai ta ɗauko kamnnin Adda na ɗin, shiyasa suke ɗibi da Umar da Abdallah, sannan na uku kuma autata, kunga dole ta zama aminiyata".
Gaba ɗaya dagowa sukayi suka dubi Baba suna dariyan yadda ya ƙarasa maganan shi cike da zolaya, Uncle Abdallah da tunda ya zauna bai tanka musu ba sai lokacin ya dubi Baban su yace, "Baba insha Allahu idan na haifi yara zan saka sunan yayah Umar da sunan Fatima, domin na ƙara faranta maka, don na lura baka haɗa son su da kowa a duniyan nan, ni kuma insha Allahu zan sake faranta maka da maimaita sunan su a ƴaƴana".......murmushi Baba yayi yace, "kaiɗin daban kake acikin ƴaƴana Abdallah, tun kana yaro burinka ka dinga faranta mun, kaima ina maka Addu'a Allah ya faranta maka duniya da lahira, tabbas ina jin Umar da Zahrah a zuciyata daban a cikin ƴaƴana, saboda sunan wanda suka ci a zuciyata, haka Indo ita kuma nafi jin tausayinta sama da kowa a cikin abinda na haifa, shiyasa babu garin Allah da zai waye ban ƙirata naji yayah ta tashi ba acikin ku, duk ranan da ban kira ta ba sai naji kaman nayi rashin wani abu a tare dani, dukkanku ina sonku kuma kowa da irin rawan da yake takawa acikin ku, Allah ya muku albarka da zuriyar ku gaba ɗaya".
Aunty Hadiza ne ta dube shi tana murmushi tace mukan bansan me muke takawa ba a cikin Æ´aÆ´an, don Baba baka cika faÉ—in abu akaina ba," ta faÉ—a kowa tana mata dariya, don duk tafiso É—an zafi kaÉ—an, toh abu kaÉ—an sai ya tunzurata.
Gyara zaman shi Baba yayi fuskar shi ɗauke da murmushi yace, "Umar, Amina, sabo duk cikin yarana ba masu haƙuri da zumunci irin nasu, ke kuma Hadiza duk kinfi kowa son nuna mun ƙauna keda Abdallah a cikin yarah na, kuma kunfi kowa nuna tausayawa a al'amurana ku ɗin kuna da wani shashi na musamman a raina, wanda bana haɗaku da kowa, kuma araina inaji idan daku kowa baziyi maraici ba dije na.
Uwata umaima kuwa ita da Nana khadija, babu masu kawo farin ciki da walwala a cikin gida na irin su, wani lokacin idan suna raha da zolaya a cikin gida na sai naji anya akwai wanda nakejin son su irin waƴannan biyun kuwa, domin basu bar kowa ba, bani ba ba manaku ba wurin zolaya da neman magana, su ɗin kurwan gidana ne, idan babu su cikin gidan sai kaji maraici ya isheka, shi yasa da umaimah tayi aure sai danayi zazzaɓi, haka yanzu maganan auren Nana khadijah, idan na tuna sai naji kaman na bita gidan ta mu zauna kawai, don gidana zaiyi maraicin masu raha a gidana", yana faɗa Nana khadija tayi tsalle tace.
"yehhhh daga dukkan alamu Baba yafi son mu nida Aunty umaima," ta juya tana duban Zahra hannunta riƙe da ƙugunta ta karkace tace, "auta ki kiyaye ni kinemi sulhu dani, don daga dukkan alamun bayanin Baba bawai sonki yafi ba, kawai kinci darajan wasu ne, ni kuma tsantsar sone yake mun, don yace gidana ma zai bini", ta juya tana kallun Baba tace, "Baba yanzu zan gayawa mahmood ya nemi gida mai ɗaki uku, domin kaima tare zamu taho, kuma kasan wani abu ma Baba? Saboda kai zan daina baccin safe na tashi na maka ƙosai da kunu don ka karya, shima kaga zai samu kulawa saboda kai", ta faɗa tana ta rawan ta kaman ba a asibiti suke ba.
Duk yadda Uncle Abdallah yakai da É—aure musu fuska amma sai da yayi dariya yace, "mama dama hankali bai wadaci Nana khadijah ba? Yanzu anata haukan sai fa tagaya wa mijin nata tare da Babanta zasu taho"?.
Dariya Baba yayi yace, "kai baka san umaima dole na lokacin da tayi aure ba nake zuwa bauchi gidanta? Ina zuwa zata gyara mun ɗakin su na parlour tace Baba yau fa agidana zaka kwana, haka zan ta lallaɓata da ƙyar zata haƙura na tafi, lokacin da ta haifi ɗanta na fari, naje ina riƙe da ɗan, kawai sai ce mun tayi Baba da ina labour room da naji azaba nace, nagode Allah da Baba na bai zama mace ba, da bazan so kasha wahalan haihuwa ba Baba na am, gara su mama da mama ƙarama su karata da wahalar akanka," Baba yana cigaba da dariya yace, "wallahi tun ranan nace bansan ranan da Uwata zata yi hankali ba, hala sai tayi suruki", ya ƙarasa dukkan su suna dariya.
Aunty Hadiza tace, "nikan Baba baka taɓa zuwa gida na ba wallahi", ta faɗa tana turo baki gaba, Mama ta dubeta tace, "Hadiza kefa baki sati bakizo duba babanki ba, ae inaga shiyasa baya zuwa miki, ae ke kinfi kowa damuwa dashi,"
Baba dariya yayi ya koma ya kwanta, rufe ido yayi yana ɗan murmushi, a hankali yace, "damo sarkin haƙuri ma ae ban taɓa zuwa mata ba, kuɗin ae kune yanzu iyayena, ku zaku dinga zuwa duba ni, su kuma yaran zan dinga zuwa duba su," damo da Amina yakeyi, wanda yana yawan ƙiranta haka.
Washegari da safe su Dr suka kama hanyar Jos, wurin ƙarfe 10:00am, suka iso cikin asibitin, bayan anyi gaishe gaishe, Baba ya tambayi Aunty hauwa ina labarin amaryar shi? Tana murmushi bata ce komai ba, Aunty Amina ce ta dubi Aunty hauwa tace, "sun ma san kuwa Baba na asibiti"?....... "ni bandai gaya musu ba, amma bansan ko uncle Abdallah ya faɗa ba", Aunty hauwa ta faɗa kanta na sunkuye a ƙasa.
Uncle Abdallah ne ya shigo idon shi akan Baba yace, "wallahi sai yanzu kafin na iso mukayi waya da Abban ta nake gaya mishi, amma yace mun shi da kansa zaizo zuwa gobe ya duba ka, amma bansan ko tare zasu zo ba".
"Abdallah am da baka ɗago shi ba wallahi, yau baifi sati biyu bafa yazo ya gaishe ni, kawai ku ƙiramun amaryar tawa naji muryan ta", ya faɗa yana tashi zaune.
Uncle sabo ne ya ɗan taimaka mishi ya gyara zaman shi, shi kuma Uncle Abdallah ya ƙira wayan Ummi, bayan ta ɗauka ne sun gaisa yake gaya mata Baba ne baiji daɗi ba, Ummi hankali a tashe take tambayan yayah jikin shi? Daga nan ya miƙa wa Baba wayan suka gaisa, bayan sun gama Aka bamu muma muka gaisa da shi, don mu ganin kaka muke mishi, duk magana da akeyi a handsfree aka saka mu, Aisha ce ta karɓa daga ƙarshe, muryar ta mai cike da rawan kai tace, "kakan ƙauye bangan kaba"?
Baba zuciyar shi cike da ƙaunar yarinyar yace, "amaryar birni nazo nayita ɓata a garinku ban gane gidan ba, sai aka sakani a boot ɗin jirgi aka wurgo ni ƙauyen mu".
Dariya tayi mai ƙarfi cike da yarinta tace, "sun maka turanci ne baka iya ba, shine suka saka ka a boot ɗin jirgi suka wirgar da kai ko?" tana ci gaba da dariyanta tace, "ka sake zuwa ina son naja gemun ka, ina son ka saya mun gyaɗa da ummm....mango", ta faɗa tana dariya.
Shima dariyan yayi yace, "toh zaki koya mun turancin sai na dawo na kawo miki"?....... Dariya tayi tace zan gayawa Abba na da Ummi na su saka ka a school sai Uncle É—in school É—in mu su koya maka turanci, Yayah Hussain É—ina da Yayah Hassan ma sun iya suna koya mun, kaima zasu koya maka sai kayi tayi".
Duk kansu ɗakin dariyan hiran Baba da Aisha sukeyi, ita kuma Aunty Hauwa sunkuyar da kanta tayi tana murmushi, uncle Abdallah kuma kallonta kawai yakeyi babu ƙiftawa.
Bayan anyi sallan azahar Dr Alƙali da matar shi suka musu sallama suka kama hanyar bauchi, ita dai Aunty hauwa duk sai tajita wani irin tunda su Dr suka tafi, duk yadda Aunty Amina tayi tajata suɗan sake irin na da duk ta kasa, ganin haka Uncle Abdallah yace bari ya maida Mama Narabi ya dawo.
Tunda ya tafi bai dawo ba sai bayan Sallan magrib, daya dawo bayan ya gaida Baba bai kula kowa ba sai danne danne kawai yakeyi a cikin wayan shi, ana sallan isha su Aunty Amina suka yi wa Baba sallama suka tafi tare da Aunty Hadiza.
Wurin 9:30pm, Abdallah ya yiwa Baba da ya fara bacci sallama, sannan ya miƙawa Uncle sabo hannu sukayi sallama, kallon Aunty hauwa yayi yace ta taso su tafi.
Kaman zata tashi kaman bazata tashi ba, haka ta ke kallonshi, Baba ne yace, "kuje mana Hauwa kada dare ya muku", haka ba don ta so ba ta tashi jiki a sanyaye tabi bayan Uncle Abdallah, suna shiga cikin motan ya É—an dube ta sannan ya kawar da kanshi, baice mata uffan ba har suka iso wani hotel a cikin jos É—in mai É—an banzan kyau, zaro ido tayi baki a buÉ—e tace, "na É—auka Narabi zamu tafi fa"?